18/09/2025
ALHAMDULLAH, ALHAMDULLAH,
SANATA MUHAMMADU ADAMU ALIERO YA GWANGWAJE IZALA JAHAR KEBBI , DA KWALEJIN KIWON LAFIYA( College of Health Science and Technology)
Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta Jihar Kebbi ta yi nassarar samun katafaren ginin makarantar koyon kiwon lafiya a cikin Birninkebbi wanda Sanata Muhammadu Adamu Aleiro (Sanatan Kebbi ta tsakiya) ya gina daga cikin ayukan mazaba.
Da yake jawabi Shugaban Kungiyar izala na jihar Kebbi , Sheikh Aliyu Adam Ladda Bunza ya gabatar da matukar godiya akan ayukan Alheri da yayiwa wannan Kungiyar, wanda s**a hada da babbar sakatariyar kungiya wadda yayi tun yana kan kujerar Gwamna da sauran Ayukan.
A nashi jawabi, Sanata Muhammadu Adamu Aleiro gadiya yayiwa shugabannin kungiya akan ziyarar da s**a kawo masa wanda saboda farin ciki har kara jaddada cewa kada kungiya ta sake neman izinin kawo masa ziyara ,duk lokacin da ake son ganin sa kofa a bude take, bangaren ginin makarantar horadda ayukan kiwon lafiya kuwa ya tabbatar da kammala aikin nan zuwa kafin karshen wannan shekara ta ,2025.
Kuma ita makarantar an dauko kammala ta cikin tsari guda 3, tsari na farko shine ginin ajuzuwa da ofisoshi, na 2 Kuma gina dakunan bincike na kimiya ( Laboratories) sai tsari na 3 shine saka kayan aiki a cikin su.