Masoya Dr Alkali salihu Zaria

Masoya Dr Alkali salihu Zaria Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Masoya Dr Alkali salihu Zaria, Grocers, Zaria, Zaria.

09/05/2026

Check out saluhu zakariyya’s video.

ALLAHMADULLAIH ALHAMDULILAH Ziyara Yan uwantaka na addini musulunci knn da dan uwa Young Alkali Gombe ya kawo wa Dr Alka...
06/05/2026

ALLAHMADULLAIH ALHAMDULILAH

Ziyara Yan uwantaka na addini musulunci knn da dan uwa Young Alkali Gombe ya kawo wa Dr Alkali Ustaz Abubakar Salihu Zaria Muna addu’ar Allah Ya saka maka da alkhari ubangiji y baka ladan ziyara dakayi fatan nasara a rayuwa ubangiji y cika maka burinka na alkhari ✊️

06/05/2026

Ameen 🤲 summa Ameen

02/05/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Mohammed Mansur Tahiru, Mohammad Mu'azu, Usman Mohammed Dawaki, Yusuf Ahmad Ahmad, Ibrahim Sa'idu, Shuaibu Haruna, Mouhammadou Salissou, Shehu Ibrahim Iro Nabeguwa, Sarah Mamza, Aminu Gariyabo Dange, Nasiru Abubakar Abdullahi, Isah Maijama'a, Alh Nasiru Adamu Inyass, Mudassir Namadi, Isah Lamido Adamu, Anas Arewa, Safiya Bena, Umar Muktar Shira, Bello Isa Mj, Musa Abdullahi, Bukar Suleman, Nazeer Naziru, Dauda Muhammad Imam, Nwakaego Ileka, Magaji Murtala Musa, Yaqoub Fadlullah Danji, Muh'd Bala Saleh, Aboulassane Makoli Manmane Aminou, Abdulkadir Muhammad, Mohammed Lawan Umar, Jamilu A Ahmed DT, Abdullahi Isah, Kabiru Hussaini, Harisu Abdullahi, Muhammad Sani Muhammad, Nkah Habibat Gambo, Umar Mohammed, Sayyadi Auwal Batijjaney, Abubakar Arrow, Abdulkadir Danzaria, Tidjani Issaka, Ummee Ummu Hanifa, Ibrahim Yusuf, Mohd Jalo, Bukar Saidu, Alhaji Abdullahi, Nafi'u Hamza, Mansur Sule, Issa Boubacar, Abdullahi M Abdull

NEMAN AURE GA MATASHI AYAU CIKE YAKE DA ƘALUBALE IRI DABAN-DABAN A yau, neman aure ga matashi ba abu ne mai sauƙi ba kam...
02/05/2026

NEMAN AURE GA MATASHI AYAU CIKE YAKE DA ƘALUBALE IRI DABAN-DABAN

A yau, neman aure ga matashi ba abu ne mai sauƙi ba kamar yadda mutane da yawa suke tunani. Ba wai kawai batun samun mace ba ne batun nauyi ne, shiri, da jurewa matsin rayuwa.

Yawancin matasa suna son aure da zuciya ɗaya, amma suna fuskantar ƙalubale masu yawa da ke sa hanya ta yi wahala. Wasu har suna kaiwa ga jinkirta aure ba don ba sa so ba, sai don yanayin rayuwa.

1. Matsalar kuɗi da tsadar rayuwa
Aure yana buƙatar shiri gidaje, hidima, alhaki, da kula da iyali. Yawancin matasa suna son su tsaya da ƙafafunsu kafin su shiga wannan nauyi, amma tsadar rayuwa tana sa hakan ya zama ƙalubale.

2. Tsoron zaɓin da bai dace ba
Aure ba wasa ba ne. Matashi da yawa suna jin tsoron shiga rayuwar da za ta zama nadama daga baya. Wannan tsoro yana sa wasu su yi jinkiri sosai wajen yanke shawara.

3. Matsin lamba daga iyali da al’umma
Wasu suna fuskantar tambayar “yaushe za ka yi aure?” kullum. Wannan matsin lamba yana ƙara damuwa maimakon ya taimaka.

4. Rashin fahimtar juna a soyayya
A wasu lokuta, mutum yana samun soyayya amma fahimta ba ta yi daidai ba burin rayuwa, hali, ko yadda ake kallon aure duk suna iya zama cikas.

5. Tsoron gazawa bayan aure
Mutum yana tunanin: “Shin zan iya kula da gida? Shin zan iya zama miji nagari?” Wannan tambaya tana yawan shiga zuciyar matashi mai tunani.

Mu sani neman aure ba kawai neman mace ba ne gina rayuwa ne. Don haka matashi yana buƙatar haƙuri, tsari, addu’a, da hikimar zaɓin abokin rayuwa.

Allah ya sauƙaƙa wa duk masu neman aure nagari, ya ba su abokan rayuwa na gari masu albarka. 🤲

Tambaya:
A ganinka, wane ƙalubale ne ya fi wahala ga matashi wajen neman aure a wannan zamani?

ku rubuta mana a comment section

MAFI DARAJA A WAJEN ALLAH DAGA CIKIN MUTANE.Mafi girman mutane a wajen Allah: Wanda ya fi tsoron Allah.Mafi daraja a cik...
01/05/2026

MAFI DARAJA A WAJEN ALLAH DAGA CIKIN MUTANE.

Mafi girman mutane a wajen Allah:
Wanda ya fi tsoron Allah.

Mafi daraja a cikin mutane:
Wanda ba shi da rowa.

Mafi daukaka a cikin mutane:
Wanda ba shi da yawan surutu.

Mafi amfani a cikin mutane:
Wanda yake amfanar mutane.

Mafi tsaftar mutane:
Wanda yake yi wa mutane kyakkyawan zato.

Mafi alkhairin mutane:
Wanda ya koyi Alkur’ani kuma yake koyarwa.

Mafi kyawun aiki a wajen Allah:
Sanya wani cikin farin ciki.

Mafi aikin da ya fi:
Yin sallah akan lokaci.

Mafi aikin alkhairi:
Biyayya ga iyaye.

Mafi aikin da Allah ya fi so:
Wanda aka dawwama a kansa koda kadan ne.

Mafi cikar imani a cikin muminai:
Wanda ya fi su kyawun hali da dabi'u.

Mafi kusancin mutane da Manzon Allah (SAW) a Ranar Kiyama:
Wanda ya fi kowa yawan yi masa salati.

Mafi daukakar daraja ga mai azumi:
Wanda ya kiyaye harshensa daga karya da gulma.

Mafi kyawun aboki a wajen Allah:
Wanda ya fi kowa zama alkhairi ga abokinsa.

Mafi hikimar mutane:
Wanda ya fi kowa lura da kura-kuran kansa maimakon na wasu.

Mafi karfin mutane:
Wanda yake mallakar kansa lokacin fushi.

Mafi arziki a cikin mutane:
Wanda Allah ya h**e masa wadatar zuciya da godiya.

Mafi kyawun gida a cikin musulmai:
Gidan da ake kyautata wa maraya a cikinsa.

Mafi kusancin bawa da Ubangijinsa:
Lokacin da bawa yake cikin sujada.

Mafi alkhairin abin morewa na duniya:
Abokin zama nagari wanda yake taimaka maka akan biyayyar Allah.

Ya Allah muna rokonka Ka sanya mu cikin bayinka wadanda Ka fi so,
Ka bamu ikon siffantuwa da wadannan kyawawan dabi'u.

Ya Allah Ka albarkaci rayuwarmu,
Ka bamu ikon dawwama akan ayyukan kwarai,
Ka kuma sanya kyakkyawan karshe ya zama rabonmu. Amin.

Addinu Annasiha

DA'AWA CE KADAI ZATASA MU SHUGA WANNAN GARIN KARFE BIYU NA DARE BABU MUSULMI KO DAYABAMUSAN KOWA BA TAFIYAN KILOMETERS 2...
01/05/2026

DA'AWA CE KADAI ZATASA MU SHUGA WANNAN GARIN KARFE BIYU NA DARE

BABU MUSULMI KO DAYA
BAMUSAN KOWA BA
TAFIYAN KILOMETERS 270
GA HAWAN MANYA MANYAN DUWATSU
GASU MATSAFA NE
HAKA NAKE KWANA A GARIN DA BABU MUSULMI KO DAYA NI KADAI

BAN TADA BARIN GIDANA DA NUFIN DAWOWA A RAYE BA KULLUM IN ZAI FITA BAN KWANA NA KEYI DA MATATS DA IYAYE NA

FIYE DA SHEKARU BIYAR INA YAKI DA YAN BOKO HARAM DA YAN BINDIGA DA IPOB ALLAH YA KARENI HAR NAGA MA AIKI LAPIA BELLE YANZU DA NAKE DA'AWA NAYI WANNAN POSTING DINNE DON IN TAIMAKAWA MASU BARAZANAN SAI SUN KASHE NI SUNSAN KAUYUKAN DA NAKE ZUWA HAR YAKAI GA ANA TRACKING NUMBER WAYA NA DON ASAN LOCATION DINA ABUN TAMBAYA ANAN SHINE BAZA KU IYA KARE ADDININ KU DA ILLIMI BANE SAI KISA KUMA KUKE KIRAN WASU YAN TA'ADDA ASHE KUMA YA TA'ADDANE

ADDU'A NA KULLUM SHINE MUTUWA KAN WANNAN HANYAR SHIYASA BAN TABA TSORON SHIGA WANI WAJE BA DUK HATSARIN WAJEN INA SHIGA KAUYUKAN MAIDUGURI DA KATSINA SOKOTO DUK DA RASHIN TSORON SU KUMA BAZAMU DAI NABA HAR RAI YAYI HALINSHI INSHA ALLAHU ALLAH KASA MU MUTU A WANNAN HANYAR KUMA KA KARBI AYYUKAN MU

ILLAR MUNAFUNCI DA KUMA HANYAR TSIRA 😒✅karɓo daga Abu Huraira (RA), Manzon Allah (SAW) ya ce:"Alamomin munafiki guda uku...
01/05/2026

ILLAR MUNAFUNCI DA KUMA HANYAR TSIRA 😒✅

karɓo daga Abu Huraira (RA), Manzon Allah (SAW) ya ce:

"Alamomin munafiki guda uku ne: Idan ya yi magana ya yi ƙarya, idan ya yi alkawari ya saɓa, idan kuma aka amince masa sai ya yici amana ." (Bukhari da Muslim).

Mafi haɗarin munafunci shi ne wanda mutum yake yi wa kansa, inda yake nuna takawa a fili amma kuma yana saɓon Allah a ɓoye.

Allah (SWT) yana cewa:
​"Suna son su yaudari Allah da waɗanda s**a yi imani, alhali ba sa yaudarar kowa sai kansu, amma ba su sani ba." (Suratul Baqara: 9).

​Mu binciki zukatanmu: Shin abin da muke nuna wa mutane shi ne ainihin abin da yake cikin zuciyarmu? Musulunci gaskiya ne, ba riga ba ce da ake cirewa a ɓoye.

Kowa yana yin kuskure, amma munafiki shi ne wanda ya mayar da yaudara da nuna fuska biyu a matsayin dabi'a.

Ya Ubangiji, ka sa mu kasance cikin bayinka masu gaskiya a fili da ɓoye.

Wane hali ne kake gani ya fi zama ruwan dare na munafunci a wannan zamanin??

Address

Zaria
Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Masoya Dr Alkali salihu Zaria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category