YIM HAUSA

YIM HAUSA Yim News Hausa

Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran IRGC, ta sanar da kaddamar da manyan hare-hare da makamai masu linzami ...
01/03/2026

Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran IRGC, ta sanar da kaddamar da manyan hare-hare da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan sansanonin Amurka guda 27 a faɗin Gabas ta Tsakiya.

Waɗannan hare-hare da IRGC ta kira Kashi na Shida na ayyukan True Promise 4, ya biyo bayan kisan babban jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, da aka yi a wani harin haɗin gwiwa na Amurka da Isra'ila.

Bayan sansanonin 27 na Amurka, IRGC ta yi iƙirarin kai hari kan sansanin jiragen sama na Tel Nof da ke Isra'ila, da kuma hedikwatar rundunar sojin Isra'ila da ke Tel Aviv.

An ƙaddamar da hare-haren kan sansanonin Amurka da ke ƙasashen Bahrain inda hedikwatar runduna ta 5 take, sai Qatar Kuwait, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, da kuma Jordan.

IRGC ta yi gargadin cewa wannan harin somi taɓi ne, domin za su ci gaba da kai munanan hare-hare har sai sun ga bayan abokan gabarsu a yankin.

Hukumomin ƙasashen da abin ya shafa, kamar ma'aikatar tsaron Qatar, sun tabbatar da daƙile wasu daga cikin makaman, yayin da aka dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a sassa da dama na yankin.

28/02/2026

Idan Kana kashi Ka hango yan Social Media




28/02/2026

Amurka da Gaske Take Domin Ganin Andaina Shari'ar Musulunci a Najeriya.




Address

Gombe Northern Nigeria
Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when YIM HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category