Ukashatu Yusuf

Ukashatu Yusuf Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ukashatu Yusuf, Farmers market, Kaduna ikara LGA danlawal kofar fada, Ikara.

15/10/2024
15/10/2024

Send a message to learn more

15/10/2024

SUFANCI JIGO NE A MATAFIYAR AHLI-SUNNAH, TIJJANIYYA MADAFACE MAI GIRMA.

Ahlu-Sunnah na da matafiyai kamar:-
1- Matafiyar Kira'a (Hafs, Nafi, Warsh da sauransu).
2- Matafiyar Hadisi (Bukhari, Muslim) da sauransu,
3- Matafiyar Ilmin Tauhidi (Asha'ira, Muturidiyya, Asariyya) da sauransu,
4- Akwai matafiyar Tafsiri (Jalalayni, Ibn Kasir) da sauransu,
5- Akwai matafiyar Mazhabobin Fikihu kamar (Malikiyya, Shafi'iyya, Hanafiyya, Hambaliyya da sauransu)
6- Sai matafiyar gyaran zuciya kamar (Kadiriyya, Sunusiyya, Tijjaniyya) da sauransu.

Duk wanda a yau, zai ware matafiyar Sufanci kamar Darikar Tijjaniyya yace da kai wani sabon Addini ne bayan MANZON ALLAH (S.A.W), to babu shakka a cikin wadanda ya dace a tausayawa shi ne sahun farko, domin kwata-kwata bai ma san me Musuluncin ba, b***e aje ga batun gidan da yake tutiya zuwa gareshi, wato "Sunnah".

Idan kuwa so yake ya nuna duk wata matafiya a kowanne fanni na addini da ta samu bayan MANZON ALLAH (S.A.W) sabon al'amari ne, to lallai ba ga Darikar Tijjaniyya kadai ya dace ya fito ya bayyana bara'a ba, face har da Matafiyai na sauran ababen da s**a shafi Musulunci, kamar Matafiyar Tauhidi (Maturidiyya) Hadisi (Bukhari), Fikihu (Malikiyya), Kira'a (Hafs)da sauransu, domin su ma wasu ne s**a zo da su bayan MANZON ALLAH (S.A.W).

Idan nasabta wani tafarki zuwa ga jagoran tafarkin ha kan na nuni izuwa ga tafarkin kagaggen tafarki ne bayan abinda ANNABI (S.A.W) yazo da shi, to a nan kuma Kalubalen kwachokam a kan ku zai kare, domin ku ne kuka kirkiri tafarki mafi sharri ga kalubalantar tafarkin MANZON ALLAH (S.A.W) har kuke ayyanawa duk Musulmin da bai kasance tare da tafarkinku ba, to sunansa ka'fi'ri, Mushriki ko kuma Dan Bidi'ah.

GASKIYAR AL'AMARI.

Ita kowacce matafiya ba da sunan da ake kiranta ko lakabinta ake mata hukunci ba, face ababen da s**a tattaru s**a ginata, dukkanin ababen da s**a tattaru s**a gina Darikar Tijjaniyya ababene da s**a zo cikin fadin ALLAH da kuma na MANZON ALLAH (S.A.W), wanda ke da ja a kan haka, sai ya bayyana inda yake da inkari domin a bashi amsa.

SABODA HAKA, IDAN MUTANE BASU DA MASANIYA A KAN ABU, TO SU DAI NA YANKE HUKUNCI CIKIN JAHILCI ZUWA GA JAHILAI YAN UWANSU, TAMBAYA YA DACE SUKE YI KO ZASU SAMU KARIN HASKE.

ALLAH YA GANAR KUMA YA SHIRYA.

Muhammad Usman Gashua ✍️

Address

Kaduna Ikara LGA Danlawal Kofar Fada
Ikara

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ukashatu Yusuf posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category