23/02/2026
Matsalar Tsaro Ta Tsananta A Yankin Alkaleri Dake Jihar Bauchi.
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a yammacin jiya a kauyukan Guruza, Gwana, Mansur, Wundo, Digare, Kafin-Duguri duk a karkashin karamar hukumar Alkaleri jihar Bauchi.
Yayin da s**a tada hankalin al’umma tare da tilasta musu tserewa daga garuwansu domin ceton rayukansu.
Har yanzu ba a tabbatar da adadin waɗanda s**a mutu ba, sai dai ana fargabar an samu asarar rayuka da dukiyoyi.
A yau kuma, daruruwan mutaneb dake zaune a garin, sun fara barin gidajensu sakamakon ci gaba da barazanar hare-hare.
Yayin da harkokin kasuwanci da noma s**a tsaya cik.
Al’ummar yankin na kira ga hukumomi da su dauki matakan gaggawa domin maido da zaman lafiya.