04/12/2025
DANMALIKIN ZURMI LIKE-MIND UPDATE
4th December, 2025
Kaitsaye daga Zawuyyar Marigayi Sheikh Umar Rabi'u Zurmi.
Alhamdulillah. A bisa umarnin jagororin wannan kungiya, mun samu hannunta tamu gudunmawar lemunan roba (drinks) zuwa ga kwamitin gudanar da Mauludin Zagaye a garin Zurmi, karkashin jagorancin Malam Sabo Umar Zurmi. Mun hannunta wadannan kaya ne ga shugaban kwamitin saukar da baki wato, Malam Abdulkarim Nasarawa da wasu mukarabban shi.
Kuma mun samu kyawawan tarbo tare da addu'o'in fatan samun nasara daga dukkanin ilahirin malamai da daliban su. Allah Yasa a yi lafiya, kuma a kare lafiya.
Allah Ya bamu nasara, Ya kuma bai wa Alhaji Ahmed Abubakar Zurmi wakilcin Zurmi da Shinkafi cikin sauki.
Wassalam.
DANMALIKIN ZURMI LIKE MINDS