06/12/2022
Yusaku Maezawa na gayyatar mutum takwas daga ko ina
afadin duniya don su raka shi wata tafiya da yake son yi zuwa
duniyar wata
Wani hamshakin attajiri dan Japan Yusaku Maezawa yana
gayyatar mutum takwas daga ko ina afadin duniya don su
raka shi wata tafiya da yake son yi zuwa duniyar wata a jirgin
SpaceX flight na Elon Musk.
"Ina son mutane daga ko ina su nemi yin wannan rakiya,"
kamar yadda ya fada a wani bidiyo da ya wallafa a Tuwita, inda
ya kuma wallafa adireshin intanet din da za a shiga a nemi
aikin rakiyar.
Ya ce shi zai dauki nauyin gaba daya tafiyar, don haka 'yan
rakiyar a garabasa za su je.
An sanya lokacin bulaguron mai taken dearMoon, ne a
shekarar 2003.
Wadanda za su nemi wanan rakiya na bukatar cika wasu
sharuda biyu: sai sun kasance duk abin da suke na taimakon
al'umma ne a wani fannin, kuma sai idan suna da burin
taimakon sauran abokan tafyar da suke da irin wannan buri, in
ji shi.
"Na sayi dukkan tikitin jirgin, don haka zai kasance tafiya ce ta
kashin kai," ya kara da cewa.
Mr Maezawa, hamshakin mai arzikin a fannin kayan kawa,
kuma fasihi, a baya ya ce ya shirya gayyatar fasihai don yin
tafiyar tare, amma sai aka gyara tsarin ta yadda mutane daga
sassan duniya daban-daban za su samu damar bin jirgin.
"Idan kana kallon kanka a matsayin fasihi, to kai fasihi ne," a
cewarsa.
A bara, ya kaddamar da wani shiri na neman sabuwar
budurwar da za ta raka shi a bulaguron, kafin daga bisani ya
fasa saboda tunani daban-daban.
A shekarar 2018, an ambaci Mr Maezawa a matsayin fasinjan
farko mai zaman kansa da zai yi zagaye a duniyar wata a jirgin
SapceX, na kamfanin Elon Musk.
Ba a bayyana yawan kudin da Mr Maezawa zai biya na tikitin
jirgin ba, amma Elon Musk ya ce makudan kudade ne.
Shirin zuwa duniyar wata na 20223 shi ne zai zama na farko da
dan adam zai yi tun bayan shekarar 1972.