KOMAI NISAN DARE

KOMAI NISAN DARE Abuabdullah Samaru

04/03/2025
04/03/2025

Wasu matan suna ganin kamar shayarwa ko ciki dalili ne da yake halatta musu barin azumi, hakan ba daidai ba ne. Mace mai ciki ko shayarwa kamar mara lafiya ne, idan rashin lafiyar ba za ta cutar da shi ba, dole zai yi azumi, haka su ma, sai idan akwai tsoron yin azumin zai iya cutar da lafiyarta ko lafiyar jinjirin da ke cikinta ko take shayarwa, shi ne ya halatta su ajiye, daga baya su rama, kamar yadda mara lafiya zai rama.

04/03/2025

Mata waɗanda aikace-aikacen gida da shirin abincin buɗa-baki ba su barinsu su samu natsuwa sosai wajen yawaita ibada, su sani, ayyukan hidimar samar da abin buɗa-baki shi ma ibada ne, niyya kawai za ki tsarkake. Sa'an nan duk da haka ki riƙa ƙoƙari wajen yin abin da ya sawwaƙa don ki jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya.

04/03/2025

Masu ciki da masu shayarwa dole sai sun rama azumi, ba ciyarwa a madadin azumi ba. An tambayi Bin Baz game da ciyarwar masu ciki da shayarwa a madadin azumi, sai ya ce: "An ruwaito hakan daga Ibnu Abbas da Ibnu Umar, amma magana ce mai rauni wadda ta saɓa da dalilai na shari'a. Mai ciki da mai shayarwa suna da hukuncin mara lafiya ne, ba hukuncin tsoho ko mara lafiya waɗanda ba su iya azumi ba".

04/03/2025

Babu laifi amma dai a kiyaye!

An tanbayi Imam Ahmad, shin mutum zai iya sumbatar muharramarsa babba... Sai ya ce: E, in baya jin tsoron faruwar wani abu.

Malamai s**a ce: kamar in ya dawo daga tafiya, ko yayin bankwana, ko nuna tausayi da qauna, a hannunta ko kanta ko kuncinta, amma banda bakinta, wannan baya halasta, baki na ma'urata ne kadai.

Hakan nan zai iya rungumeta, duka da sharadin kubuta daga fitina, daga gare shi ko gareta.
Amma in har yin hakan zai iya motsa shawar mahaifin ko diyar to baya halasta, haramun ne.

Shaikh Magaji Zarewa

04/03/2025

Talaka Bawan Allah

Address

Hayin Dogo Samaru Zaria Kaduna State
Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when KOMAI NISAN DARE posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category