20/04/2024
DAGA CIKIN ILLAR MADIGO A TAKAICE….
Manzon Allah (SAW) a Hadisin Ibn Abbas (RA) a lokacin da yake jero wadanda Allah ya tsine masu, harda ‘yan Luwadi’, Allah ya tsine ma duk masu aikin (luwadi), irin aikin da mutanen Annabi Lut s**a yi, Wallahi wanan tsinuwa ta shafi hadda yan madigo.
Karka/ karki yarda ku shiga cikin wannan tsinuwar ta Allah da tsinuwar Manzonsa, mala’ikunsa da mutanan kirki, domin babu asara ga dan adam k**ar ace Allah da Mazonsa sun tsine masa, lallai asara takai asara, Allah ya kiyaye mu.
Ta fannin zamantakewa da kiwon lafiya kuwa, akwai illoli masu yawa da madigo da luwadi ke haifarwa a jikin ma’abocinsu k**ar haka:
1. Suna kawar da sha’awar aure baki daya, domin a addinance da kuma al’adance akan daura aure ne tsakanin mace da namiji, To macen da take madigo zata kasance bata sha’awar namiji baki daya, ko tayi auren, tayi ne kawai, amma ba zata yi sha’awar mijin ba.
2. Ba zata sami biyan bukata a kwanciyar aure ba. Shi kuma jima’i a tsakanin ma’aurata, yana kara gina so da kauna a tsakanin juna, Koda an sadu da ita, to ba zata ji sha’awarta ta gushe ba har sai ta hadu da ‘yar uwarta mace sun goga da juna, Shi yasa kake ganin hatta daga cikin matan aure masu irin wanan mummunan aikin, suna aikata wannan mummunar dabi’ar, ko da kuwa suna gidan mijinsu.
3. Madigo na haifar da yaduwar ciwon sanyi. a duk lokacin da wadda take dauke da ciwon sanyi tayi tarayya da wadda bata da shi, to anan zata harba mata shi, domin wannan discharge din yana dauke da kwayoyin cuta da zasu yadu har ya shafe ta.
4. Madigo yana haifar da cututtukan da ke sa kaikayi ga farjin mace, idan mai kaikayin mara ko kuraje a cikin farji ko zubar farin ruwa, sanadiyyar wani infection, k**ar na vulvo vaginal candidiasis, yeast infection, da sauran su, idan s**a yi gogayya da juna, to zata dauki wannan ciwon, cikin sauqi.
5. Madigo yana haifar da yaduwar cutar Kanjamau/Sida (wato AIDS). Kuma ban ga yadda za’a kare wannan kwayar cutar ba, domin takan biyo ruwan dake fitowa a gaban mace ta shafi ‘yar uwarta, kuma ba za’a iya yin amfani da condom ba, kuma ma bincike ya nuna cewa Condom ba ta iya kare komai. Kawai magani shine, aji tsoron Allah a daina (Abstinence).
6. Madigo yana haifar da ciwon mara – Dama, su mata sun fi kowa yawan ciwon mara, wasu ma da shi aka haife su, wasu kuma a lokacin al’ada yake zo masu, wasu kuma daga baya s**a dauko shi a wani wuri (infections). Gogayyar da suke yi gaba-da-gaba da juna na haifar da kamuwa da ciwon mara, musamman na infections. Ayi ta faman neman magani a rasa sanin dalili.
7. Madigo yana haifar da ciwon ruhi (spiritual problems) – A nan, shi ciwon ruhi ba fa ciwo bane da zaki gani a zahiri, amma a hakika zaki ji alamunsa a gangar jikin ki. Na farko dai zai busar da zuciyar ki, sai ya kasance baki shakku ko tinanin zaki iya mutuwa a kowane lokaci. Sha’awarki zata gushe ta koma ga ‘yan mata kawai. Da zaran kin ga mace mai girman kirji ko mai manyan mazaunai duk sai sha’awarta ta k**a ki. Sannan komai nisan ki da ita zaki iya neman ta. Har ki tsufa zaki kasance kina ganin sha’awar mata ‘yan uwanki.
8. Zai janyo maki gushewar farin jini a fuskar maza, sai kiga duk masoyanki mata ne, gaki kyakkyawa amma ba mai so, basirar ki tabi ta dushe, tunanin ki ya sauya. Wata rana sai ki kasa daina wa. Kuma zuwa gaba sai ya busar da ke, ki rinka ramewa, duk ni’imar jikin ki ta mace, ta gushe, kibi ki bushe, kiyi matukar muni. Kuma a lokacin sai kiyi dana-sani, a lokacin da dana-sanin ba zai amfane ki ba! Allah ya shirye mu baki daya.
Dr Sumayya Ibrahim Sa'ad Shin akwai kuskure cikin wanan bayani domin kuna daya daga cikin masana harkar lafiya ta dan Adam, hakika zan so mu qara samun haske cikin comment section.
Muhammad Ubale Kiru, Ina fatan zaka qara wayar mana da kai dan gane da wanan al’amari duk da cewar nasan kana iya bakin qoqarinka.
Abdussamad Tijjani Sani✍️