Naxeer Ibn Aliiyu Bajoga

Naxeer Ibn Aliiyu Bajoga Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Naxeer Ibn Aliiyu Bajoga, Grocers, Bajoga Funakaye LGA, Bajoga.

22/07/2024

Jiya agabana wani soja yamari budruwata Amma dayake shi so makahone ko Gani banyiba🙈👌🤩mz

19/07/2024

Nidae nasan tabbas malaman nan Inba Dan Allah sukeyi ba to suma tabbas yanxu da sun shiga yajin aiki

07/01/2024
Innal laha laayu gayyiru maa bi qaumin hatta yugayyiru mabi anfusikum.Allah baxai turo da Buhari kuma ya turo Tinubu ba ...
05/09/2023

Innal laha laayu gayyiru maa bi qaumin hatta yugayyiru mabi anfusikum.
Allah baxai turo da Buhari kuma ya turo Tinubu ba har sai kun roko da kanku. Idan baxaku canxa ba to gaba kuma Naxeeru ne.
Allah ya bamu ikon canxawa.

09/07/2023

DON ALLAH MU RINQA KOYAWA YARA IRIN WANNAN KACICI-KACICIN.

1. Ayoyi nawane Qur'ani mai tsarki yake dauke dasu?.

A. 6235
B. 6666.√
C. 6237
D. 6238

2. Sau nawa kalmar Qur'an yazo acikin Alqur’an Mai girma?

A. 67
B. 68
C. 69
D. 70.√

3. Wani abun sha ne da ake sonshi sosai kuma aka ambata a Qur'ani?

A. Zuma
B. Madara.√
C. Ruwa
D. Juice

4. Wani abinci ne da akafiso kuma aka ambace shi a Qur'ani?

A. Zuma.√
B. Madara
C. Kankana
D. Dabino

5. Wacce surah ce mafi gajarta acikin Qur'ani?

A. Falaq
B. NASS
C. IKLASS
D. KAUSAR.√

6. Wani abune Allah yafi rashin kaunarsa a Alqur’ani duk da cewa halal ne?

A. Aikin Hajji
B. Mutuwar aure ko saki.√
C. Aure
D. Kisan kai

7. Wani harafine akafi amfani dashi sosai dashi acikin Qur'ani?

A. Wa
B. Ba'un
C. Alif.√
D. Qaf

8. Wani harafine akafi karancin amfani dashi acikin Qur'ani?

A. Zaa.√
B. Maa
C. Taa
D. Laa

9. Wace dabbace datafi kowacce girma da aka ambata acikin Qur'ani?

A. Kifi
B. Katon kifin ruwa
C. Giwa.√
D. Macijiya

10. Wace dabbace kankanuwa da aka ambata a Qur'ani?

A. Quda
B. Sauro.√
C. Gizo-Gizo
D. Tururuwa
Ans = Saura Q.2:26

11. Wacce sura ce ke daukeda mafi qanqantan harufa a Qur'ani?

A. 41
B. Suratul kausar 42.√
C. 43
D. 44

12. Wacce surace ake kiranta da suna uwar Qur'ani?.

A. Baqara
B. Fatiha.√
C. Iklass
D. Yaseen

13. Surori nawane s**a fara da: Al-Hamdulillah?

A. Hudu
B. Biyar.√
C. Shida
D. Bakwai

[ Fatihah, Anaam, Kahf, Saba & Fatir ]

14. Surori nawane sunansu harafi dayane kawai?

A. Biyu
B. Uku.√
C. Hudu
D. Biyar
[ Qaf, Sad & Noon ]

15. Surori nawane s**a fara da kalmar ‘Inna ‘?

A. Uku
B. Hudu.√
C. Biyar
D. Shida.
[ Sura Fatha, Nuh,Qadr, Kausar ]

16. Surori nawane aka saukar a makkah?
A. 85
B. 86.√
C. 87
D. 88

17. Surori nawane aka saukar a Madinah

A. 28.√
B. 27
C. 26
D. 25.

18. Wacce surace mai sunan yaren Sayyidul waraa sallallahu alaihi wasallam?.

A. Lahab
B. Quraish.√
C. Hashim
D. Sab'i

19. Wacce surah ce ake Kira zuciyar Qur'ani?

A. Iklas
B. Yase

03/06/2023

TARIHIN KIRKIRO JIHOHI A NAJERIYA

Yankuna: Tun kafin shekarar 1914 lokacin da Turawan mulkin mallaka s**a shiga yankin da a yanzu ya zama Najeriya kasar na rarrabe ne cikin dauloli 4, wadanda wasunsu s**a keta har cikin kasashen Ghana da Kamaru.

1. Daular Arewa: Daular Arewa ta hada da Daular Kanem Borno da daular Hausa, wadanda s**a kunshi wasu daga cikin kasashen Hausa kamar Zazzau, Gobir, Kano, Katsina, Daura da kuma wasu garuruwan kabilu kamar Gwari, Kebbi, Nupe Yalwa da dai sauransu.

2. Daular Calabar: An kafa daular Calabar tun shekara ta 1000 AD wato bayan fakuwar Annabi Isa AS, don haka ta kasance daular da tafi kowace dadewa a tarihin Najeriya.

Tarihi ya nuna cewa wasu ‘yan biyu ne s**a kafa daular da a farko aka fi sani da daular Nri ta kabilar Ibo.

Daular ta fadada ikonta har zuwa cikin kasar Kamaru ta yanzu.

3. Daular Oduduwa ko ta Yoruba: Wannan daular ta kunshi asalin kabilar Yarabawa wadanda cibiyarsu ke Ile-Ife da Oyo dake yankin kudu maso yammaci, wanda tarihi ya nuna cewa Oduduwa ne ya fara kafata, yayin da ya tura 'yansa su kafa wasu garuruwan da s**a zama sarakunansu.

4. Daular Benin: Daular Benin ita ce daula mafi karfi a tarihin Najeriya wadda ita ma take yankin kudu maso yammacin kasar. Wannan daular ta yi karfi sosai a wancan lokacin, inda ta fadada har zuwa cikin kasar Ghana. Daular Benin ta yi suna wajen sassake sassake a nahiyar Afirka.

Mulkin Mallaka

A shekarar 1914, turawa sun hade yankunan arewa da kudanci da kuma Lagas, abinda ya samar da Najeriya da ake da ita a yanzu.

Daga nan sun kasa kasar gida hudu domin tafiyar da ayyukan gwamnati:

Yankin Lagas,
Lardunan Arewaci
Lardunan Gabashi
Lardunan Yammaci

Har ya zuwa wannan lokacin wasu yankunan Kamaru na cikin Najeriya.

Kundin tsarin mulkin shekarar 1951 ya mayar da lardunan zuwa matsayin yankuna, wato yankunan Legas, Arewa, Gabashi da Yammaci.

A shekarar 1967, Janar Yakubu Gowon wanda shi ne shugaban kasa a lokacin, ya kasa yankuna hudunda ake da su zuwa jihohi 12, biyo ba

27/05/2023

An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam a garin Daura, a shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacin
yakan ce 1964). Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, a wurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma shi ne musabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai s**a zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano. Tun kafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978. Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Haka ya rika yin wannan karatu guda biyu: Waccan makarantar ya je ta da daddare bayan sallar isha'i, waccan kuma ta koyo harshen larabcin da yamma. Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Kasa-Da-Kasa Ta Afrika da take Khartoum, Sudan.Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi nisa wajen karatunsa na digiri na uku,

28/03/2023

Malama Fólashade Mùjidat Ahmed Tinubù, babbar ɗiyar Bola Ahmed Tunibu Tana Karanta Qur'ani, Allah Yayi Mata Albarka🙏

28/03/2023

AZUMI DA HUKUNCE HUKUNCEN SA

*MENE NE AZUMI...??*

*1. AZUMI A LUGGA*
Shine kamewa
*2. ASHARI'ANCE:-* Shine kamewa daga barin chi ko sha da saduwa da iyali tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin ibada.

*RUKUNAN AZUMI*

1. Yin niyya
2. Kamewa daga ci ko sha da saduwa da iyali
3. Zamani (lokachin yin azumi).

*SUNNONIN AZUMI*
1. Gaggauta buda baki
2. Jinkirta sahur
3. Addu'a yayin buda baki
4. Yin sahur da jinkirta shi.

*MAKARUHAN AZUMI*
1. Kaiwa matuka wajen kurkuran baki
2. Sumba
3. Dauwamar da kallo na sha' awa
4. Tunani akan al'amuran saduwa
5. Shafa ko runguma
6. Dandanan wani abu
7. Yin kaho.

*ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI*
1. Saduwan wani abu zuwa makoshi (narkakke)
2. Fitarda maniyyi ko maziyyi da gangar
3. Saduwa ta hanyar tilasta
4. Ci ko sha da tunanin sauran dare
5. Chi ko sha da gangan
6. Saduwan wani abu wanda ba narkakkeba zuwa makoshi
7. Ridda.

*ABUBUWAN DA SUKE HALAS.*
1. Yin asiwaki
2. Sanyaya jiki da ruwa
3. Tafiya ta halas
4. Sanya magani wanda ya dache
5. Tauna wani abu ga karamin yaro
6. Sanya turare.

*ABUBUWAN DA AKAYI RANGWAME*
1. Hadiye yawu
2. Rinjayen amai da magwas
3. Rinjayen wani kwaro zuwa ga makoshi
4. Kuran kan hanya
5. Wayan gari da janaba
6. Yin mafarki da rana

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
Naxeer Ibn Aliiyu Bajoga.

26/03/2023

*_FALALAR AZUMI DA AMFANINSA GUDA 37_*

Falala da amfanin Azumi anan duniya da gobe lahira da kuma falalar watan Ramadhana.

Daga cikin falalar watan Ramadhana da falalar yin azumi acikinsa:-

*1-Azumi garkuwane da yake kare bawa daga shiga wuta,kuma yana kare bawa daga aukawa sabon Allah,kuma yana magance sha’awa da kuma kare mutum daga fadawa zina da kallon haramun*


*2-Azumin yini guda daya dan Allah,yana kare bawa daga shiga wuta tsawon tafiyar shekara sama da 70*


*3-Babu abinda bawa yake samun kariyar shiga wuta kuma ya shigar da shi aljanna kamar Azumi*


*4-Allah yana baiwa masu azumi ladarsu ba tare da iyakancewa ba*


*5-Mai azumi yana samun murna da farin ciki guda biyu,lokacin bude bakinsa da kuma ranar alqiyma lokacin da yaga tarin ladarsa da sakamakon Azuminsa*


*6-Warin bakin mai Azumi a ranar alqiyama yafi kamshin turaren miski awajan Allah*


*7-Azumi da alqurani suna ceton bawa awajan Allah agobe alqiyama,shiyasa aka shar’anta mana yawaita karatun alqurani da darussansa alokacin azumi*


*8-Azumi yana kankare zunubai kuma kaffarane wasu daga cikin laifukan da baya ya aikata masu girma*
’ida da Nisa’i da Baqara

*9-Azumi yana kare mutum daga fitina acikin ransa da dukiyarsa da iyalinsa*
da Muslim

*10-Allah ya tadani wata kofa acikin gidan Aljanna ga masu azumi kadai*
da Muslim

*11-Allah yana shayar da masu Azumi wani ruwa idan sun shiga kofar azumi a aljanna daga nan basa kara jin kishin ruwa har abada*


*12-Awatan Ramadhana ne Allah ya saukar da alqurani mai girma shiyasa aka shar’anta mana yin azumi acikinsa dan dacewa da godiya ga Allah cikin saukar da alqurani*
Baqara

*13-Daure Shaidhanu da masu tsarin kai daga cikin aljannu*
da Muslim

*14-An bude kofofin Aljanna baki daya a farkon daren watan Ramadhana da rufe kofofin wuta baki daya,kuma baza’a bude kodayaba har zuwa karshen azumi*


*15-Allah yana yanta bayinsa daga wuta zuwa Aljanna

04/03/2023

Shawarwarin Da Falalu a dorayi Ya Ba Matasa Akan Amfani da Kafafen sada zumunta

Babu abu mafi saurin rudar da mutum ya sauya masa tunani lokaci gudu irin rayuwar social media. Domin mafi yawan kaso na abin da ake rubutuwa ko yadawa ba gaskiya ba ne.

‘Dan uwa yi hankali da abin da kake gani, kuma kayi duban tsanaki, kabi abin da zaka karu. Domin da dama sun bi a makance an rufta su, ba su kare a matattara mai kyau ba.

Wajibi ka sakawa kanka linzami, in kana bibiyar masu rubuce-rubuce a social media. Da ka ga anyi in da hankalinka bai kwantaba kawai anzo tashar da zaka sauka.
Idan kuwa ka biyewa musu to ba za ayi nisa ba, zaka gane ka afka cikin haɗari.

Social media wata matattara ce da ke dauke hankalin mafi yawan mutane daga gaskiya zuwa karya. Lokacin guda take sauya fasalin marasa lissafin cikinmu su fara sabuwar dabi’a su manta asalin su waye su.
Ga misalai nan BARKATAI

Mu maida hankali ga ingantattu shafuka masu yada
-Ilimin Addini
-Ilimin zamani
-Sahihan Labarai duniya daga sanannu gidajen jarida
-Harkar Lafiya
-Saye da sayarwa da Kasuwanci

A cikin wadannan 👆Ina da yaqinin zamu sami riba, maimakon biye masu yada Karya, gaba, kiyayya, shedanci, shashanci da farraka kawunan Al’umma.

Allah ya bamu ikon yada alkairi. Amin.
Barkanmu da Juma’a

Address

Bajoga Funakaye LGA
Bajoga

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Naxeer Ibn Aliiyu Bajoga posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category