Abdulrashid Yali

Abdulrashid Yali Bauchi liman mahamood Street

20/01/2026

With MALAM – I'm on a streak! I've been a top fan for 14 months in a row. 🎉

---Wani lokaci a ƙauye wani mutum yana da jaki guda ɗaya, shi ne kaɗai abin da yake amfani da shi wajen ɗaukar kaya da z...
03/09/2025

---

Wani lokaci a ƙauye wani mutum yana da jaki guda ɗaya, shi ne kaɗai abin da yake amfani da shi wajen ɗaukar kaya da zirga-zirga. Mutumin yana ƙaunar jakin sosai, saboda shi ne ginshiƙin rayuwarsa.

Rana ɗaya sai mutumin ya ɗora kaya masu nauyi a kan jakin ya nufi kasuwa. A hanya, sai jakin ya tsaya ya ƙi tafiya. Mutumin ya yi ta bugawa da ƙorafi, amma duk da haka jakin ya tsaya kyam, bai motsa ba.

Da ɗan lokaci sai mutumin ya sauko daga bayan hanya ya zauna yana tunani. A lokacin ne wani dattijo ya wuce, ya ce masa:

“Ya kai bawan Allah, ba duka ba tsawa ne za su sa wannan jaki ya motsa. Idan ka nuna masa tausayi, kuma ka sauke ɗan nauyi daga bayansa, zai yi tafiya da yardar kansa.”

Mutumin ya saurara. Ya ɗan sauke wani ɓangaren kaya, ya shafa jakin a baya cikin tausayi, sannan ya ja igiyarsa cikin nutsuwa. Nan da nan jaki ya motsa ya fara tafiya, har s**a isa kasuwa lafiya.

Daga wannan rana, mutumin ya fahimci darasi cewa duk wani halitta, ko dabba ce ko mutum, idan ka nuna masa tausayi da adalci, zai amsa maka da biyayya. Amma idan ka zalunce shi, zai ƙi yin abin da kake so.
Dawane darasi kuka amfana cikin wannan labarin

---Malam✍️

02/09/2025

GASA!! GASA!! GASA!!

Ina Masoya Bala Wunti Ga dama ta musamman gare ku.....

Akwai gasa kan sabon waƙar da Rarara ya yi domin Bala Wunti.

Ka’idojin shiga gasa:

1. A yi video na waƙar cikin minti 2 kacal.

2. A yi tagging ga mawakan Rarara da Aisha Humaira tare da account ɗin Bala Wunti.

3. A samu likes 250 da comments 50 a shafin da aka saka bidiyon.

4. Dole a saka hotunan Bala Wunti a jikin bidiyon.

5. A yi amfani da waya ko kyamara mai ɗaukar hoto/bidiyo mai kyau.

Ranar rufe gasa:
Daga yau 31 ga Agusta 2025 zuwa 6 ga Satumba 2025 da ƙarfe 12 na dare.

Bayan an saka video ɗin, sai a tura mana da WhatsApp tare da link ɗin posting ɗin don tantancewa:
2347049481540

Kyaututtuka:

Na ɗaya – ₦120,000
Na biyu – ₦80,000
Na uku – ₦50,000

Alkalan gasa:

Muhammad Sani Abdulhamid (Chairman)

Abdullahi Chinade Abdullahi

Ibrahim Weeza

Abdusalam Abdullahi

Khadija Usman

Giftson Bitrus

Masu ɗaukar nauyi:

Shalelen Nasaru

30/08/2025

🟡 Bambancin Jikin Namiji da Mace 🟡

🔹 Namiji yana da zagayen hormone na awanni 24.

Safiya: Yana cike da kuzari da natsuwa.

Tsakiyar rana: Yana da himma da jarumta.

Yamma: Yana fara yin kasala.

Dare: Jiki yana bukatar hutu.

🔹 Mace kuwa tana da zagayen hormone na kwanaki 28.

Bayan al’ada: Tana samun kuzari da himma.

Lokacin ovulation: Tana jin farin ciki, ta cika da kuzari.

Bayan haka: Tana buƙatar hutu da tunani.

Lokacin haila: Jiki yana neman cikakken hutu.

🌿 Wannan yana nuna cewa halin da muke ciki na yau da kullum yana da alaƙa da yadda jikinmu yake aiki. Ka fahimci jikinka, ka kula da shi.

28/08/2025

TAUSAYIN TSADAR RAYUWAR GA MA'AIKATA GWAMNAN JIHAR IMO YA KARA ALBASHI ZUWA 104,000.
______

Gwamnan Imo Ya Ƙara Mafi Ƙarancin Albashi Zuwa N104,000

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya amince da ƙarin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan gwamnati a jihar daga N76,000 zuwa N104,000.

Uzodimma ya sanar da wannan sauyi ne a lokacin wata ganawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago da aka gudanar a daren Talata a fadar gwamnatin jihar da ke Owerri.

A cewar rahoton jaridar The Punch da kuma Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN), ƙarin ya shafi ma’aikata daban-daban, inda:

Mafi ƙarancin albashin likitoci ya tashi daga N215,000 zuwa N503,000

Na malamai a manyan makarantu daga N119,000 zuwa N222,000

Da kuma sauran ma’aikata bisa tsari.

Gwamnan ya bayyana cewa ma’aikatan jihar sun fuskanci manyan ƙalubale tun bayan zuwansa mulki, ciki har da matsalar tsaro, annobar COVID-19, matsin tattalin arziki sakamakon manufofin gyara, da kuma rikici kan mafi ƙarancin albashi da cire tallafin man fetur.

Ya ce: “Idan aka biya ma’aikata albashi mai kyau, za a samu ƙwarewar aiki, iyalai su more rayuwa mai sauƙi, kuma tattalin arzikin cikin gida ya bunƙasa.”

Uzodimma ya kuma bayyana cewa kudaden shiga na jihar (IGR) sun ƙaru daga N400m zuwa sama da N3bn a kowane wata, lamarin da ya bai wa gwamnati damar ɗaukar wannan sabon mataki.

ME ZAKU CE KAN HAKAN.....?

09/06/2025
04/06/2025

Allah sarki😭😭 Na dauki wasu Dalibai s**a dinga zabga turanci tunaninsu Ni timine😆😆 Kawai sai s**aji na sako Baki Ana buga yaran bature Dani😆 .

Wai Mai napep Amma kaje makaranta nace a hanya na koya, Ya akai...?😆😆 wlh abun ya Basu mamaki.

Duk Wanda kaganshi da sabon Dan sahu akan kwalta magana ake ta kusan 5 million. 😭

Saboda iya gwangwanin sa ma,Ana kafin a rufashi anasaida shi 3.5 {million uku da rabi}

Kuma a baka purchase 4.5 wasuma 5 million 😭 Amma a Haka wani zai baka #50 yace make Haka take biya😭 Bayan yanzu Babu passinger na #50.

A hakan ma wasu bibiyarka suke su sace maka😭😭Harkar Nan Tana bukatar Girmama mawa wajen alummah. Zaka iya daukan Dalibi/Daliba wasu su dinga kallon ai Kai Kamar bakayi karatu ba.

Saboda Taimakon juna muke Muda passinger ❤️❤️❤️🤏 Allah ya bamu nasara ya rabamu da miyagu🤲🤲 muyi following juna saboda samun karfin guiwa na kawo sabon labari


Matukin Adaidaita Sahu Abdulrasheed MALAM #

01/04/2025

DAURE KA/KI KARANTA KUMA AYI SHARING!

Tabbas, baza kasan kai waye bane sai kazo aure? Aure na saura kwana kadan kuma ina da matsalar wasu kudade wanda hakan yasani dole na bi kan yan uwa da abokan arziki don su taimaka min da aro amma sai de kash duk wanda na tunkare shi sai kaji yana komawa gefe.

Tabbas, ina jin ciwo kuma na rasa yadda zanyi, na mika komai a gurin Allah. Ina cikin wannan zulumin ne sai na tuna ina da shafin Facebook ( MALAM mai followers sama da dubu 15K shine sai na yanke shawara na yi posting bukatun na ko da Allah zai sa na dace da mutane masu karfin hali.

Abun da ya fi bani ciwo shine yadda yan uwa masu wada suke barin dangin su batare da tamaka musu ba lokacin da suke bukata.

Naje gurin wani dan uwana wanda nake tunanin Zai iya share min hawaye na amma abun takaici da na tambaye bukatuna sai yace min zai duba, dubawan da baiyi ba kenan har yanzu.

Wallahi, tun da nake a rayuwata banta roko ba sai wannan karon kuma dole ce tasa ni. Ko anan social media nayi ne saboda ina tunanin akwai mutanen kirki Wanda in Allah yasa na dace to za su iya taimaka min.

Ko ni a wannan Page din na sha nemawa mutane taimako suna kuma dacewa. Allah yaga zuciyata kuma yasan manu fata, in karya nake ya sani in kuma gaskiya ne to ya sani. Nasan yin rubutu a social media don neman bukata yana cike da kalubale, wasu za suyi tunanin kai Dan damfara ne ko kuma kana karya ne, wasu kuma za su ma comments din izgili amma duk da hakan ina da karfin gwuiwar samun wanda za su taimaka min saboda Allah kuma da zuciya mai kyau.

Wallahi bukata ba ta wuce 300k ko kuma 150k ba kuma ita ma aro ne ke nema wanda insha Allah zan biya a hankali bayan biki. In har akwai mai niya dagaske zai iya min magana ta inbox ko don na masa karin bayani.

Ga account number ta kamar haka:

Account number: 2032798085

Bank: first bank.
Bank name Abubakar Abdurrashid

Nagode!

Address

Bauchi Liman Mahmood Street
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abdulrashid Yali posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category