The Secretary Zaria LG

The Secretary Zaria LG This is the official page of the Office of the Council Secretary, Zaria Local Government

A yau, Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), daga cikin manufofinsa na bada dama da kuma...
12/05/2026

A yau, Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), daga cikin manufofinsa na bada dama da kuma hada kai da kungiyoyi don cigaban alโ€™umma, yayin da yake wakiltar Shugaban Karamar Hukumar Zariya, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), ya karbi bakuncin tawaga da mambobin kungiyar โ€œ๐Š๐€๐’๐€๐‡๐€ ๐Š๐–๐€๐‘๐€๐ˆ๐Š๐€๐“๐”๐Š๐€ ๐‚๐Ž๐Œ๐Œ๐”๐๐ˆ๐“๐˜ ๐ƒ๐„๐•๐„๐‹๐Ž๐๐Œ๐„๐๐“ ๐€๐’๐’๐Ž๐‚๐ˆ๐€๐“๐ˆ๐Ž๐ ๐™๐€๐‘๐ˆ๐€โ€ da kuma โ€œ๐“๐”๐ƒ๐”๐ ๐‰๐”๐Š๐”๐ ๐–๐Ž๐Œ๐„๐ ๐€๐–๐€๐‘๐„๐๐„๐’๐’ ๐…๐Ž๐‘๐”๐Œโ€ a ofishinsa.

Sunkai ziyarar ne domin kara karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnatin karamar hukumar Zaria da kungiyoyin wajen bunkasa hadin kai, karfafa mata, da kuma ci gaban alโ€™umma a fadin Zaria.

Sakataren ya yaba wa kungiyoyin bisa jajircewarsu da gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban alโ€™umma, tare da tabbatar musu da ci gaba da samun goyon bayan karamar hukumar kan duk wasu shirye-shiryen da za su amfani jamaโ€™a.

Haka kuma, ya sake jaddada kudurin wannan gwamnati karkashin jagorancin Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga) na tabbatar da shugabanci mai bai wa kowa dama, hada kan alโ€™umma, da kuma dorewar ci gaba a matakin karkara.

๐—ฆ๐—ถ๐—ด๐—ป๐—ฒ๐—ฑ:
๐—›๐—ฎ๐˜€๐˜€๐—ฎ๐—ป ๐—ญ๐—ฎ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐˜†๐˜†๐—ฎ
๐—ฃ.๐—” ๐— ๐—ฒ๐—ฑ๐—ถ๐—ฎ ๐—ฎ๐—ป๐—ฑ ๐—–๐—ผ๐—บ๐—บ๐˜‚๐—ป๐—ถ๐—ฐ๐—ฎ๐˜๐—ถ๐—ผ๐—ป
๐—ข๐—ณ๐—ณ๐—ถ๐—ฐ๐—ฒ ๐—ผ๐—ณ ๐˜๐—ต๐—ฒ ๐—–๐—ผ๐˜‚๐—ป๐—ฐ๐—ถ๐—น ๐—ฆ๐—ฒ๐—ฐ๐—ฟ๐—ฒ๐˜๐—ฎ๐—ฟ๐˜†
๐—ญ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ฎ ๐—Ÿ๐—ผ๐—ฐ๐—ฎ๐—น ๐—š๐—ผ๐˜ƒ๐—ฒ๐—ฟ๐—ป๐—บ๐—ฒ๐—ป๐˜
11๐˜๐—ต ๐—”๐—ฝ๐—ฟ๐—ถ๐—น, ๐Ÿฎ๐Ÿฌ๐Ÿฎ๐Ÿฒ

JUMMAโ€™AT MUBARAK ๐Ÿ“ฟ๐Ÿ•ŒYA ALLAH! Grant us peace of mind and keep our hopes alive. Many feel broken and in need of comfort. I...
08/05/2026

JUMMAโ€™AT MUBARAK ๐Ÿ“ฟ๐Ÿ•Œ

YA ALLAH! Grant us peace of mind and keep our hopes alive. Many feel broken and in need of comfort. It may be hard for some to focus on blessings when times are tough. When storms are brewing and days look dark, guide us to the path of light. Aameen.

Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), a yau, yayin da yake wakiltar Shugaban Karamar Huk...
06/05/2026

Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), a yau, yayin da yake wakiltar Shugaban Karamar Hukumar, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), ya karba bakuncin wasu kungiyoyin siyasa, masu ruwa da tsaki, da kuma sauran mutane dabandaban a ofishinsa.

Daga cikin wadanda s**a kai ziyarar akwai matasa daga Gundumar Wucicciri wadanda suke karkashin kungiya mai suna Uba Sani and Abbas Tajudden Continuous Support Group. Kungiyar ta kai ziyarar ne domin tabbatar da biyayyarsu, nuna gamsuwa da jagorancin gwamnatin APC, tare da tattauna dabarun da za su bi dangane da harkokin siyasa mai zuwa da kuma yadda za su ci gaba da goyon bayan jamโ€™iyyar APC a dukkan matakai.

A wata ganawar, Sakataren ya kuma karbi bakuncin shugabanni da mambobin Uba Sani Ambassadors, wata kungiya mai tsari da kuma manufa ta wayar da kan jamaโ€™a da goyon bayan siyasa domin tabbatar da manufofin Jamiyyar APC a Karamar Hukumar Zaria.

A yayin tattaunawar, an mayar da hankali kan karfafa tsarin cikin gida, magance wasu batutuwan kungiyoyi, da kuma daidaita dabaru da za su inganta hadin kai tsakanin kungiyoyin goyon baya da ke aiki a karkashinsa, gabanin zabukan da ke tafe.

๐—ฆ๐—ถ๐—ด๐—ป๐—ฒ๐—ฑ:
๐—›๐—ฎ๐˜€๐˜€๐—ฎ๐—ป ๐—ญ๐—ฎ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐˜†๐˜†๐—ฎ
๐—ฃ.๐—” ๐— ๐—ฒ๐—ฑ๐—ถ๐—ฎ ๐—ฎ๐—ป๐—ฑ ๐—–๐—ผ๐—บ๐—บ๐˜‚๐—ป๐—ถ๐—ฐ๐—ฎ๐˜๐—ถ๐—ผ๐—ป
๐—ข๐—ณ๐—ณ๐—ถ๐—ฐ๐—ฒ ๐—ผ๐—ณ ๐˜๐—ต๐—ฒ ๐—–๐—ผ๐˜‚๐—ป๐—ฐ๐—ถ๐—น ๐—ฆ๐—ฒ๐—ฐ๐—ฟ๐—ฒ๐˜๐—ฎ๐—ฟ๐˜†
๐—ญ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ฎ ๐—Ÿ๐—ผ๐—ฐ๐—ฎ๐—น ๐—š๐—ผ๐˜ƒ๐—ฒ๐—ฟ๐—ป๐—บ๐—ฒ๐—ป๐˜
6๐˜๐—ต ๐—”๐—ฝ๐—ฟ๐—ถ๐—น, ๐Ÿฎ๐Ÿฌ๐Ÿฎ๐Ÿฒ

A yau, Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), karkashin jagorancin Shugaban Karamar Hukum...
05/05/2026

A yau, Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), karkashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), ya ci gaba da ganawa da muhimman masu ruwa da tsaki, don kara tabbatar da kudurin wannan gwamnati na rungumar kowa da kuma inganta hadin gwiwa a matakin kasa.

Daga cikin wadanda ya karba akwai shugabanni da mambobin Kungiyar Tinubu/Uba Sani Continuous Support Group. Tawagar ta kai ziyarar ban girma domin sake gabatar da kansu a matsayin wata kungiya mai kishin Jamโ€™iyyar ta APC wacce ta taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jamaโ€™a da goyon baya ga jamโ€™iyyar APC a fadin Jihar Kaduna. Sun sake jaddada biyayyarsu da rikon amana ga manufofin jamโ€™iyyar, tare da bayyana aniyarsu ta ci gaba da kokarin karfafa jamโ€™iyyar a dukkan matakai.

Haka kuma, Sakataren ya karbi bakuncin mambobin Kungiyar Masu Sayar da Wayoyi da Injiniyoyi ta Karamar Hukumar Zaria mai suna Association of Phone Sales and Engineers, Zaria Local Government. Kungiyar ta ziyarci ofishin ne domin nuna godiya ga Sakataren bisa manufofinsa na bude kofa ga kowa da kuma saukin kai wajen muโ€™amala. Taron ya gudana cikin fahimta da tattaunawa mai maโ€™ana, inda aka mayar da hankali kan hadin gwiwa da rawar da kananan โ€˜yan kasuwa ke takawa wajen cigaban alโ€™umma.

A yayin ganawar, Kungiyoyin biyu sun kuma bayyana matsayinta na siyasa tare da nuna cikakken goyon bayanta ga jamโ€™iyyar APC, inda s**a jaddada kudurinsu na bada gudunmawa ga cigaban jamโ€™iyyar a cikin karamar hukumar Zaria.

๐—ฆ๐—ถ๐—ด๐—ป๐—ฒ๐—ฑ:
๐—›๐—ฎ๐˜€๐˜€๐—ฎ๐—ป ๐—ญ๐—ฎ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐˜†๐˜†๐—ฎ
๐—ฃ.๐—” ๐— ๐—ฒ๐—ฑ๐—ถ๐—ฎ ๐—ฎ๐—ป๐—ฑ ๐—–๐—ผ๐—บ๐—บ๐˜‚๐—ป๐—ถ๐—ฐ๐—ฎ๐˜๐—ถ๐—ผ๐—ป
๐—ข๐—ณ๐—ณ๐—ถ๐—ฐ๐—ฒ ๐—ผ๐—ณ ๐˜๐—ต๐—ฒ ๐—–๐—ผ๐˜‚๐—ป๐—ฐ๐—ถ๐—น ๐—ฆ๐—ฒ๐—ฐ๐—ฟ๐—ฒ๐˜๐—ฎ๐—ฟ๐˜†
๐—ญ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ฎ ๐—Ÿ๐—ผ๐—ฐ๐—ฎ๐—น ๐—š๐—ผ๐˜ƒ๐—ฒ๐—ฟ๐—ป๐—บ๐—ฒ๐—ป๐˜
5๐˜๐—ต ๐—”๐—ฝ๐—ฟ๐—ถ๐—น, ๐Ÿฎ๐Ÿฌ๐Ÿฎ๐Ÿฒ

Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), karkashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar Zaria, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Ja...
05/05/2026

Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), karkashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar Zaria, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), ya ci gaba a yau da gudanar da ganawa da kungiyoyi da sauran mutane daban daban a ofishinsa, inda hakan ke kara tabbatar da kudirin wannan gwamnati na bude kofa ga kowa da kuma bai wa matasa dama.

Daga cikin wadanda ya karba akwai dan takarar shugabancin Kungiyar Daliban Zazzau ta Kasa (NAZAS), mai suna Bilal Bashir wanda ya kai ziyarar girmamawar domin neman goyon baya, shawarwari gabanin zabukan kungiyar da ke tafe.

A yayin ganawar, Sakataren ya jaddada muhimmancin shugabanci mai dogaro da gaskiya, daโ€™a, da hidima ga alโ€™umma. Ya kuma karfafa wa dan takarar gwiwa da ya kasance mai mai da hankali, ya rungumi dabiโ€™un hadin kai da zaman tare, tare da fifita jin dadin dalibai idan aka ba shi damar jagoranci.

๐—ฆ๐—ถ๐—ด๐—ป๐—ฒ๐—ฑ:
๐—›๐—ฎ๐˜€๐˜€๐—ฎ๐—ป ๐—ญ๐—ฎ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐˜†๐˜†๐—ฎ
๐—ฃ.๐—” ๐— ๐—ฒ๐—ฑ๐—ถ๐—ฎ ๐—ฎ๐—ป๐—ฑ ๐—–๐—ผ๐—บ๐—บ๐˜‚๐—ป๐—ถ๐—ฐ๐—ฎ๐˜๐—ถ๐—ผ๐—ป
๐—ข๐—ณ๐—ณ๐—ถ๐—ฐ๐—ฒ ๐—ผ๐—ณ ๐˜๐—ต๐—ฒ ๐—–๐—ผ๐˜‚๐—ป๐—ฐ๐—ถ๐—น ๐—ฆ๐—ฒ๐—ฐ๐—ฟ๐—ฒ๐˜๐—ฎ๐—ฟ๐˜†
๐—ญ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ฎ ๐—Ÿ๐—ผ๐—ฐ๐—ฎ๐—น ๐—š๐—ผ๐˜ƒ๐—ฒ๐—ฟ๐—ป๐—บ๐—ฒ๐—ป๐˜
5๐˜๐—ต ๐—”๐—ฝ๐—ฟ๐—ถ๐—น, ๐Ÿฎ๐Ÿฌ๐Ÿฎ๐Ÿฒ

A yau, Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), karkashin jagorancin Shugaban Karamar Hukum...
04/05/2026

A yau, Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), karkashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), ya karbi tawagar Shugabanni da mambobi daga kungiyar TINUBU/UBA SANI GRASSROOTS EXPANSION MOVEMENT 2027 (TUGEM) a Zaria.

Kungiyar, wadda Hon. Aliyu Usman (Aliko) ya kafa, kungiyar an kafata ce ta domin tsarawa da tabbatar da grassroots mobilization , kuma an samar da ita domin wayar da kai da fadadaa goyon bayan Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Uba Sani, da dukkan โ€˜yan takarar jamโ€™iyyar APC a Zaria da ma sauran wurare. Wannan tsari yana gudana ne karkashin jagoranci da kulawar Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter) da Darakta Janar na Kaduna State Schools Quality Assurance Authority (KSSQAA), Farfesa Usman Abubakar Zaria.

A yayin ganawar, Sakataren ya yaba da kokaari da jajircewar shugabanni da mambobin kungiyar, musamman yadda s**a tsara tsarin su da inganci da tsari mai kyau domin tabbatar da isar da sako da hulda da jamaโ€™a a matakin kasa.

Ya jaddada muhimmancin hadin kai da tsari wajen karfafa dimokuradiyya da kuma ci gaban siyasa a matakin karamar hukumar. Haka kuma ya karfafa musu gwiwa da su ci gaba da jajircewa da mai da hankali wajen cimma manufofinsu.

A matsayin tallafi ga ayyukansu, Sakataren ya ba da gudummawar Naira Dubu Dari Biyu (โ‚ฆ200,000) domin taimaka wa ฦ™ungiyar wajen gudanar da ayyukanta.

๐—ฆ๐—ถ๐—ด๐—ป๐—ฒ๐—ฑ:
๐—›๐—ฎ๐˜€๐˜€๐—ฎ๐—ป ๐—ญ๐—ฎ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐˜†๐˜†๐—ฎ
๐—ฃ.๐—” ๐— ๐—ฒ๐—ฑ๐—ถ๐—ฎ ๐—ฎ๐—ป๐—ฑ ๐—–๐—ผ๐—บ๐—บ๐˜‚๐—ป๐—ถ๐—ฐ๐—ฎ๐˜๐—ถ๐—ผ๐—ป
๐—ข๐—ณ๐—ณ๐—ถ๐—ฐ๐—ฒ ๐—ผ๐—ณ ๐˜๐—ต๐—ฒ ๐—–๐—ผ๐˜‚๐—ป๐—ฐ๐—ถ๐—น ๐—ฆ๐—ฒ๐—ฐ๐—ฟ๐—ฒ๐˜๐—ฎ๐—ฟ๐˜†
๐—ญ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ฎ ๐—Ÿ๐—ผ๐—ฐ๐—ฎ๐—น ๐—š๐—ผ๐˜ƒ๐—ฒ๐—ฟ๐—ป๐—บ๐—ฒ๐—ป๐˜
๐Ÿฐ๐˜๐—ต ๐—”๐—ฝ๐—ฟ๐—ถ๐—น, ๐Ÿฎ๐Ÿฌ๐Ÿฎ๐Ÿฒ

BARKA DA JUMAโ€™AHYa Ubangijinmu, ka ba mu alheri a duniya, ka ba mu alheri a lahira, ka tsare mu daga azabar wuta. Ameen
01/05/2026

BARKA DA JUMAโ€™AH

Ya Ubangijinmu, ka ba mu alheri a duniya, ka ba mu alheri a lahira, ka tsare mu daga azabar wuta. Ameen

A yau, Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), yayin da yake wakiltar Shugaban Karamar Huk...
30/04/2026

A yau, Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), yayin da yake wakiltar Shugaban Karamar Hukumar, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), ya karbi bakuncin mutane daban-daban da kungiyoyin masu ruwa da tsaki a ofishinsa.

Daga cikin wadanda ya karba akwai Comrade Sani Ibrahim Ndagana (Ajeeb Dan Gaske), dan takarar shugaban Dalibai na National Association of Zazzau Students (NAZAS), tare da tawagarsa. Dan takarar ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin neman goyon baya da shawarwari daga Sakataren, yayin da yake takara na wakiltar dalibai a kananan hukumomi goma sha daya na lardin Zazzau.

A nasa jawabin, Sakataren ya yaba da ziyarar tare da ba shi shawarwari masu muhimmanci, inda ya bukace shi da ya kasance cikin shiri ko dai na nasara ko akasin haka. Ya kuma jaddada muhimmancin sadaukar da kai, juriya, da gaskiya a shugabanci, bisa laโ€™akari da kwarewarsa a harkokin siyasa.

Haka kuma, Sakataren ya karbi bakuncin tawagar kungiyar UBA SANI 2WICE MOVEMENT, wadda fitacciyar kungiyar goyon bayan gwamna Senator Uba Sani ce a Zaria da Jihar Kaduna, karkashin jagorancin Kwamishinan Kudi, Ibrahim T. Muhammed. Sun kai ziyarar ne domin gaisuwa da nuna goyon bayansu.

Sakataren ya yabawa kokarinsu tare da sake jaddada goyon bayansa ga manufofin kungiyar, yana mai nuna kudurinsa na ci gaba da tallata shugabancin Gwamna Uba Sani da jamโ€™iyyar APC a Zaria. Haka kuma ya yabawa shugabannin kungiyar bisa kokarinsu wajen ganin nasarar jamโ€™iyyar APC a zaben 2027 mai zuwa.

Daga karshe, Sakataren ya karbi bakuncin mambobin JUSHI YOUTH PROGRESSIVE FORUM karkashin jagorancin Mallam Mustapha. Kungiyar ta bayyana ayyukanta da s**a hada da daukar nauyin jarabawar JAMB ga dalibai, tallafawa masu kananan sanaโ€™oโ€™i, shirye-shiryen horaswa, da ayyukan ci gaban alโ€™umma. Sun kuma jaddada goyon bayansu ga ayyukan gwamnati da kuma kudurinsu na ganin jamโ€™iyyar APC ta samu nasara a zabuka masu zuwa.

A nasa jawabin, Sakataren ya yaba da irin gudunmawar da kungiyar ke bayarwa wajen ci gaban alโ€™umma. A matsayinsa na dan unguwar Jushi, ya bayyana cikakken goyon bayansa da alakar sa da kungiyar. A matsayin tallafi ga ayyukansu, ya amince da bayar da gurbin tallafawa mata guda goma (10) domin bunkasa kananan sanaโ€™oโ€™insu.

๐—ฆ๐—ถ๐—ด๐—ป๐—ฒ๐—ฑ:
๐—›๐—ฎ๐˜€๐˜€๐—ฎ๐—ป ๐—ญ๐—ฎ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐˜†๐˜†๐—ฎ
๐—ฃ.๐—” ๐— ๐—ฒ๐—ฑ๐—ถ๐—ฎ ๐—ฎ๐—ป๐—ฑ ๐—–๐—ผ๐—บ๐—บ๐˜‚๐—ป๐—ถ๐—ฐ๐—ฎ๐˜๐—ถ๐—ผ๐—ป
๐—ข๐—ณ๐—ณ๐—ถ๐—ฐ๐—ฒ ๐—ผ๐—ณ ๐˜๐—ต๐—ฒ ๐—–๐—ผ๐˜‚๐—ป๐—ฐ๐—ถ๐—น ๐—ฆ๐—ฒ๐—ฐ๐—ฟ๐—ฒ๐˜๐—ฎ๐—ฟ๐˜†
๐—ญ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ฎ ๐—Ÿ๐—ผ๐—ฐ๐—ฎ๐—น ๐—š๐—ผ๐˜ƒ๐—ฒ๐—ฟ๐—ป๐—บ๐—ฒ๐—ป๐˜ ๐—–๐—ผ๐˜‚๐—ป๐—ฐ๐—ถ๐—น
๐Ÿฏ๐Ÿฌ๐˜๐—ต ๐—”๐—ฝ๐—ฟ๐—ถ๐—น, ๐Ÿฎ๐Ÿฌ๐Ÿฎ๐Ÿฒ

30/04/2026

Alhamdulillah, Allah ya taimake Mu.

A yammacin yau, wata kungiyar jajirtattun matasa wadda ta kunshi mata da maza muasu dogaro da kansu mai suna Modern Desi...
28/04/2026

A yammacin yau, wata kungiyar jajirtattun matasa wadda ta kunshi mata da maza muasu dogaro da kansu mai suna Modern Design Tailoring Organization daga Tudun Wada, Zaria, ta kai ziyarar ban girma ga Sakataren Karamar Hukumar, Hon. Shuaibu Abdullahi, a office dinsa, yayin da yake wakiltar Shugaban Karamar Hukuma, Engr. Jamil Ahmad Muhammad.

Kungiyar ta bayyana ziyarar tasu da nufin sake jaddada cikakken goyon bayansu ga Sakataren da kuma jamโ€™iyyar APC a Zaria. Haka kuma sun yi amfani da wannan dama wajen bayyana kudirorinsu na inganta manufofinsu na siyasa da kuma ayyukan ci gaban alโ€™umma.

A matsayin girmamawa ga shugabancinsa da kuma jajircewarsa wajen gudanarwa, tawagar ta karrama Sakataren da lambar yabo ta kwarewa (Award of Excellence).

A nasa jawabin, Sakataren ya nuna godiya bisa ziyarar tare da yaba wa kungiyar kan hadin kansu, dogaro da kai, da kuma rawar da suke takawa a siyasance da kuma wajen ci gaban alโ€™umma. Domin karfafa musu gwiwa da tallafawa ga ayyukansu, ya ba su gudummawar Naira dubu hamsin (N50,000) domin su ci gaba da bunkasa kungiyar da ayyukanta.

๐—ฆ๐—ถ๐—ด๐—ป๐—ฒ๐—ฑ:
๐—›๐—ฎ๐˜€๐˜€๐—ฎ๐—ป ๐—ญ๐—ฎ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐˜†๐˜†๐—ฎ
๐—ฃ.๐—” ๐— ๐—ฒ๐—ฑ๐—ถ๐—ฎ ๐—ฎ๐—ป๐—ฑ ๐—–๐—ผ๐—บ๐—บ๐˜‚๐—ป๐—ถ๐—ฐ๐—ฎ๐˜๐—ถ๐—ผ๐—ป
๐—ข๐—ณ๐—ณ๐—ถ๐—ฐ๐—ฒ ๐—ผ๐—ณ ๐˜๐—ต๐—ฒ ๐—–๐—ผ๐˜‚๐—ป๐—ฐ๐—ถ๐—น ๐—ฆ๐—ฒ๐—ฐ๐—ฟ๐—ฒ๐˜๐—ฎ๐—ฟ๐˜†
๐—ญ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ฎ ๐—Ÿ๐—ผ๐—ฐ๐—ฎ๐—น ๐—š๐—ผ๐˜ƒ๐—ฒ๐—ฟ๐—ป๐—บ๐—ฒ๐—ป๐˜
๐Ÿฎ๐Ÿฒ๐˜๐—ต ๐—”๐—ฝ๐—ฟ๐—ถ๐—น ๐Ÿฎ๐Ÿฌ๐Ÿฎ๐Ÿฒ

Address

Zaria Local Government Sectariat
Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when The Secretary Zaria LG posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share