05/05/2025
Please admin approved 🙏....
Ina zaune agidan mu ƙawata ta kirani tace" humaira Dan Allah ki taimake ni kizo kiyiwa hajiya ƙarya ta barmu mu fita wallahi hubby ne baida lafiya inason naje na ganshi Dan Allah humaira"
Nace" gaskiya Maryam bazan iya ba hajiya tana ganin mutuncin na bazan mata ƙarya na zubda mutuncin Nan ba"
Maryam tace" haba ƙawata Dan Allah ki taimake ni kizo "
Nace " badamuwa ga ninan zuwa"
Naje na samu hajiya mukagaisa nace hajiya dama aunty Zainab ce takirani tace Dan Allah nazo na roƙeki kibar Maryam muje mutaya ta aiki"
Hajiya tace " badamuwa Amman Dan Allah karku daÉ—e saboda yau yayanta zai dawo Kuma kinsan baya son yawo "
Nace" insha Allahu zamu dawo da wuri " naje na jira Maryam ta shirya muka fito tace Dan Allah humaira muje ki rakani "
Nace gaskiya bazan je ba ni gidan aunty Zainab zanje"
Tace" tohh shikkenan ta gode"
Nace " Dan Allah Maryam karki daÉ—e "
Tace" insha allahu "
A bun mamakin shine Maryam Bata dawo gida ba har mangariba hajiya ta kirani tace" Muna Ina ne ga yayanta ya dawo Yana nemanta nace ai ta tafo tun ɗazu Bata ƙariso bane?"
Wasa gaske Abu har bayan isha Maryam Bata koma gida ba lokacin ni Kuma har na koma gidan mu Dan tun kafin la'asar na koma ,
Hankali na yayi mungun ta shi ni da 'yan gidan mu da Kuma 'yan gidansu Maryam hajiya ta kira Aunty Zainab ta tambayeta ko Maryam ta koma na aunty Zainab take shaida mata ai ni kaɗai naje Maryam bataje ba Abu dai har kwana ɗaya shiru Nan zargi ya haukaina na shiga ta shin hankali matuƙa ......
Zanci gaba labarin Nan a gaske ya faru