02/02/2026
Jiya Lahadi 1/2/2026 Alh Murtala Ibrahim Danmalikin Boto, Ya Jagoranci Taron Wasu Rukuni Daga Cikin Magoya Bayan Mai Girma Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi M.A Abubakar SAN.
Rukunonin Da S**a Tarun Sun Hada Da Tsofaffin Kwamishinonin Da S**ayi Aiki Karkashin Gwamnatin Mai Girma M.A Abubakar SAN. Sai Tsofaffin Shugabannin Kananan Hukumomi Da S**a Jagoranci Kananan Hukumomin Su Lokacin Gwamnatim M.A Abubakar SAN. Sai Tsofaffin Masu Bada Shawari/ Da Masu Tallafa Na Musamman, A Lokacin Gwamnatin M.A Abubakar SAN. Sai Tsofaffin EXCO Da Sabbi A Bangaren Jam,iya.
Yayin Taron Danmalikin Boto Ya Tabbatar Wa Mahalarta Taron Cewa Mai Girma Tsohon Gwamna M.A Abubakar SAN Ya Gama Dukkannin Shirye Shirye Kuma Dayyi Takara Da Izinin ALLAH Kuma Dayyi Nasara.
Bayan Jawabin Shugaban Taron, Ansamu Wakilci Daga Dukkan Rukunoni Dasuka Taru Wanda S**ayi Jawabin Jindadin Wannan Sako Na Takaran M.A Tare Da Nuna Goyon Bayansu Dari Bisa Dari (100%} Amadadin Rukunin Dasuke Wakilta.
Taron Ya Sanya Farin Ciki Da Jindadi Wa Magoya Bayan Na M.A Inda Kowa Ke Cewa Daman Wannan Sakon Suke Jira Don Daukan Mikati Tare Da Isar Da Wannan Babban Sakon Wa Alumman Su.
Daga Karshe An Rufe Taro Da Addu,an ALLAH Ya Dawo Mana Da Gwamnatin Mai Girma Tsohon Gwamna Muhammed Abdullahi Abubakar SAN. AMEEN