Abuu ikrima العلاج با القرآن والسنة

Abuu ikrima العلاج با القرآن والسنة GIDAN YIN MAGANI TA HANYAR ALQUR'ANI DA SUNNAH TARE DA ƳAƳAN ITATUWA.

11/10/2025

Assalamu Alaikum Warahmatullah

20/11/2024

🌳🌴🌿☘️ 🙏🏻🙏🏻🌾💐🪻🌲

MAFI GIRMAN HANYA DA AKEBI WURIN WARWARE DA LALATA MATSALAR (SIHIRI) KO (MAITA) DAKE TARE DA MUTUM DAKUMA SAMUN CIKAKKEN RIGAKAFI.

((ÃYATUS SIHIRI))

Assalamu alaikum
Warahmatullah

Ƴan'uwa masu Albarka barkanku da warhaka da fatan Kuna cikin Aminci da qoshin lafiya tare da dukkanin Ahalinku Allah yasa haka.

Haqiqa ina mai farincikin gabatar muku da (Ãyatus Sihiri) da irin matuqar Ta'asirinsa a rayuwar Musulmi.

👉🏼 GASU KAMAR HAKA:

1: Karanta Suratul FATIHA, sau 3 ko 7

2: Karanta Aya ta (102) na Suratul Baqara (Wattaba'u...) sau 3 ko 7

3: Karanta (Ãyatul Qursiyyi) sau 3 ko 7

4: Karanta Aya ta 117 zuwa 122 na Suratul A'arafi (Wa Auhainaa..) sau 3 ko 7

5: Karanta Aya ta 79 zuwa 82 na Suratu Yunus (Waqala Fir'aunu..) sau 3 ko 7

6: Karanta Aya ta 65 zuwa 70 na Suratu Daha (Qãlu yaa Musa..) sau 3 ko 7

7: Karanta Suratul ikhlas da Suratul Falaq da Nasi, sau 3 ko 7

👉🏼 YADDA ZA'A KARANTASU

Da farko mutum zai samu Ruwan Sama inya samu imbe samuba to sai asami Ruwa mai tsarki dai dayin buqata sai a Sanya ganyen Magarya danye ko busashshe a garwaya sai a samu wani bawan Allah mai qoqari ya karanta waɗannan Ayoyi da Surorin aciki ana tofawa, ko kuma mai karatun ya kusanto da abinda ruwan keciki dab da bakinsa, kowanne tare da A'uziya da Bismillah,

👉🏼 YADDA ZA'AYI AMFANI DASHI

➡️ Mutum zai Sha Kuma yayi wanka dashi amma ba'a banɗaki ba, zai game dukkannin jikinsa, Safe da dare kafin a kwanta na kwana 3 ko 7.

➡️ Sa'anan za'a iya yayyafawa a cikin daki tare dayin Bismillah domin kore duk wani mugun abu dake cikin ɗakin.

👉🏼 FA'IDOJINSA

Haqiqa Karanta waɗannan Surori da Ayoyi masu Albarka nada matuqar muhimmanci a rayuwar Musulmi tare da Fa'idoji dayawa, ga kaɗan daga ciki:

1️⃣: Yana warware SIHIRI nan take.

2️⃣: Yana koran Aljani da aka tura nan take daga jikin Mutum.

3️⃣: Yana qona duk wani Cuta da Aljani ko maye yasa a jikin Mutum.

4️⃣: Yana Lalata Shirin MAITA nan take .

5️⃣: Yana iya kashe Aljani ko Maye idan s**ayi taurin kai.

6️⃣: Yana bayyana SIHIRI ko MAITA nan take a jikin Mutum.

7️⃣: Yana dawo da mutum cikin hayyacinsa nan take.

8️⃣: Yana dawowa mutum da Lafiyarsa da Kuzarinsa.

9️⃣: Yana toshe mashigar Aljani ko Maye a jikin mutum.

1️⃣0️⃣: Kuma babban riaga kafine daga dukkan wani mugun HALITTA.

👉🏼 Duk wannan yana Ta'asirine da izinin Allah, sa'anan dakuma Emanin mutum.

👉🏼TAJRIBA

💯 Babu shakka ni bazan iya sanin adadin mutane dana haɗa musu ko s**ayi da kansu s**a samu waraqa ba.

🤲🏼 Yaa Allah kayimana muwaafaqa ka Amintar damu a rayuwa.

@ ABUU IKRIMA

👉🏼 Daga Zauren Abuu ikrima na
(دار العلاج با القرأن والسنة مع الأعشاب)
WHATSAP

👉🏼 Don Karin bayani ko Tambaya
(07061933096) ☎️

15/08/2024
14/03/2024

Assalamu alaikum warahmatullah

21/02/2024

🌵🌵 🌴🌴 ☘️☘️

بسم الله الرحمن الرحيم

𝑭𝑨'𝑰𝑫𝑨𝑹𝑴𝑼 𝑻𝑨 𝒀𝑨𝑼
0️⃣5️⃣

𝑨𝑴𝑭𝑨𝑵𝑰𝑵 𝑯𝑨𝑫𝑰𝑵 𝑺𝑯𝑰𝑭𝑨'𝑼𝑵 𝑳𝑰𝑵𝑵𝑨𝑺

➡️ Masana s**ace:
Yin amfani da wannan hadin yana karawa mutum lafiya tare da nishadi da kuzari kuma yana yaqar cututtuka dake jikin dan Adam, kuma riga kafine mai karfi, wannan yasa ake cewa (Shifa'un linnas), gasu kamar haka:

1- 𝑮𝑨𝑹𝑰𝑵 𝑯𝑨𝑩𝑩𝑨𝑻𝑼𝑺𝑺𝑨𝑼𝑫𝑨
𝒎𝒂𝒊 𝒊𝒏𝒈𝒂𝒏𝒄𝒊
2- 𝑴𝑨𝑵 𝒁𝑨𝑰𝑻𝑼𝑵, 𝒎𝒂𝒊 𝒊𝒏𝒈𝒂𝒏𝒄𝒊

3- 𝒁𝑼𝑴𝑨, 𝒎𝒂𝒊 𝒊𝒏𝒈𝒂𝒏𝒄𝒊.

👉🏼 𝒀𝑨𝑵𝑫𝑨 𝑨𝑲𝑬 𝑯𝑨𝑫𝑨𝑺𝑼

Za a samu Zuma mai kyau, Kofi 1, sai Garin Habba Cokali 4 sai kuma Man Zaitun Cokali 3, bayan an hadasu sai ana sha cokali 1 da safe 1 da dare, kuma yana dacewa ga dukkannin dabi'a.

🤲🏼 𝒀𝒂𝒂 𝑨𝒍𝒍𝒂𝒉 𝒌𝒂𝒚𝒊𝒎𝒂𝒏𝒂 𝑴𝒖𝒘𝒂𝒂𝒇𝒂𝒒𝒂𝒉 𝑫𝒖𝒏𝒊𝒚𝒂 𝒅𝒂 𝑳𝒂𝒉𝒊𝒓𝒂.

@ 𝑨𝑩𝑼𝑼 𝑰𝑲𝑹𝑰𝑴𝑨 ✍🏼

👉🏼 𝑫𝒂𝒈𝒂 𝒁𝒂𝒖𝒓𝒆𝒏 𝑨𝒃𝒖𝒖 𝒊𝒌𝒓𝒊𝒎𝒂 𝒏𝒂
(العلاج با القرأن والسنة)
𝑾𝑯𝑨𝑻𝑺𝑨𝑷

👉🏼 𝑫𝒐𝒏 𝑲𝒂𝒓𝒊𝒏 𝒃𝒂𝒚𝒂𝒏𝒊 𝒌𝒐 𝑻𝒂𝒎𝒃𝒂𝒚𝒂
(07061933096) ☎️

✍🏼✍🏼          ✍🏼✍🏼          ✍🏼✍🏼AYOYIN NEMAN SAMUN NATSUWA DA AMINCI DAGA DUKKAN FIRGICI.       Assalamu alaikum        ...
01/01/2024

✍🏼✍🏼 ✍🏼✍🏼 ✍🏼✍🏼

AYOYIN NEMAN SAMUN NATSUWA DA AMINCI DAGA DUKKAN FIRGICI.

Assalamu alaikum
Warahmatullah

Yan'uwa barkanku da warhaka da fatan Kuna cikin Aminci da qoshin lafiya tare da dukkanin Ahalinku Allah yasa haka.

Ina mai farincikin kawo muku wasu za6a66un Ayoyin Alqur'ani mai girma don neman samun Natsuwa da Aminci daga dukkan firgici, wanda ake kiran Ayoyin da suna (Ãyaatus Sakeena) Lalle sunada matuqar Ta'asiri na ban al'ajabi a rayuwar musulmi.

➡️ Babu shakka Magabata da dama sun jaraba Kuma sunga ta'asiri mai girma da ban mamaki.

👉🏼 ÃYATUS SAKEENA
➡️ Babban malaminnan IBNU QAYYIM (Allah yayimasa Rahama) ya fada a cikin littafinsa mai suna (Madarijis salikeena) shafi na (502-504) yana cewa: "Malamina Sheikhul islam IBNU TAIMIYYA yakasance idan al'amura s**a tsananta gareshi yakan Karanta (Ãyatus Sakeena) nan take sai ya samu Sauqi da Kuma Nutsuwa.

Sai IBNU QAYYIM (Allah yayimasa Rahama) yace: Kuma nima na jaraba karanta (Ãyatus Sakeena) a yayinda zuciyata ta fada cikin juyayi da rikicewa kuma naga ta'asiri mai girma a tare da ayoyin wurin Sanya Natsuwa da kwanciyar hankali.

👉🏼 GASU KAMAR HAKA:

1: Suratul Baqara aya ta (248).

2: Suratu Tauba aya ta (26).

3: Suratu Tauba aya ta (40).

4: Suratul Fathi aya ta (4).

5: Suratul Fathi aya ta (18).

6: Suratul Fathi aya ta (26).

👉🏼 YADDA ZA'A KARANTASU

Aduk sanda Mutum ya tsinci kansa cikin mawuyacin hali, sai ya zauna yayita karanta wadannan Ayoyin masu Albarka iya yadda ya sauwaqa da niyyar samun Natsuwa da kwanciyar hankali...

👉🏼 FA'IDOJINSA

Haqiqa Karanta wadannan Ayoyi masu Albarka (Ãyatus Sakeena) nada Fa'idoji dayawa ga kadan daga ciki:

1️⃣: Yana kawar da Tsoro a zuciya.

2️⃣: Yana Kawar da Firgicin zuci.

3️⃣: Yana kawarda shubuhohin a zuciya.

4️⃣: Yana sanya Natsuwa da kwanciyar hankali a zuci.

5️⃣: Yana Kawar da radadin Fitina a zuci .

6️⃣: Yana Kawar da Damuwa daga zuci.

7️⃣: Yana Kawar da Baqinciki daga zuci.

8️⃣: Yana kore waswasin zuuciya.

👉🏼 Duk wannan yana Ta'asirine da izinin Allah, sa'anan dakuma Emanin mutum da ikhlaainsa.

👉🏼TAJRIBA

💯 Babu shakka mutane da dama sunga ta'asirin wadannan Ayoyi masu Albarka.

🤲🏼 Yaa Allah kayimana muwaafaqa Duniya da Lahira.

@ ABUU IKRIMA

👉🏼 Daga Zauren Abuu ikrima na
(العلاج با القرأن والسنة)
WHATSAP

👉🏼 Don Karin bayani ko Tambaya
(07061933096) ☎️

26/12/2023

✍🏼✍🏼 ✍🏼✍🏼 ✍🏼✍🏼

AYOYIN NEMAN WARAKA DAGA DUKKANNIN RASHIN LAFIYA.

Assalamu alaikum
Warahmatullah

Yan'uwa barkanku da warhaka da fatan Kuna cikin Aminci da qoshin lafiya tare da dukkanin Ahalinku Allah yasa haka.

Ina mai farincikin kawo muku Ayoyin neman waraka wanda ake kiransu da (Ãyaatush Shifa'i) Wanda sunada matuqar Ta'asiri na ban Al'ajabi a rayuwar musulmi.

➡️ Babu shakka Magabata da dama sun jaraba Kuma sunga ta'asiri mai ban mamaki.

👉🏼 TARIHINN (Ãyaatush Shifa'i)

An ruwaito (lmamul Kushairi) yace: " Dana yayi rashin lafiya mai tsanani har saida na debe tsammani daga warkewarsa, sai al'amarin ya tsananta gareni nashiga wani mawuyacin hali, watarana na kwanta bacci sai nayi mafakin Annabi (S.a.w) sai na kokamasa rashin lafiyanda dana yake fama dashi sai Manzon Allah (S.a.w) yace dani (Ina kake da Ãyatush Shifa'i) ma'ana (ya baka Karanta masa Ãyaatush Shifa'i) ba? yace saina farka daga baccin sai nayi ta tunani akan Ãyatush - Shifa'i din sai naganosu a gurare shida a cikin Alqur'ani, sai yace: Saina tattarasu na rubucesu a falle 1 sai na karantasu sau wani adadi da niyyan neman waraka kawai sai yakasance waraka da izinin Allah mabuwayi"

👉🏼 GASU KAMAR HAKA:

1: Suratul Fatiha

2: Suratu Tauba aya ta (14)

3: Suratu Yunus aya ta (57)

4: Suratun Nahli aya ta (69)

5: Suratul isra'i aya ta (82)

6: Suratush Shu'ara'i aya ta (80)

7: Suratu Fussilat aya ta (44).

👉🏼 YADDA ZA'A KARANTASU

Da farko mutum zai samu Ruwa dai dayin buqatarsa musamman ma (Ruwan zam-zam) sai ya Karanta wadannan Ayoyin aciki yana mai tofawa, ko kuma ya kusanto da abinda Ruwan keciki dab da bakinsa sai ya Karantasu tare da kyakkyawar niyya,

👉🏼 YADDA ZA'AYI AMFANI DASHI

➡️ Mutum zai Sha Kuma yashafe Dukkannin jikinsa da Ruwan, Safe da Dare kafin a kwanta, zai sha da Safe kafin yaci koma.

➡️ Sa'anan za'a iya shafawa a ga6o6i dasuke ciwo tare dayin Bismillah.

👉🏼 FA'IDOJINSA

Haqiqa Karanta wadannan Ayoyin masu Albarka nada Fa'idoji dayawa ga kadan daga ciki:

1️⃣: Yana warkar da cutanda aka kasa gane masa .

2️⃣: Yana Kore Aljani daga jiki.

3️⃣: Yana lalata duk wani cuta da Aljani yasa a jikin Mutum.

4️⃣: Yana warkar da Cututtukan Zuciya.

5️⃣: Yana warkar Cututtukan gangan Jiki .

6️⃣: Yana lalata SIHIRI a jikin Mutum.

7️⃣: Yana warkar da matsalar Waswasi, ds

👉🏼 Duk wannan yana Ta'asirine da izinin Allah, sa'anan dakuma Emanin mutum da ikhlaainsa.

👉🏼TAJRIBA

💯 Babu shakka ni bazan iya sanin adadin mutane dana yimusu ko s**ayi da kansu ko akayi musu s**a samu dacewaba.

🤲🏼 Yaa Allah kayimana muwaafaqa Duniya da Lahira.

@ ABUU IKRIMA

👉🏼 Daga Zauren Abuu ikrima na
(العلاج با القرأن والسنة)
WHATSAP

👉🏼 Don Karin bayani ko Tambaya
(07061933096) ☎️

26/12/2023

Assalamu alaikum warahmatullah

Yan'uwa dake wannan Zaure namu mai Albarka ina mai yimuku fatan Alkhairi tare da Ahalinku.

In shaa Allahu Anjima da Dare zan kawo mana bayani gameda (Ãyaatush Shifa'i) ma'ana Ayoyin Waraqa

Allah yayimana Muwaafaqah

@ Abuu ikrima

27/11/2023

✍🏼✍🏼 ✍🏼✍🏼 ✍🏼✍🏼

MAFI GIRMAN RIGAKAFI DA KUMA KORAN SHARRI DAKE TARE DA MUTUM A RAYUWARSA.

Assalamu alaikum
Warahmatullah

Yan'uwa barkanku da warhaka da fatan Kuna cikin Aminci da qoshin lafiya tare da dukkanin Ahalinku Allah yasa haka.

Ina mai farincikin sanardaku wannan RIGAKAFI mai matuqar Ta'asiri na ban Al'ajabi a rayuwar musulmi

1: Karanta Suratul FATIHA sau 7

2: Karanta AYATUL KURSIYYI sau 7

3: Karanta Suratul KAFIRUN sau 7

4: Karanta suratul IKHLAS sau 7

5: Karanta Suratul FALAQ sau 7

6: Karanta Suratun NAS sau 7

👉🏼 YADDA ZA'A KARANTASU

Da farko mutum zai samu Ruwa dai dayin buqatarsa sai ya Karanta wadannan Surorin aciki yana mai tofawa, ko kuma ya kusanto da abinda Ruwan keciki dab da bakinsa sai ya Karanta Surorin, kowanne tare da A'uziya da Bismillah,

👉🏼 YADDA ZA'AYI AMFANI DASHI

➡️ Mutum zai Sha Kuma yashafe Dukkannin jikinsa da Ruwan, Safe da Dare kafin a kwanta.

➡️ Sa'anan za'a iya yayyafawa a cikin Daki tare dayin Bismillah domin samun Aminci.

👉🏼 FA'IDOJINSA

Haqiqa Karanta wadannan Surori masu Albarka nada Fa'idoji dayawa ga kadan daga ciki:

1️⃣: Riga kafine daga dukkan Sharri.

2️⃣: Yana Kore Ajani nan take da jikin Mutum.

3️⃣: Yana qona duk wani Cuta da Aljani yasa a jikin Mutum.

4️⃣: Yana Sauqar da Zazza6i duk qarfinsa.

5️⃣: Yana sanyaya jiki duk Zafinda yayi.

6️⃣: Yana bayyana SIHIRI a jikin Mutum.

7️⃣: Yana Sanya mutum cikin nishadi da jindadi rayuwarsa.

8️⃣: Yana qarawa mutum Lafiya da Kuzari wurin ayyukan Alkhairi.

9️⃣: Yana toshe mashigar Aljani a jikin mutum. ds

👉🏼 Duk wannan yana Ta'asirine da izinin Allah, sa'anan dakuma Emanin mutum.

👉🏼TAJRIBA

💯 Babu shakka ni bazan iya sanin adadin mutane danyimusu ko s**ayi da kansu s**a samu dacewaba.

🤲🏼 Yaa Allah kayimana muwaafaqa ka bamu lafiya kasa adace.

@ ABUU IKRIMA

👉🏼 Daga Zauren Abuu ikrima na
(الشفاء با القرأن والسنة)
WHATSAP

👉🏼 Don Karin bayani ko Tambaya
(07061933096) ☎️

26/11/2023

✍🏼✍🏼 ✍🏼✍🏼 ✍🏼✍🏼

GAMEDA MASU FAMA DA MATSALAR ULSER (olsa) GASTRIC

ASSALAMU ALAIKUM
WARAHMATULLAH

ALHAMDULILLAH

To yan'uw gameda wannan matsalar sai a nemi wadannan itatuwa masu Albarka don samun waraqa in shaa Allah.

1: Ingantaccen GARIN ZAITUN

2: Ingantaccen GARIN HABBATUSSAUDA

3: Ingantaccen ZUMA Wanda ba miss

4: lngantaccen MA'UL WARDI

👉🏼 YADDA ZA'A HADASU

Da farko bayan an samu ZUMA Kofi 1 sai azuba HABBA cokali 4 a garwayashi sosai sa'anan a zuba ZAITUN shima cokali 4 tare da WARDI marfi 2 sai a garwaya sosai za'aga yayi kyau har yana sheqi ga kamshin WARDI na tashi.

👉🏼 YADDA ZA'A SHA

Yadda mai fama da jinyar ULSER (olsa) zaisha hadin wannan magani mai Albarka shine,

Da Safe kafin mutum yaci komai (karya) zaisha cokali 2 sai kuma da Dare bayan ya gama cin komai yazo kwanciya yasha cokali 2, babu shakka wannan hadin nada matuqar Ta'asiri da izinin Allah game da matsalar ULSER (olsa) musamman ma irin Ulser (olsa) dake sanya Quna, Radadi a Qirji da rage karfin Numfashi mutum yake numfashi sama sama, tashin zuciya, Amai (hararwa) tsananin ciwon Ciki, yawan sa yinwa, ramar da mutum, ds.

👉🏼 TAJIRIBA

✔️ Babu shakka na hadawa mutane da dama wannan hadin Kuma cikin ikon Allah da Amincewarsa sun samu Lafiya,

💯 Akwai Wanda yayi shekara 6 baya AZUMI Amma cikin ikon Allah dayayi anfani da wannan hadin yanzu har Azumin litin da Alhamis yakeyi,

💯 Akwai wadanda s**a kawo mahaifiyarsu tajima tana fama Amma datayi amfani da wannan hadin cikin Amincewar Allah yanzu ta warke tana komai.

💯 Akwai wasu Samari biyu Wanda s**ayi fama sosai Amma yanzun cikin Amincewar Allah sunwarke sunkoma sana'arsu.

🙏🏻 GODIYA TA TABBATA GA ALLAH

🤲🏼 Yaa Allah kayimana muwaafaqa ka bamu lafiya kasa adace.

@ ABUU IKRIMA

👉🏼 Daga Zauren Abuu ikrima na
(الشفاء با القرأن والسنة)
WHATSAP

👉🏼 Don Karin bayani ko Tambaya
(07061933096) ☎️

Address

Jalo Waziri Street
Gombe
112

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abuu ikrima العلاج با القرآن والسنة posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Abuu ikrima العلاج با القرآن والسنة:

Share

Category