Umar faruq na kabobi

Umar faruq na kabobi Umar faruk na kabobi
Katsina state Kaita L G

MUTANE KALAR BIYAR 5 NA ROKE KU DON ALLAH KU CIRE SU A RAYUWARKU..Akwai wasu mutane guda biyar wadanda ko jinin jikinka ...
12/04/2026

MUTANE KALAR BIYAR 5 NA ROKE KU DON ALLAH KU CIRE SU A RAYUWARKU..

Akwai wasu mutane guda biyar wadanda ko jinin jikinka ne, matukar suna da wadannan halayen wallahi kaska ne wadanda suke tsotse maka farin ciki. Ga su nan:

1. Wanda Ka Yiwa 99 Ya Manta Saboda 1: Mutumin da zaka narkar da gumi da dukiyarka a kansa sau 99, amma ranar da ka gaza ko ka ce ba zaka iya ba sau 1, zai manta duk alherin da ka taba yi masa ya maida kai mugu.

2. Munafuki Mai Taya Ka Kuka: Wanda idan ka samu nasara ba zai taba yi maka murna ba, amma idan wata faduwa ko asara ta same ka, shine na farko da zai zo ya nuna yana tausaya maka alhalin a ransa murna yake yi yaga baka da komai.

3. Mai Ci Da Kai Yana Ɓata Ka: Wanda yake cin abincinka, yake amfana da aljihunka da girmanka a gabanka, amma idan ya fita majalisa ko cikin mutane shine zai fara zubar maka da mutunci ya tona asirinka.

4. Wanda Bai Tausayin Gumin Ka: Mutumin da ko yaga kana fuskantar matsanancin hali ko kana bin bashi, bai damu ba. Burinsa kawai ka biya masa bukatarsa, tunda a lissafinsa kai baka da matsala.

5. Mai Son Ka A Lokacin Da Kake Da Shi: Wanda girmanka da kwarjininka a wajensa ya danganta da kudin dake aljihunka. Ranar da asirinka ya tonu, wallahi ko kallon arziki ba zai yi maka ba, zai daina sanin kana yi.

Dan uwa, ba wai tsanarsu zaka yi ba, kawai ka yanke mu'amala da su domin ka tsira da lafiyar kwakwalwarka.

Allah ya bamu ikon tsare mutuncinmu.
UMAR ALIYU DAHIRU✍️

Manzon Allah (ﷺ) ya ce:"Duk wanda ya lazimci neman gafarar Allah (Istigfari), Allah zai sanya masa mafita daga kowane ƙu...
28/03/2026

Manzon Allah (ﷺ) ya ce:
"Duk wanda ya lazimci neman gafarar Allah (Istigfari), Allah zai sanya masa mafita daga kowane ƙuncin rayuwa, Ya kuma yaye masa kowace damuwa, sannan zai azurta shi ta inda bai taɓa tsammani ba."

(Abu Dawud | Riyad as-Salihin 1873)

*🕌GORON JUMA,A🕌*_*Yaku Ƴan uwana kusani a yau ka ga wani ya yi aure, kai kuma har yanzu kana jira. Ka ga wani ya gina gi...
16/01/2026

*🕌GORON JUMA,A🕌*
_*Yaku Ƴan uwana kusani a yau ka ga wani ya yi aure, kai kuma har yanzu kana jira. Ka ga wani ya gina gida, kai kana haya. Ka ga wata ta yi arziki, kai kana fama. Amma tambaya ita ce: shin Allah Ya manta da kai? A’a. Kaddara ba ta yin kuskure. Lokaci ba ya makara. Abin da ke makara shi ne fahimtarmu. Hakuri ba rauni ba ne. Hakuri karfi ne. Hakuri hujja ce cewa ka yarda da tsarin Ubangiji. Duk wanda ya yi hakuri, ba yana nufin bai ji zafi ba; yana nufin ya yarda ya jira alkhairi maimakon ya karbi abin da bai shirya masa ba. 🙏🙏✅✅

Barkammu da juma,a
16/01/2026

Barkammu da juma,a

11/01/2026
Duk wuya duk rintsi kada kataba bari lokacin sallah yayi batare da katashi kayita ba 🫵👂👂
10/01/2026

Duk wuya duk rintsi kada kataba bari lokacin sallah yayi batare da katashi kayita ba 🫵👂👂

Alhamdulillah aka kulli halin 🥰
05/01/2026

Alhamdulillah aka kulli halin 🥰

Address

R/lemo Titin Jira
Otukpa

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Umar faruq na kabobi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category