09/04/2026
Assalamu'alaikum barkan mu da wannan lokaci fatan alkhairi da fatan nasara.
Amadadin al-ummar wannan yanki namu mai albarkar. Wato yammacin Kargi. Wanda yahada garuruwa kamar haka. BAKARA, KURAYE, UNGUWAR SODA, KAMFA, UNGUWAR MA'ARU, JAMA'ARE, KULIN KARABA, UNGUWAR MAI GADA, DA KARABA.
Zamuyi amfani da wannan damar domin isar da sakon al-umman wannan yanki da na kungiyoyin matasa kamar haka.
BAKARA YOUTH DEVELOPMENT ASSOCIATION.
WESTERN KARGI INITIATIVE FOR PEACE AND PROGRESS.
NEMAN YANCI MATASA NA KUBAU LG.
Amadadin dukkan wannan kungiyoyi da al umman wannan yanki mai albarka.
Muna mika saqon godiya da jinjinan bangirma da bangajiya bisa ziyarar aiki da BZ yakai wannan yanki mai albarka.
ACCOUNTER GENARAL na Kaduna State,
Bashir Sulaiman Zuntu. dan takaran kujerar majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar, IKARA / KUBAU. yakai ziyarar aiki wanda akafara jiya laraba kungiyoyin matasa da al-umman yanki ne s**a shirya aikin gayya, domin gyara hanyar su wanda ta tashi daga garin Kargi zuwa Unguwar Soda, Unguwar Maigada, Bakara, Jama'are, Kuraye, Unguwar Ma'aru, Kamfa, Kulin Karaba zuwa Karaba.
Megirma AG yabi wannan hanya gaba dayanta inda yaje har daji wajen da ake hako burji domin zubawa akan hanyar, inda ananne yayi jawabai masu yawa.
Bashir Sulaiman Zuntu acikin jawabin nasa yayi godiya da jinjina ga Matasa bisa kokari da jajircewa da sukeyi wajen fitowa subada gudunmawar su ga wannan aiki. yayi godiya ga saraku damasu ungunni da kungiyoyin da suke shirya wannan aiki lokaci zuwa lokaci. A wannan ziyara kuma nan take yaba da gudunmawar kudi mai yawa, kuma yayi alkawarin isar da saqon al-umman wannan yanki ga mai girma Gwabna yace insha Allah su zasuyi sanadiyyar wannan hanyar da tsayinta befi km 10 zuwa 15 ba.
Ziyarar tashi tasami rakiyar manyan jigajigan jam'iyyar APC na karamar hukumar Kubau Kaduna State irin su
Vice Chairman Kubau LGA. Jafaru Ibrahim Kubau
Alhaji Haruna Gaja Gaja
Alhaji Idris Saleh Kargi
Speeker Kubau LGA Malam Salmanu
Kasilan mazabar Kargi Comrd Gaddafi Yusuf
Shugaban Jam'iyyar APC Kargi ward, Isah Ado
Sakaran Jam'iyyar APC Kargi ward Sule Karaba
Shugaban yan Midiya Kubau LGA Abdulrashid Dauda ( Prince Prince) da dai sauransu
Ubangiji Allah yasaka da alkhairi mungode
đź–‹MAHMUD A YAKUBU đź–‹