Aliyu Adamu Muhammad-HRF/Activist

Aliyu Adamu Muhammad-HRF/Activist Activism is my passion

12/06/2023

Bazance komai game da maganar Kashim Shettima ba har sai na samu complete video clip na program din da yayi,domin babu adalci ace kayi hukunci akan magana na second 13 alhali anyi magana mai tsayi ne...

14/05/2023

Tarbiyya ya gama ta6ar6arewa a cikin al'umma,sai kaga yaro a social media kayi jika dashi ko ka haifeshi amma yana maka rashin kunya,wanda wallahi a shekarun baya abin ba haka yake ba sam,ko me ya jawo haka yanzu?

04/05/2023

IPOH(MAGUZAWA)
Akwai aiki babba a gaban al'umma wajen kawarda wannan Munafukai masu neman haddasa rigima tsakanin Hausawa da Fulani...Ziyarci shafin Aliyu U. Tilde don samun cikakken bayani...

The segregation of boys and girls in senior secondary schools and some Junior secondary schools across Bauchi State is 1...
22/03/2023

The segregation of boys and girls in senior secondary schools and some Junior secondary schools across Bauchi State is 1 of 1000s legacies that Dr. Aliyu U. Tilde(PhD.) left in the history of Educational Sector,he left but his achievements will always be remembered and the good people of Bauchi State will always pray for your success in your life endeavor.

CIGABA A MA’AIKATAR ILIMI (1)KARKASHINGOMNA BALA MOHAMMED, KAURAN BAUCHI Ya zama wajibi gare ni in rubuta abubuwan cigab...
09/03/2023

CIGABA A MA’AIKATAR ILIMI (1)
KARKASHIN
GOMNA BALA MOHAMMED, KAURAN BAUCHI

Ya zama wajibi gare ni in rubuta abubuwan cigaba da muka kawo lokacin da nake Komishinan Ilimi a karkashin Maigirma, Gomnan Jahar Bauchi, Senata Bala Abdulkadir Mohammed, Kauran Bauchi, saboda kore wasu shubhohin da abokan hamayya da wadanda matakan gyaran da muka dauka bai musu dadi ba. Da ma haka gyara yake—mabarnaci dole ya koka, ya kushe, musamman idan gyaran ya taba hanyar haramiyarsa. Amma idan rana ta fito, tafin hanu ba ya kareta.

A wannan shafin, na jero abubuwa 10 na farko cikin sama da abubuwa 100 da na yi a Ma’aikatar Ilimi da sahhalewar Gomna. Zan kawo sauran a kashi na biyu da na uku. Saura ya rage ga mai karatu ya fahimci ko cigaba aka kawo ko lalata ilimi aka yi k**ar yanda malalatan malamai, da rubabbun jami’ai da masu neman mulki ido rufe, da wadanda ba su samu biyan bukatarsu a wajen Gomna ba, suke cewa.

Shi kuwa Gomna sai ya yi hakuri; ya kawo ni ne don in yi gyara kuma na yi iya kokarina. Allah ya ba shi ladan sahhalewa da goyon bayan da ya rika bani a lokacin. Zancen na masa zagon kasa da na yi wadannan ayyuka da zan shata a kasa makircin baragurbin yan’siyasa ne wadanda tun ran farko ba su so a yi gyara ba, ko na miskala zarratin, k**ar yanda halinsu yake ko yaushe, sai dai a dau hakkin talakawa a ba su su ci. Na san na musu laifi, amma don Allah kar su yafe mun.

Kuma duk wadanda s**a ga laifin Kaura a wadannan matakan gyaran, to su binciki zukatansu. Munkirai ne la-muhala. Allah ya raba mu da sharrinsu.

Ga cigaban nan a jere. A yi karatu lafiya.
_____________

1. RAGE KUDIN MAKARANTA: Mun iske makarantun gomnati da yawa sun zama k**ar na kudi inda ake tatsar iyaye kullum, ana biyan N2,700 – N5,000 duk shekara wa dalibi guda banda sauran abubuwan kawowa na yau da kullum k**ar Izal, tsintsiya, fartanya, A4 papers, da sauransu. Idan dalibi bai kawo ba a hana shi shiga aji. Sai muka rage kudin makaranta (PTA) zuwa N700 kacal wanda za a biya a tsawon shekara.

Azzaluman da abin ya shafa sun koka cewa ba zai ishe su ba amma lissafi ya nuna hakan ya isa tunda daliban da yawa, kuma makarantun ba sa biyan albashi ko gyara makaranta da kudin. Yanboko masu hali suna ganin wannan ba komi ba ne saboda suna da kudin ta hanyar halal ko haram. Amma talakawa 500 ma tashin hankali ne a gunsu. Idan mutuum yana da yara 5 a makaranta, samun ya zakulo wajen N20,000 a lokacin da ko abinci ba yi da shi a gida babban abu ne.

Kuma zancen wai kudin ba su isa ba duk bogi ne. Misali, makaranta mafi yawan dalibai a jahar, mai dalibai 5,077, mun saya mata isassun kayan lura da makaranta da ta nema amma duk a N445,000 kacal. Ka tuna makarantar za ta tara kudin PTA akalla N3,553,900. Wannan ya ishi makarantar sayen alli, da A4 paper, da fartanya da tsintisya da sauransu. Amma da iyaye sun tara musu izal 5,077, tsintsiya 5,077, da me za su yi da su banda su kai kasuwa su sayar? Wannan lalata ilimi ne a Jahar Bauchi a gun wadanda aka toshe wa hanyar tatsar talakawa.

2. TILASTA WA MALAMAI ZUWA MAKARANTA DA SHIGA AJI: Daga cikin abinda muka iske shi ne rashin zuwan malamai da yawa makaranta. Kididdigar da muka samu daga timebook na makarantu da muka tattaro tun farko ya nuna kashI 45% kacal na malaman sakandare ke zuwa koyarwa a-kai-a-kai. Wasu malaman ma sun yi shekaru ba a gan su ba. Wannan shi ya sa muka kawo na’urar dangwala yatsa (fingerprint terminal) wacce ke rattaba zuwan malami makaranta da yawan darussan da ya koyar kullum. A yayin da iyaye suke murna don sun ga chanji a halartar malamai makaranta, wasu jihohi suna kwaikwaya, jama’a na yabawa, su kuwa malalatan malamai da ba su son koyarwa suna nan suna ta zagi a Facebook suna cewa an bata ilimi a Jahar Bauchi. Sun aza abin zai tsaya in na tafi; amma, kash, na’urar dangwale ta ci gaba da aiki. Sai a yi hakuri. Wannan yana daga cikin dalilan da wasu suke hantarar Gomna Kaura da yin barazanar ba za su sake zabarsa ba. Amma amanar yara aka ba mu. Ba za mu bar katti su yi ta karbar albashi suna cutar da su wajen rashin koyarwa ba. Sun aza in wani Gomnan ya zo, zai bari su yi sharholiya.

3. CIYAR DA YARA A MAKARANTU: Gomnatin Jahar Bauchi da tana ba da N81.2million don ciyar da dalibai a makarantun sakandare na kwana a Jahar. Abin mamaki shi ne duk da wannan kudin yara suna kwana da yunwa don bai wuce kashi 1/3 na abincin yake shiga bakinsu ba, wannan ma sai daliban da s**a ci sa’a. Sauran kudin ana sama da fadi ne da su tsakanin yankwangila, yansiyasa, shugabannin makarantu da jami’ai masu lura da suto da masu dafa abincin. Wannan matsala ce ta shekaru da yawa kuma ana samunta a duk jihohi. Karshe, yara dole su rika zuwa makaranta da abinci suna dafawa, ko su rika yawo a gari suna wanke wanke da sauran ayyuka a gidaje da otel da manyan makarantu. Yanmata a makarantun kwana kuwa da yawansu a lalata su. Tabbas.

Ganin haka ya sa muka kawo tsarin masu bibiyar abinci daga karbarsa a makaranta har ya shiga bakin yara. Nan take abubuwa s**a canza. Yara s**a rika samun hakkinsu, s**a daina watangaririya a gonaki da garuruwa. Har na bar kujerata, wannan tsarin na tafiya daidai. Da fatar wacce ta karbe ni za ta tsaya a kai. Amma fa, ran shugabannin makarantu da yawa ya baci. Hakaza jama’ar gari, manya, da makarantun ke garinsu, wadanda ake raba abincin yaran da su, sai kuka suke yi. Kar ka ambaci yansiyasa da yankwangila. Dole maciya amana su koka. Su ce an lalata ilimi.

4. YAKI DA CIN HANCI DA RASHAWA: Wannan babban al’amari ne da ke lalata tsarin ilimi inda iyaye da dalibai da malamai ke biyan kudi kafin su samu hakkinsu; ko ake sama da fadi a kan kudaden da ya k**ata a ce an yi amfani da su a ayyukan gudanar da ilimi. Wannan ya hada da fannin jarrabawa, da na daukan dalibai a makarantu, da na ciyarwa a makarantun kwana, da ciyar da ma’aikata gaba (promotion), da sarrafa kudaden bashin Bakin Duniya na SEPIP da BESDA, da aringizon kwangila da wajen biyan yankwangila hakkinsu, da sauransu.

A dukkan wadannan al’amurra, mun shata layi inda muka hana cin hanci da karbar rashawa a cikinsu ta hanyar kawo fasahar zamani, da sa ido, da ladabtar da wadanda aka k**a da laifi, da canza musu wurin aiki, da sauransu. Babu wani uba ko dalibi da zai ce sai da ya ba da sisi kafin aka ba shi hakkinsa; ko malami ya ce sai da ya ba da kudi kafin ya samu cigaba; ko dankwangila ya ce sai da ya ba da kudi kafin aka biya shi; ko shugabannin makarantu s**e an rike musu kudin cefanen abincin yara. Kowa alat kawai zai ji. Wannan ya rage wa mutane dawainiya sosai. Amma fa ya bata ran wadanda da suke sharholiya; suna nan ba za su daina kokawa ba da yin sharri.

5. TSARIN TIRASIFA KAWAI. Cikin abubuwan da muka dakile shi ne amfani da kudi nakadan a al’amurran gudanar da Ma’aikatar Ilimi. Duk abinda za a yi dole a yi shi ta hanyar tiransifa cikin asusun mutane, da makarantu da Ma’aikata. Wannan ya sa mun tilasta wa kowace makaranta bude asusun banki, akasari ba su da shi a lokacin da na zo in ba na SBMC ba da s**a yi don karbar kudin SEPIP. Na fi shekara uku ban ga gundarin kudi ba a Ma’aikatar Ilimi albarkacin wannan tsarin. Wannan ya sa a take makarantu ke samun kudadensu ba k**ar da da za a kawo kudin a buhu daga banki, su zo su yi layi ana diba musu ba, ana cire na kungiya da kason shugabanni da na sa’idawa. Duk kudaden Ministiri sai shiga cikin asusu suke kai-tsaye, walau na jarrabawa ne, ko na rijistar makaranta, da sauransu. Idan s**a fita kuwa, ana iya ganin ina s**a je, wa aka biya da dalilin biyansu. Komishina zai samu alat, haka Babban Sakataren ma’aikatar da akanta. Wannan tsabatace al’amari ya jawo bakin ciki ga mahandama da yawa. Dole su ke ce mun ba na son mutane su amfana. Amfani a gunsu a bari su cuci jama’a.

6. TSARIN INDEX NUMBER: Wannan tsari ne da muka fito da shi don tantance daliban sakandare da sanin adadinsu da inda suke a Jahar Bauchi. A fayil guda na manhajar EXCEL, an samar da kundin wadannan bayanai masu muhimmanci wajen tsara lamurra. Ya zama dole a yi haka don a hana aringizon dalibai da kawo dalibai na waje cikin jarrabowin WAEC; NECO da BECE da kuma wajen diban dalibai (admission) a makarantu ko samar da abin more rayuwa a makarantu.

Wannan tsarin ya hana shugabannin makarantu da malamai diban dalibai barkate ba tare da izini ba har abin ya gagari Gomnati. Misali, an daina aringizon dalibai a makarantun kwana wanda yin haka ya janyo wa gomnatin da ta shude bashin N450million na kamfanin CFA bayan gomnatin ta biya gama biyan N81.2million da ke kanta a kowane wata. Gomnatin Kaura ta gaji wannan bashin wanda muka biya rabi a lokacin da na bar kujerar.

7. SAYEN KAYAN AIKI WA MAKARANTU: An jima ba a saya wa makarantu kayan aiki ba, irin su alli, da takardun rubutu, da rijista, da kayakin lura da makarantun, da sauransu. A lokacin da nake Komishinan Ilimi, na mai da hankali kan saya wa makarantun sakandare da suke karkashin ma’aikatar ilimi kayan aiki iya gwargwado daga kudaden da na samu na $1million ta karshe ta tsarin SEPIP da kuma rarar N161million da muka samu a 2021. Sau uku muna cika babban suto na Makarantar Army Barracks da irin wadannan kayan muna raba wa makarantu su. Akwai dubban kujerun makaranta, da na cin abincin yara, da katifu, da gidan soro, da barguna, da injunan markade, da wilbaro, da duk abinda ake bukata na lura da makaranta a ciki. Duk an raba wa makarantu masu bukata kuma da saura a ciki a lokacin da na bari.

8. CIYAR DA MA’AIKATA GABA (Promotion): A karon farko an ciyar da ma’aikata da malaman da suke karkashin Ma’aiakatar Ilimi fiye da 3,900 gaba a 2022 ba tare da nuku-nuku ko uwa a bakin murhu ba. Wasu sun yi shekara 10 ba labari. Hakaza, mun samu sahhalewar Gomna na cigaba da biyan su karin albashin da zai biyo bayan cigaban nasu. A lokacin da na bar kujerar, ana cikin shirin cika takardun da ake bukata daga baitalmali na aiwatar da karin kudin.

An kuma kawo tsari na bai daya, na ba sani ba sabo, wanda a cikinsa, sai an tabbatar da hazakar ma’aikaci wajen aikinsa k**ar yadda rahoton mabibiya (inspection template) ya nuna kafin a ci da ma’aikaci gaba. Wannan ya zama dole don a cire son zuciya, da sanayya, da cin hanci, da sauran munanan dabi’u wajen cigaban ma’aikata da malamai.

Sannan kuma na shiga tsakani har aka samu sahhalewar Gomna na a biya malaman manyan makarantu karin albashi da suke nema saboda cigaban da aka musu na shekaru. A lokacin da na bar kujera, ana kan matakan aiwatarwa tsakanin makarantun da Baitalmali.

9. BA BASHI: Na gudanar da Ma’aikatar Ilimi bisa tsarin kudi lakadan—ba daukan bashi. Har na bar wajen, ba mutum daya ko wata hukuma da take bin Gomnatin Kaura sisin kwabo a lamurran da s**a shafi Ma’aikatar ilimi da makarantunta. In ka ga bashi, to wanda ya yi kwantai ne muka gada daga gomnatocin baya. Shugabannin makarantu sun daina bin bashin kudin cefane, suna samun tiransifa kafin dalibai su dawo ko kafin wata ya kare; duk dankwangilan da muka ba shi aiki, to akwai kudinsa a kasa, yana karewa ana biyansa. Duk hukumomin jarrabawa na NABTEB, NBAIS, NECO, WAEC ko JAMB ba wacce ke bin Jahar Bauchi ko sisi na jarrabawa a lokacin da na sauka daga kujera, duk da mun gaji bashin sama da N605million. Alhamdulillah. Wasu jihohin ana bin su kudin na shekaru.

10. LURA DA MAKARANTUN KWANA: Mun bai wa makarantun kwana kulawa ta musamman. Banda tabbatar da cewa dalibai na samun abincinsu sau uku a wuni k**ar yadda aka tsara, Ma’aikatar Ilimi ta yi kokarin samar da abubuwan more rayuwa da karatu a cikinsu, duk da cewa manyan kongilolin da muka nemi a yi su na gyaran wasu gine-gine ba a samu daman yinsu ba. Mun tabbatar a makarantun akwai wutan lantarki, ruwan sha da na aiki, gadaje, katifu, barguna, gidajen sauro, kwanukan cin abinci, teburan cin abinci, kujerun karatu, kayan wasanni, da sauransu. Wannan ya zama wajibi ne saboda idan ba da su ba, karatun yaran a cikin makarantun zai yi wuya.

Hakan nan, mun hana keta (bullying) a makarantun wanda gami da rashin kayan more rayuwa da na karatu ya sa iyaye da yawa ba sa son kai y’ay’ansu makarantun kwana. Alhamdulillahi mun sauke wannan nauyin a lokacina.

_____________
Zan tsaya a nan. A kashi 2 za mu ci gaba da lissafo cigaban da aka samu. Da fatar maikaratu zai dakace ni. Na gode.

Dr. Aliyu U. Tilde
9 Maris 2023

Halinda wannan canjin kudi ya haifar a kasuwanninmu na fadin kasar nan😭😭😭😭😭
16/02/2023

Halinda wannan canjin kudi ya haifar a kasuwanninmu na fadin kasar nan😭😭😭😭😭

All these sort of nonsense must stop...✓Physical violence✓Sexual violence✓Psychological violence✓Economic violence
10/02/2023

All these sort of nonsense must stop...
✓Physical violence
✓Sexual violence
✓Psychological violence
✓Economic violence

10/02/2023

Value Respect more than LOVE!
RESPECT is LOVE!!

Kasa ta rikice,dolene a matsayina na Dan Gwagwarmaya mai fafatukar kare hakkin al'umma(HRF/Activist) mu nemowa jama'a ma...
06/02/2023

Kasa ta rikice,dolene a matsayina na Dan Gwagwarmaya mai fafatukar kare hakkin al'umma(HRF/Activist) mu nemowa jama'a mafita cikin gaggawa😎

Address

Gombe Road
Bauchi
740102

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aliyu Adamu Muhammad-HRF/Activist posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Aliyu Adamu Muhammad-HRF/Activist:

Share

Category