06/01/2026
"SHAHARA" TSAKANIN AMFANI DA CUTARWA.
Kalmar “shahara” na nufin yin fice ko yin suna a cikin al'umma, wato mutum ko wani abu ya yi fice har kowa ya san shi ko ya yarda da shi. Wannan hali yana da amfaninsa da kuma sharrinsa, kamar yadda za mu bayyana .
✅ Amfanin Shahara (Fa'idodi)
1. Saukaka Isar da Saƙo
Idan mutum ya shahara, yana da sauƙin jawo hankalin jama'a, musamman idan yana da kyakkyawar manufa kamar wa'azi, ilimantarwa ko gyaran al'umma.
2. Zama Misali Ga Wasu.
Mashahuri na iya zama abin koyi ga matasa da sauran jama'a idan yana da kyawawan ɗabi'u da hali nagari.
3. Samu Girmamawa da yawa.
Mashahuri na iya samun girmamawa daga jama'a da kuma dama a gurare da yawa kamar shugabanci, kasuwanci, ko harkokin al'umma.
4. Tasiri Wajen Canza Rayuwar Wasu
Mutane masu suna suna da ikon canza tunani da halayen jama'a saboda tasirinsu, kamar yadda ake gani a wajen malamai, shugabanni, da mawaka masu tunani.
❌ Sharrin Shahara (Illoli)
1. Kiburi da Girman Kai.
Wasu mutane na fara ɗaukaka za su daina ganin girman Allah da darajarta mutane , sakamakon shahara.sai alfahari da riya da rena jama'a da wulaƙanta mutane.
2. Hasada da Kiyayya
Mashahuri kan fuskanci hassada da kiyayya daga wasu da ba su son ganin ci gabansa.
3. Kaucewa daga Hanyar Gaskiya
A wasu lokuta mashahuri yafi yin aiki don jin daɗin jama'a, ba don Allah ba, kuma ya bar gaskiya domin tsoron ya rasa farin jini.
4. Tsananin Jarabawa da Fitina
Shahara na jawo nau'o’in jarabawa iri-iri: kamar alfahari ,shaye-shaye, zinace-zinace, cin haram, da barin ibada saboda shagaltuwa da duniya.
5. Sauƙin ƙatare Iyakoki.
Mutane masu suna na iya tsallake iyakokin addini ko al’ada saboda suna ganin su “ba kamar kowa ba ne.”
Shahara ni’ima ce idan aka yi amfani da ita wajen inganta rayuwa da gyaran al’umma. Amma tana iya zama fitina mai girma idan aka yi sakaci da ita. Saboda haka, masu suna su ji tsoron Allah, su kasance da tawali’u, su rike gaskiya kuma su guji alfahari da yawan magana.
Allah ka tsare mana iman