09/11/2025
An Ruwaito, MANZON ALLAH(S.A.W) Lokacin Da Ya Je Al'arshi a Daren Mi'iraji Yayi Nufin Ya Cire Takalmansa,
Sai Aka Ƙira Shi: "Me Yasa Zaka Cire Takalmanka???"
Sai Ya Ce:
"Ina Jin Tsoron Kar a Faɗa Min Abin Da Aka Faɗawa Ɗan-uwana ANNABI MUSA(A.S);
اخلع نعليك
Sai Aka Ƙira Shi(Da Wata Murya):
"Ya RASULULLAHI! Idan MUSA, Yana Da Nufi, Kai Kuma Kai Ne Abin Nufin,
Idan MUSA Ya Kasance Yana So, Kai Kuma Kai Ne Abin Son,
Idan MUSA Yana Nema, Kai Kuma Kai Ne Abin Neman,
Idan MUSA Ya Kasance Makusanci, Kai Kuma Masoyi Ne."
Tambaye Ni Abin Da Kake So, Ni Mai Ji Ne, Kuma Mai Amsawa;
Sai MA'AIKI(S.A.W) Ya Ce: "Ya UBANGIJINA! Ba Ina Roƙonka AMINATU Wacce Ta Haife Ni Ba Ne, Ko HALIMA Wacce Ta Shayar Da Ni, Ko FAƊIMATU 'Ya Ta, A'a, Ina Roƙonka Ne Al'umata.!"
Sai ALLAH(S.W.T) Ya Ce:
"Ya NABIYYUR-RAHMATI! Tausayinka Ga Al'ummarka, Al'ummarka Halitta Ce Mai Rauni,
Ni Kuma UBANGIJI Ne Mai Tausasawa, Kai Kuma ANNABI Ne Mai Girma.
Mai Rauni Ba Zai Tozarta Ba a Tsakanin Mai Tausasawa Da Mai Girma.
Na Rantse Da Girmana Da Ɗaukakata Ranar Ƙiyama Zan Raba Tsagi Biyu Tsakanina Da Kai, Kana Cewa; Al'ummata Al'ummata, Ni Kuma Ina Cewa; Rahmata Rahmata!".
صلوعلى بدرالمنيروالسراج الوهاج
ALLAH Ya 'Kara Rura Wutar SOYAYYAR ANNABI MUHAMMADU(S.A.W) a Cikin Zukatanmu, Ya Sa Mu Cikin CetonSA(S.A.W), Ameeeen❣️🙏😭
DUK MAI ƘAUNAR ANNABI ﷺ YAYI SHEARING