Mubarak Adam Ala amfana

Mubarak Adam Ala amfana Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mubarak Adam Ala amfana, Grocers, Cairo.

21/11/2025
17/11/2025
15/11/2025

SALLAR DARE – ƘOFA TA SIRRIN RAYUWA

Ka taɓa jin yadda zuciya ke yin nauyi da damuwa, kamar babu mafita? Ko ka taɓa jin yadda kake son canji a rayuwarka amma kana rasa hanyar farawa? To, ka sani: akwai wata ƙofa da Allah ya buɗe musamman domin bayinsa masu neman ceto – wannan ƙofa ita ce Sallar Dare.

A lokacin da kowa ya yi bacci, duniya ta nutsu, sai kai da Ubangijinka kaɗai. Babu hayaniya, babu shishigi, babu jan hankali – sai kai da addu’a. Wannan lokacin ne ALLAH yake saukowa sama ta duniya yana cewa:
👉 “Wayyo wanene zai roƙe Ni, in amsa masa? Wayyo wanene zai nemi gafara, in gafarta masa?”

Ka ɗan yi tunani… idan ka rasa wannan damar, shin ba ka rasa mafi daraja ba?

Sallar dare ba sai ta daɗe ba.

Idan ka iya raka’a biyu ne ka tashi ka yi.

Ka yi sujada ɗaya da hawaye, ka roƙi ALLAH da gaske.

Ka faɗi bukatunka cikin sirri – nasara, lafiya, kariya, albarka.

Wallahi, duk wanda ya ɗan gwada wannan ibada, ya san daɗin rayuwar da babu komai sai ALLAH a zuciya.

📢 Kar ka tsaya kai kaɗai!
Turawa ɗan’uwa, aboki, ko wani group domin su ma su ci moriyar wannan sirri. Wataƙila rayuwar wani ta canza saboda wannan tunatarwa, kuma kai ka samu lada har abada.

🕋 Tashi daren yau ka gwada. Wataƙila wannan dare ne zai zama sabon farkon rayuwarka.

15/11/2025

YANZU-YANZU: Wata Bazawara Ta Bayyana Sharuddan Mijin Da Take Nema

Wata bazawara mai suna Hajiya ta bayyana cewa tana neman mijin aure nagari, wanda zai kasance mai kula da gida cikin aminci da jajircewa musamman idan ba ta nan.

Ta ce bukatarta ita ce ta samu abokin rayuwa mai gaskiya, rikon amana da kyakkyawan hali, wanda zai cika rawar da namiji ke takawa a cikin gida ba tare da wata matsala ba.

A cewarta, tana son aure na zaman lafiya, fahimtar juna da mutunta juna. Duk mai sha’awa zai iya turo da bayanansa ta hanyoyin da ta tanada domin ci gaba da tattaunawa.

SASHEN TALLACE TALLACE

_______________________________

Ko Kun San Cewa Kamfanin Freshdata Sun Karya Farashin Datar MTN 1GB ₦520.

Ga yadda tsarikan nasu yake.
👇🏽

(MTN SME 1GB ₦520)
(Airtel SME 1GB ₦360)
(9mobile 1GB ₦250)

Ga masu buƙatar referral code.
👇🏽
Freshdata

Website, freshdata.com.ng

Abin farin ciki Datar tana da ƙarfin da har sai ya kai kwana 30 kafin ƙarfinta ya ƙare. Hanzarta kayi download App a nan👇🏽
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.msorgdevelopers.freshdata

Idan kayi download sai kayi register, idan baka iya register ba sai ka tuntuɓi Agent a WhatsApp zasu koya maka yadda za kayi rijista kyauta.

07067488964
07035570974

Ga Link Whatsapp group Freshdata
https://whatsapp.com/channel/0029VaAzQRO9Bb61etDBwG0b

15/11/2025

BA SHA'AWA KAƊAI KE SA GABANKI JIƘEWA BA

Ba maza kaɗai ke iya fahimtar lafiyar al'uransu ba. Kamar yadda muka yi darasi a baya na yadda duk safiya gaban maza yake miƙewa idan suna bacci.
Suma mata suna da hanyar da suke iya gane suna cikin ƙoshin lafiya musamman ta ɓangaren farjinsu.

Sau tari wasu matan suna kokawa na yadda gabansu yake jiƙe a kullum. Wasu matan na ɗaukan hakan tamkar wata lalurace ko kuma yawan jaraba ce na son Jima'i, sam abun ba haka yake ba a cewar masana.

Shi gaban mace mai lafiya a kullum ana son ganinsa yana cikin naso da kuma danshi. Wannan ne yake tabbatar da mace na cikin koshin lafiya a ɓangaren al'auran ta, kamar yadda masana s**a tabbatar.
Wannan ruwan da yake jiƙa gaban mace ba ya nufin tana da ƙarfin sha'awa. Sai dai ruwane da yake wanke duk wani abu mara kyau da zaran ya shigeta.
Da yake Allah Ya halicci gaban mace a buɗe, hakan na iya sa cuta ta shigeta cikin sauƙi. Da wannan ne sai Allah Ya mata wani ruwa na daban daga jikinta da zai riƙa wanke mata gabanta lokaci zuwa lokaci ba tare da sai tayi amfani da ruwa ko sai a lokacin da ta zo tsarki ba. Ganin cuta na iya shiga gaban mace a kowani lokaci, sai Allah Ya hukunta aikin wannan ruwan gaban mace a kowani lokaci cikin awanni 24.
Mata masu ƙarancin shekaru sunfi ganin gabansu a jiƙe a ko yaushe. Hakan na kasancewa ne saboda yadda jinin jikinsu yake da lafiya da ƙuruciya. Sannan kuma basu samun wadatar yin Jima'i kamar yadda mace mai aure take samu. Domin yawan Jima'i yakan rage fitowar wannan ruwan a gaban mace. Haka nan idan mace shekarunta ya soma ja, ita ma ba kasafai za a riƙa ganin hakan daga gareta ba sai idan mace mai hali ce tana samun abincin da suke ƙara ni'ima sosai tana ci ko sha.

Masana sun hana mata amfani da f**a ko turare a gabansu. Domin gaban mace bai buƙatar wani ruwa ko sinadari daga waje domin ya wanke shi. Wannan ruwan dai dake fitowa a jikinki shine ruwan dake kula da tsaftace gabanki da kuma yaƙar duk wata cutar data tinkaro gabanki.
Don haka mata masu damuwa saboda yawan jiƙewa da gabansu yake yi su daina damun kansu. Lafiya ce suke da shi.

Haka kuma ba domin wannan ruwan ba da sun riƙa fama da cututtuka.
Shi yasa masana ke baiwa mata shawara su riƙa amfani da ruwan ɗumi wajen yin tsarki maimakon ruwan sanyi. Domin ruwan ɗumi na ƙara taimakawa wajen kashe cutukan dake gaban mace.
Yana kuma da kyau mata su riƙa amfani da kamfen da aka yi su da auduga wato cotton fabric underwears domin sun fi dacewa da kula da lafiyan gabansu maimakon sauran yaduka.

Ruwa a jiki da gaban mace. Shi yake sa ta zama mace. Duk macen da taga tana ɓata kayanta, kada ta ɗauka jarabace da ita, a'a lafiya ce. Sai dai daga lokacin da taga ruwan ya sauya launi kuma yana wari ko ƙarni. Tayi maza ta tuntuɓi likita.

15/11/2025

Ummul khairi, khairan in sha Allah

15/11/2025

Address

Cairo

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mubarak Adam Ala amfana posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category