Mukaru da Juna

Mukaru da Juna Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mukaru da Juna, Grocers, Bakin kasuwa Faggo, Bauchi.

04/05/2026

Fulani bandit on work

29/04/2026

ALLAH yasa muyi kyakkyawan karshe

Wasu suna kwance acikin “ƙabari”! sama da shekaru dubu‚ suna burin ina ma za su samu damar ko da yin raka'a ɗayace amma ...
09/04/2026

Wasu suna kwance acikin “ƙabari”! sama da shekaru dubu‚ suna burin ina ma za su samu damar ko da yin raka'a ɗayace amma hakan ba zai samu ba saboda alƙawarin Allah cewa:

ومن وراء هم برزخ إلى يوم يبعثون

Yanzu kake da dama‚ domin kai ga shi lafiyarka ƙalau, kana da isasshen lokaci‚ kana zuwa inda kake so‚ kaci kasha abinda kake so‚ amma sallar farillarma saika ga dama kake yi akan lokaci ko kuma cikin jam’i‚ Ya khasãra!‚ kasani wannan damar idan ta wuce ka har abada bazata dawo ba‚ wasu suna burin su sameta amma rashin lafiya ko kwanciyar ƙabari ya hana‚ kaima dole ɗaya daga ciki zai sameka.

Imam Muhammad bin sirina ((Rahimahullah)) yana cewa: “Da ace za'a bani zaɓi na yi raka'a biyu ko na shiga aljanna”!? Yace:’’ da ya zaɓi raka'a biyu akan aljanna”! Babbar nadamar da zakayi a rayuwarka shine ka koma ga Allah kana ɓata lokacinka ba tare da yin salla acikin jam'i ba ko kuma kan lokaci ba‚ domin matuƙar sallarka ta yi kyau dukkan ayyukanka sunyi kyau haka idan ta ɓaci k**ar yadda hadithi ingantacce ya tabbata daga Annabi ((SalLalLaHu Alaihi wasalLam))‚ matuƙar kana tsayarda salla akan lokaci dukkan wasu buƙatu da damuwarka Allah zai yaye.

Sheikh Shafee'u Yusuf

ALLAH SARKÌ: "Babban Burina Kowane Musulmì A Kowace Akida Yake Ya Shiģa Aljañna, Ba Ni Da Damuwa Don Musuĺmì Ya Shiga Al...
27/11/2025

ALLAH SARKÌ: "Babban Burina Kowane Musulmì A Kowace Akida Yake Ya Shiģa Aljañna, Ba Ni Da Damuwa Don Musuĺmì Ya Shiga Aljañna Saidaì Farin Ciki Mara Misaltuwa, Kuma Zan Yi Bakìn Cikì Idan Musuĺmì Ya Shiģà Wutà", Cewar Marigayi Sheik Dahiru Bauchi

Allah Ya jikan Sheik Dahiru Bauchi.

SHÊIKH DAHIRU BAUCHI: Malamin Da Ya Fi Kowa Yawan Zuri’ar Mahaddata Alkur’ani A DuniyaFitaccen malamin addinin Musulunci...
27/11/2025

SHÊIKH DAHIRU BAUCHI: Malamin Da Ya Fi Kowa Yawan Zuri’ar Mahaddata Alkur’ani A Duniya

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kafa tarihin zama mutumin da ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a tarihin duniya.

Alkaluma sun nuna cewa Shehin Malamin, wanda yana da ’ya’ya da jikoki da ma tattaba-kunne kusan 300 da s**a haddace Alkur’ani.

A cewar kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, wadanda s**a karrama malamin da lambar yabo, Sheikh Dahiru Bauchi shi ne mutum na farko da ya taba samun irin wannan baiwar.

Bayanai sun nuna mashahurin malamain yana da ’ya’ya 95 da jikoki 406 da tattaba-kunne 100. Daga cikin wannan adadin, ’ya’yansa 77 da jikoki 199 da kuma tattaba-kunne 12 ne s**a haddace Alkur’anin

Yana daga cikin Halifofin Sheikh Inyass

Sheikh Darihu Bauchi ne daga cikin halifofin Shehu Ibrahim Inyass, Halifan Darikar Tijjaniyya, bayan wanda ya assasa ta, wato Sheikh Ahmadu Tijjani.

Yana daga cikin manyan malaman Musulunci a Najeriya, shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli da ke bayar da Fatawar Musulunci a Najeriya sannan babban jigo ne a Darikar Tijjaniya a Najeriya da ma Afirka.

A zantawarsa da ’yan jarida shekarun baya a Bauchi, Sheikh Dahiru ya ba da takaitaccen tarihinsa, inda ya ce, “Tarihina dai ni Bafulatani ne, dukanin kakannina hudu Fulani ne, domin kowane mutum yana da kakanni hudu — ta wajen mahaifinsa biyu, ta wajen mahaifiyarsa biyu.

To ni dukanin kakannina Fulani ne babu inda muka hadu da wata kabila ta kowace fuska. Mu Fulanin Bauchi ne a lokacin da Jihar Bauchi take hade da Jihar Gombe.

“Bayan da aka raba Jihar Bauchi da Jihar Gombe, sai muka zama mu Fulanin Jihar Bauchi ne, a lokaci guda kuma Fulanin Jihar Gombe ne.

Ta wajen mahaifina ni Bafulatanin Jihar Bauchi ne, ta wajen mahaifiyata ni Bafulatanin Nafada ne da ke Jihar Gombe.

“An haife ni ne a watan Janairu".

Allah ya gafarta wa Malam.

Hausawa basu taba yabo nasu ko goya masa baya ko kare shi in har  ya zama ɓata gari,bara-gurbi.wai kun taba jin wanda ak...
17/11/2025

Hausawa basu taba yabo nasu ko goya masa baya ko kare shi in har ya zama ɓata gari,bara-gurbi.

wai kun taba jin wanda aka da laifin informer dumu-dumu Hausawan s**a bar shi a raye? Ai inaaa...su da kansu zasu karshi kuma su yi murnq da shagalin cire mugun iri daga xuriyar su.

Kai shi yasa fa, ake masu kirari da "Bahaushe mai ban Haushi,"

A tarihin Hausawa dubun-dubatar shekaru basu taba yiwa wata kabila abokiyar zamansu cin amana da butulci ba, sai dai su ayi masu.

Hausawa sun fi kowacce kabila ɗaukar ƙaddara da haƙuri da kuma son zaman lafiya,

saboda son zaman lafiyar Hqusawa kana iya zaga gida dubu baka samu wukar yanka mai kyau ba, tsabar kyautatawa kowa zato, son zaman lafiya,Bahaushe yasa bai tanadi makami ba, bare ya zauna yana tunanin ɗaukar fansa.

Hausawa ne ƙabilar dake tarbar baki, su yi masu riga da wando, babu nuna wariya, har su watsar dana su munanan al'adu su dauki na Hausa.

A tarihin kabilar hausa, ba a taba samun wani fitaccen ɗan ta'adda daga kabilar ba .

Wannan ya nuna tsantsar tarbiyya da tsaftar tunanin hausawan tun magabatan farko na kabilar

Hausawa su ne kaɗai ƙabilar da s**a ɗauki alakar Musulunci fiye da ta kabila.

Bahaushe ya yarda duk wanda Allah ya ba shugabanci ya jagorance shi, komai asalinsa. yayarda kowa ya shugabance shi ko daga wace kabila yake.

Kai shifa Bahaushe sam-sam ba mayan mulki da son shugabanci bane.ba mai taƙama da iko bane.

Kai Shifa bahaushe Abin da yake nema kawai ya ci, ya sha, ya rayu cikin salama da kwanciyar hankali.

Saboda tsabar son zaman lafiyar bahaushe ne yace "zama lafiya ya fi zama dan sarki". Yau dai babu sarautu babu zaman lafiyar.

Don allah ku bar hausawa su rayu, kun shafe tarihinsu me kyau kun jingina kare-rayi, an bautar da tunanin su ansa sun yi shiru.
kunce shafe zamantowar su kabila, sun yi shiru
Yau kuma su ake so a shafe.

Ibrahim Gamji✍️

Harshen Hausa shi ne na bakwai (7) a duniya a yawan masu amfani da shi, saɓanin ayyana shi a matsayin na goma sha tara (...
16/11/2025

Harshen Hausa shi ne na bakwai (7) a duniya a yawan masu amfani da shi, saɓanin ayyana shi a matsayin na goma sha tara (19) da wani shafin ƙididdiga mai suna "intelpoint.com" ya yi, wanda ya kwarara a shafukan yanar gizo.

Sun ruwaito cewa yawan masu magana da harshen Hausa miliyan 94 ne kaɗai kuma sam ba haka bane.

Akwai wani masani da ya bayyana cewa a yanzu, masu magana da harshen Hausa ba maganar miliyan ɗari biyu (200) ake yi ba, sai dai riɓin wannan adadin.

A wata hira/tattaunawa da gidan jaridar BBC Hausa s**a yi da Farfesa Bunza na Jami'ar Sakkwato (Sokoto), wanda yana daga cikin masana da s**a yi fice wajen nazarin harshen Hausa.

Masanin ya bayyana cewa, harshen ya zarce yadda ake masa kallo domin ya tumbatsa fiye da tunani.

Farfesan ya bayyanawa gidan jaridar BBC cewa, "A ƙididdigar da aka yi a baya a duniya, cikin harsuna 7,500, Hausa ita ce ta 11 a yawa."
Ya ce, sai dai ba za su ƙaryata wannan rahoto ba kai tsaye.
Daga nan, Farfesan ya ƙara da cewa, "Mu a bincikenmu ya nuna mana, harshen Hausa shi ne na 7 a duniya."

Hausa ta zama ɗaya daga cikin manyan harsunan duniya da ake amfani da su a mu'amullar yau da kullum, da kuma yaɗa saƙonni a kafafen yaɗa labarai, da kuma shafukan sada zumunta.

Masana sun tabbatar da cewa harshen na ƙara bunƙasa, k**a daga yadda mutane da dama a sassa daban-daban ke amfani da shi wajen magana da juna, har ma ta fannin rubutu da wallafe-wallafe na littattafai, jaridu, waƙoƙi.

Masanin ya yi bayanin cewa, daga binciken da malaman harshen Hausa magabata s**a yi, babu wata ƙasa a yankin Afirka ta Yamma da Hausawa ba su da yawa, "ko a ce ƙabilun asalin ƙasar da kaɗan s**a rinjayi Hausawa."
ya ce "Don haka a Afirka, Hausawa sun fi kowace kabila yawa, sannan harshen Hausa ya fi kowane harshe a Afirka,"

Ya ƙara da cewa, a tsakanin sauran ƙasashen Afirka, babu ƙasar da Hausawa ba su ziyarce ta ba ko kuma suna ziyartar ta har yanzu.

TUSHEN MATSALAR HAUSAWA DA FILLANI A YAU Bahaushen Nijeriya ya ginu, ya tarbiyyantu, ya kuma taso akan fahimtar cewa duk...
16/11/2025

TUSHEN MATSALAR HAUSAWA DA FILLANI A YAU

Bahaushen Nijeriya ya ginu, ya tarbiyyantu, ya kuma taso akan fahimtar cewa duk ƙasar nan baya da makusancin da ya wuce Bafillace.

Duk inda aka taɓa Bafillace a duniya sai Bahaushe ya ji zafi. Duk inda Bahaushe ya haɗu da Bafillace a duniya ji yake yaga ɗan uwa. Hakan tasa duk al'amarin da aka sanya Bafillace a ciki, Bahaushe na jin ya samu gamsasshen wakilci saboda baya taɓa tunanin za'a cuce shi.

A ƙasar nan kaf, ko ince a duniya, Bafillace baya da inda ya wuce masa ƙasar Hausa. Anan zaiyi kiwon sa ba tsangwama. Anan zai sakata ya wala. Saboda mafi akasarin Sarakuna da Malamai masu faɗa a ji a ƙasar Hausa Fillani ne ƴan uwansa. Akasarin jagororin ƙasar na gwamnati da siyasa duk Fillani ne ƴan uwansa. Sannan uwa uba, talakawan ƙasar basa ganin banbancinsa da su.

Lokacin da wasu Fillani dake zaune a cikin dazuzzuka a waɗansu yankuna na Nijeriya s**a fara ɗaukar mak**ai akan talakawan yankin da suke da sunan kare kai, Hausawan Nijeriya sun goyi bayan Fulani har suna ganin ƙiyayyar addinin Musulunci ne da ƙabilanci s**a sa waɗancan ƙabilun jidali da Fillani. Bahaushen mutum baya gani, ba kuma ya son yaji an faɗi laifin Bafillace.

Yau an wayi gari duk faɗin Nijeriya ba inda Fillanin daji ke ta'addanci da cin karen su ba babbaka k**ar ƙasar Hausa. Duk inda s**a gwada yin hakan tun daga ƙasashen Yarbawa har zuwa na Ibo da na Tibi, shugabannin yankunan na gargajiya da na addini da na siyasa sun haɗa ƙarfi da ƙarfe da talakawansu wajen taka masu birki don kare yankinsu da al'ummunsu; amma banda ƙasar Hausa.

Me yasa sai a ƙasar Hausa ne, gida ga dukkan Fillani, inda Fillani ne ke sarautar gargajiya da jagorancin siyasa da gwamnati, anan ne kaɗai ake ba ƴan ta'adda uzuri, anan ne suke cin karensu ba babbaka?

A kashe maza, a tozarta mata a tada ɗaruruwan ƙauyuka da gonaki, duk a ƙasar Hausa!

Duk waɗannan taadancin da fillanin daji ke yi a ƙasar Hausa babu wani fittaccen Shugaba ko Sarki ko jagoran siyasa a ƙasar Hausa da ya f

Meyasa ake yiwa hausa kisan kare dangi a kasar suFulani kuji tsoron ALLAH
16/11/2025

Meyasa ake yiwa hausa kisan kare dangi a kasar su
Fulani kuji tsoron ALLAH

Address

Bakin Kasuwa Faggo
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mukaru da Juna posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category