14/11/2021
Lahadi:: 14/11/2021. NATSI: K/Magana 3:13-36. KAN MAGANA: Hikima tana da daraja. Karatun yau Tana nuna Mana yadda hikima Take, da Kumada Kuma irin sakamako da za mu samu idan muna da ita wato zamu kasance da farinciki Mai yawa kullayomi. Mu yarda cikin hikimar Allah a wurin mu tafi azurfa saboda tana da babban riba fiye da ta sahihiyar zinariya. Hikimar Allah tana kunshe da tsawon kwanaki saboda tafarkinta jamhuriyace. In mun dauki lokaci mun lura da sama zamu ga sun kasance bisa ga Hikimar Allah, haka kuma duniya. Muga yadda Rana,wata da taurari suna rataye a sararin sama. Akan me suke ratayawa? Babu wanda ya sani sai ubangiji Allah. In muna da Hikimar Allah,to, bazamu ji soron kowace matsifar duniyar Nan da take cike dazunubi (zab 23:4). Yan'uwa yana da kyau mu yi kokari mu zauna da kowa lafiya in ya yiwu. Wato kada mu hanawa makwabtanmu Rance,in muna da shi. Sa'adda muke yin haka,zamu guje wa mugunta ,mu nemi adalcin ubangiji,zaya bamu a yalwace ta wurin Hikimar sa. In mun lura karatu yana nuna gidajennuna gidajen mugaye zasu cika da la'anar ubangiji. Amma ga adalci,musu tsoron ubangiji, asirin Allah yana tare da su. Masu hikima Kuma zasu gaji daraja a Nan duniya da kuma a gaban Allah, to mu nemi hikimarsa. Mu ki duk komai da zai jawo mana kunya da fushin Allah. ABIN LURA: mu guji mugunta. ADDUA: Ya uba na sama,ka bani Hikimar ka domin in guje mugayen ayuka. Amin