Cmrd Rabi'u A'A Dandume

Cmrd Rabi'u A'A Dandume Fear Allah Wherever you are

Kira Zuwa ga YAN Uwana Matasa masu ta'ammali da wannan kafa ta Facebook Dangane da kalaman batanci da cin zarafin juna d...
13/09/2026

Kira Zuwa ga YAN Uwana Matasa masu ta'ammali da wannan kafa ta Facebook Dangane da kalaman batanci da cin zarafin juna da wasu sukeyi
Assalamu alaikum
# # # # # # # # # # # # # # # #
Maganar gaskiya itace
Wasu Suna siyasa a makan CE ida nun su rufe kamar Wadanda ba suyi karatu ba Kai wasu in mukai duba da kyau za muga ta wani bangaren ma gara Wadanda ba suyi karatun bama dasu Koda yake karatu daban tarbiyya daban duba da yadda s**a dauki siyasar
""""""""""""""""
Yana da kyau Musani cewa ita fa siyasa bai zama dole ace duk abinda kake so sai al'ummah sun so Shi ba wannan Yasa Nike ganin kuskuren dukkan Wanda suke kallon Wadanda s**a Sha ban ban a siyasa Ama tsayin abokin gaba harma kaji yana furta Muna Nan kalamai a gare Shi tare da cin zarafin Shi Dana iyayen Shi Wanda hakan ko kadan baida ceba
Domin ita siyasa duk Wanda yasanta ya San cewa Bata da masoyi na din din haka Kuma Bata da maqiyi na din din
Amma babban abin ta kaici mun tsinci kanmu a wani Hali Wanda zakaga sbd ban bancin ra'ayi kawaii Sai kaga wasu Suna kallon Wanda ra'ayin su baizo Daya ba kamar Wanda yayi ridda
Ya Kai Mai irin wancan tinanin ya kamata kadawo hankalin ka kayi karatun ta natsu kagane cewa samun wani bai Hana naka, Kuma dukkan abinda Allah ya rubuta Zaka samu a Rayuwar ka baza kabar duniya ba har sai ka same Shi sannan Kuma kasani ba sai kaci zarafin wani ba ko kayi fitina da wani ba Zaka samu
Allah Yasa Mudace Ya bamu ikon gyarawa Amin
Naku Har kullum
Rabee'u El-zakareeya Dandume Lahadi 13/09/2026.

SANARWA!    SANARWA!    SANARWA!Kwamitin Shirya Maulidin Zagaye gari ƙarƙashin Majalisar Shura Ta Muryar Dariƙa, Reshen ...
08/08/2026

SANARWA! SANARWA! SANARWA!
Kwamitin Shirya Maulidin Zagaye gari ƙarƙashin Majalisar Shura Ta Muryar Dariƙa, Reshen Ƙaramar Hukumar Dandume

Yana sanar da Al'ummar Annabi Muhammad saw cewa za'a yi Zagayen Maulidin bana kamar yadda Majalisar Amintattu ta Shura ta cimma matsaya kamar haka

1. ZAGAYEN MAKARANTUN ISLAMIYYOYI

RANA: Lahadi ta biyu ga Watan Rabi'ul Thani 9/4/1448. Hijrah

Daidai da

20/9/2026. miladiyya

2. ZAGAYEN DUKA GARI KUMA

RANA: Lahadi ta biyu ga watan 5, Jimada Awal

14/5/1448. Hijrah

Daidai da

25/10/2026. miladiyyah

Allah ya kaimu ya bamu Arzikin yin Khidima ga Annabi Muhammadu SAWW

Tuntuɓa

WANNAN SHINE KOYARWAR SUFAYE SUFANCI NA FUSKANTAR DA BAWA NE ZUWA ABABE GUDA 5.1- Kyautata alaka da ALLAH, ta hanyar aik...
20/07/2026

WANNAN SHINE KOYARWAR SUFAYE SUFANCI NA FUSKANTAR DA BAWA NE ZUWA ABABE GUDA 5.

1- Kyautata alaka da ALLAH, ta hanyar aikata ababen da ya yi umarni, da nesantar hane-hanensa, lazimtar halarto da tsoronsa badini da zahiri cikin komai a ko ina, kwadayin falalarsa, tsoro tare da neman tsari daga jalalarsa, neman yardarsa cikin ibada daga barin yin jinga da shi.

2- Bin MANZON ALLAH (S.A.W) cikin zance da aiki, soyayyarsa da tsananta ladabi gareshi, girmama duk abinda ya alakantu da shi, neman albarkasa da kuma neman kusanci da shi duniya da lahira.

3- Kyautata alaka da dukkan halittun ALLAH, cikin barin kudurtar cuta b***e cutarwa, cikin son amfanarwa da riskar da alkairi, cikin cirarwa zuwa ga aikata kyakkyawa daga barin mummuna.

4- Tsarkake zuciya da neman jibancin ALLAH a kan lamarin Nafsu, ta hanyar lazimtar zikirin ALLAH, neman tsira daga kaidin Shedan cikin umarni da mummuna da hani ga aikata kyakkyawa.

5- Kishi da son yaduwar Addinin ALLAH, neman ilmin addini da ilmantar da bayin ALLAH, yada addini da baiwa addini kariya, kyautata da'awa ga wadanda ba Musulmi ba, tare da kiyaye harshe ga Musulmi yayin mu'amala.

ALLAH KA TABBATAR DA MU BISA TAFARKIN SUFANCI, KA TSARE MU BIYEWA SABANIN HAKA.
Rabiu Zakariyya Dandume

Alhamdulillahi ✖️3    A Ranar Lahadi 31/05/2026 Muka Gudanar da Taron Sada zumunci Na tsoffin Daliban Makarantar GDPSS D...
02/06/2026

Alhamdulillahi ✖️3
A Ranar Lahadi 31/05/2026 Muka Gudanar da Taron Sada zumunci Na tsoffin Daliban Makarantar GDPSS Dandume Wadanda Muka kammala a Shekarar 2011 Haqiqa Munyi zumunci da juna Mun Kuma tattauna Muhimman abubuwa da S**a shafi cigaban Rayuwar Mu da Muhimmancin zumunci da taimakon juna Muna Godiya Matuqa da Malahalarta dama Wadanda Basu Samu damar halarta ba Allah Ya Saka ma kowa da Alkhairi Ya Kuma Maimaita Mana Yaqara hada kawunan Mu Allahumma Amin Ya Allah
Cmrd Rabiu Zakariyya Dandume
Chairman of the Occasion

29/05/2026

This version of Facebook uses less data and works in all network conditions.

Ya Allah buwayi ga gara Misali Kaine Mahaliccin Mu Majibin cin Lamuran mu    Muna roqon Ka da kyawawan Sunayen Ka Tsarka...
23/05/2026

Ya Allah buwayi ga gara Misali Kaine Mahaliccin Mu Majibin cin Lamuran mu
Muna roqon Ka da kyawawan Sunayen Ka Tsarka Ka kashiga cikin Lamarin Mu kabamu kariya da kariyar Ka kajiqan Magabatan Mu Ka kyautata karshen mu Ka azurtamu da arzikin Ka Mayalwaci Kasa Mufi karfin zuciyar mu Allah Kabamu Dawwa mammen zaman Lafiya A karamar hukumar mu ta Ɗandume, jahar Mu ta Katsina dama Kasarmu Nigeria Baki Daya
Ya Allah kakawo Mana karshen Wannan Musiba data addabe Mu Ka amintar damu katsaya Mana da tsayawar Ka Alfarmar Annabi Muhammadu s.a.w da Al'qur'ani.
Rt. Comrd Rabee'u El-zakareeya Dandume

AMFANIN HAƊIN KAI GUDA GOMAAllah Maɗaukaki ya ce:“ ku yi riƙo da igiyar Allah gaba ɗaya, kada ku rarraba.”— Al-Qur'an 3:...
07/05/2026

AMFANIN HAƊIN KAI GUDA GOMA

Allah Maɗaukaki ya ce:

“ ku yi riƙo da igiyar Allah gaba ɗaya, kada ku rarraba.”

— Al-Qur'an 3:103
Annabin Rahma (saw) ya ce:

“Muminai a cikin soyayya da tausayi da jinƙai kamar jiki guda ne.”

( Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim)

Abubuwa goma da Hadin kai yake kawowa :

1. Samun ƙarfi da ɗaukaka

Haɗin kai yana sa al’umma ta zama mai ƙarfi, abin girmamawa da tsaro.

2. Nasara akan maƙiya

Idan mutane s**a haɗu s**a zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, maƙiya ba sa samun damar rarraba su.

3. Yawaitar soyayya da ƙauna

Haɗin kai yana kawar da ƙiyayya, hassada da gaba tsakanin mutane.

4. Sauƙaƙa ayyuka masu wahala

Aiki idan an haɗa hannu ana samun sauƙi da saurin kammalawa.

5. Samun ci gaba a al’umma

Duk wata al’umma mai haɗin kai tana samun bunƙasa a ilimi, tattalin arziki da tsaro.

6. Karfafa addini da gaskiya

Haɗin kai tsakanin masu gaskiya yana taimakawa wajen ɗaukaka addini da yaɗa alheri.

7. Kawo zaman lafiya

Inda akwai haɗin kai ana samun kwanciyar hankali da zaman lafiya.

8. Taimakon juna a lokacin buƙata

Haɗin kai yana sa mutane su riƙa taimakon juna cikin wahala da damuwa.

9. Kariya daga fitina da rikice-rikice

Rarrabuwar kai tana kawo fitina, amma haɗin kai yana hana hakan.

10. Samun yardar Allah

Musulunci ya ƙarfafa haɗin kai da kauce wa sabani

Haɗin kai ginshiƙi ne na ci gaban al’umma da nasararta. Duk inda aka samu haɗin kai, za a samu ƙarfi, zaman lafiya da albarka. Amma rarrabuwar kai tana jawo rauni da koma baya.

Allah ya haɗa kanmu akan gaskiya.
Rabiu Zakariyya Dandume
07/05/2026

Kira Zuwa ga YAN Uwana Matasa masu ta'ammali da wannan kafa ta Facebook Dangane da kalaman batanci da cin zarafin juna d...
30/04/2026

Kira Zuwa ga YAN Uwana Matasa masu ta'ammali da wannan kafa ta Facebook Dangane da kalaman batanci da cin zarafin juna da wasu sukeyi
# # # # # # # # # # # # # # # #
Maganar gaskiya itace
Wasu Suna siyasa a makan CE ida nun su rufe kamar Wadanda ba suyi karatu ba Kai wasu in mukai duba da kyau za muga ta wani bangaren ma gara Wadanda ba suyi karatun bama dasu duba da yadda s**a dauki siyar
""""""""""""""""
Yana da kyau Musani cewa ita fa siyasa bai zama dole ace duk abinda kake so sai al'ummah sun so Shi ba wannan Yasa Nike ganin kuskuren dukkan Wanda s**a Sha ban ban a siyasa Ama tsayin abokin gaba harma kaji yana furta Muna Nan kalamai a gare Shi tare da cin zarafin Shi Dana iyayen Shi Wanda hakan ko kadan baida ceba
Domin ita siyasa duk Wanda yasanta ya San cewa Bata da masoyi na din din haka Kuma Bata da maqiyi na din din
Amma babban abin ta kaici mun tsinci kanmu a wani Hali Wanda zakaga sbd ban bancin ra'ayi kawaii Sai kaga wasu Suna kallon Wanda ra'ayin su baizo Daya ba kamar Wanda yy ridda
Ya Kai Mai irin wancan tinanin ya kamata kadawo hankalin ka kayi karatun ta natsu kagane cewa samun wani bai Hana naka, Kuma dukkan abinda Allah ya rubuta Zaka samu a Rayuwar ka baza kabar duniya ba har sai ka same Shi sannan Kuma kasani ba sai kaci zarafin wani ba ko kayi fitina da wani ba Zaka samu
Allah Yasa Mudace Ya bamu ikon gyarawa Amin

22/08/2025

WAJIBI NE KOWANNE BALIGI KO BALIGA SU SAN BANBANCI TSAKANIN WADANNAN

1_ MANIYYI
2_ WAZIYYI
3_ WADIYYI

BABUJIN KUNYA ACIKIN SANIN ADDINI NANA AISHA (R.T.A) TANA CEWA ALLAH YAJI ƘAN MATAN MADINA KOKAƊAN KUNYA BATA HANASU NEMAN ADDININSU.

1_ MANIYYIN NAMIJI
Maniyyin Namiji Ruwane Mai Kauri Fari Wanda Yake Fitowa Yayin Babbar Sha'awa Ko Wasada Zakari Sannan Yana Tunkuɗo Juna Lokacin Da Yake Fitowa Kuma Warinsa Yana K**ada Warin Hudar Dabino Ko Damamman Gari Idan Kuma Yabushe Yana Ƙamshin Kwai.

1_ MANIYYIN MACE
Maniyyin Mace Shima Ruwane Tsinkakke Mai Fatsi Fatsi Fari Wanda Yake Fitowa Yayin Babbar Sha'awa K**ar Saduwa Ko Wasa Da Farji Sannan Yana Tunkuɗo Juna Lokacin Dayake Fitowa Zataji Tsananin Sha'awa Da Daɗi Lokacin Da Yake Fitowa Kuma Warinsa Yana K**a Da Warin Hudar Dabino Ko Damamman Gari Yana Ƙamshi Idan Yabushe Shima Yana Ƙamshin Kwai Sannan Sha'awa Zata Yanke Bayan Fitowarsa.

HUKUNCIN FITAR MANIYYI SHINE, YANA WAJABTA WANKA.

2_ MAZIYYI
Ruwane Tsinkakke Dayake Fitowa Yayin Ƙaramar Sha'awa K**ar Tunanin Aure Ko Kuma Tuna Wacce Kakeso Ko Matarka Ko Kallan Matar Wani, Mace Kuma Yana Fitowa Ne Idan Tayi Tunanin Mijin Da Take Sha'awa Kuma Yana Fitowa Yayin Wasa Tsakanin Miji Da Mata Saidai Shi Baya Tafiyar Da Sha'awa Kuma Wani Lokacin Ba'a Sanin Yafito Sannan Yafi Fitowa Mata Fiye Da Maza.

HUKUNCINSA SHINE WANKE FARJI GABADAYA.

3_ WADIYYI
Wani Farin Ruwane Dayake Fitowaa Abayan Fitsari Kokuma Lokacinda Aka Ɗauki Abu Mai Nauyi Kuma Yafi Fitowa Marassa Aure Mace Ko Namiji.

HUKUNCNSA SHINE WANKE WAJAN.

Allah Kabamu Ilimi Mai Amfani Duniya Da Rahira Wallahu A'alam.

RUFE TAFSIR DA KHATAMA 2025/1446Amadadin kwamitin Gudanar da Tafsirin Al Qur'ani Mai Girma na Babban Masallacin Juma'a N...
25/03/2025

RUFE TAFSIR DA KHATAMA 2025/1446

Amadadin kwamitin Gudanar da Tafsirin Al Qur'ani Mai Girma na Babban Masallacin Juma'a Na cikin Garin Dandume L.g Katsina.

Wanda Khalifa Sheikh Tijjani Sheikh Abdullahi Dandume tare da Alaramma M. Aliyu Abubakar suke gabatarwa.

Ana sanar da Al'umma idan Allah ya kaimu Ranar Alhamis 27/08/1446/ zaayi Khatama na sauka sannan Kuma Za'a rufe Tafsirin wannan Shekarar.

Da karfe goma na safe, a Babban Masallacin Juma'a Na cikin Garin Dandume.

Allah ya bada ikon Halarta.
Ameeen

Address

Hizburraheem U/Rimi Dandume
Dan Dume

Telephone

+2347033068885

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Cmrd Rabi'u A'A Dandume posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Cmrd Rabi'u A'A Dandume:

Shortcuts

Share

Category