27/09/2025
Lokacin da uwa ta kafa wa ɗanta sharadi ta ce masa: “A’a” ⛔
Sai wani babba, ko mahaifinsa, ko kakansa, ko kakarsa ya tsoma baki ya ce:
“Ki bar shi, babu matsala, kar ki tsaurara masa…”
🔁 A nan ne ake fara shuka rudani a cikin zuciyar yaro.
👦 A ganinsa:
Uwa = wacce ta ƙi yarda tana tsaurarawa ❌
Sauran manya = wadanda s**a yarda suna sauƙaƙa masa ✅
Haka al'amarin yake canzawa a kwakwalwarsa:
🚫 Matsayin uwa a wajen shi yana samun tan garɗa,
🚫 Ikonta akan shi yana raunana,
🚫 Yaro kuma yana fara yin watsi da umarnin ta, yana samun ruɗani tsakanin aikin daidai da kuskure.
👨👩👧 Yaro yana buƙatar a samu daidaito akan magana ɗaya, ba maganganu masu karo da juna ba.
Tarbiyya mai kyau ba ta bunƙasa a cikin gidan da ke cike da sabanin ra’ayi, amma ana iya samun ta a cikin yanayin fahimta da haɗin kai tsakanin iyalai.
🎯 Idan kuna son tallafa wa uwa: ✅ Ku zama masu taimaka mata wajen aiwatar da dokoki, ba masu kawo mata cikas wanda zai rusa ƙoƙarinta ba.
Idan kuma akwai buƙatar a sake duba lamarin, to a yi hakan ba tare da yaro ya gani ko ya ji ba, domin kiyaye daraja da girmanta a idonsa.
📌 Muhimman abubuwan da suke sa a samu daidaiton tarbiyya a cikin gida:
1️⃣ Ku zama a kan ra’ayi guda ɗaya akan ƙa’idojin tarbiyya.
2️⃣ Kada ku yi sabani a gaban yaro; don kada ya ji zai iya daukar mataki da kansa ko ya zaɓi ɓangare ɗaya a cikin ku.
3️⃣ Ku fifita amfanin tarbiyya mai dorewa fiye da jin daɗin zuciya na ɗan ƙanƙanin lokaci.
4️⃣ Ku tuna: tarbiyya ba tana nufin yarda da duk abin da yaro yake so ba, illa shirya shi ya zama mai bin umarni da kuma sanin iyakokinsa.
Idan yaro ya ga haɗin kai tsakanin manya, sai ya ji daɗi ya samu aminci…
Idan kuma ana mutunta ƙa’idoji a cikin gida, sai ya taso da halin nagarta, cike da karfi zuciya wanda ya san haƙƙinsa da abin da ya rataya a kansa.