Hanyar Garin malam mudi

Hanyar Garin malam mudi Wannan kafar an samar da ita ne domin isar da sakon harka Islamiyya dama duniya baki daya.

07/11/2025
๐’๐ก๐ข๐ง ๐ƒ๐ฎ๐ค ๐–๐š๐ง๐๐š ๐˜๐š ๐Œ๐š๐ฅ๐ฅ๐š๐ค๐ข ๐–๐š๐ฒ๐š๐ซ ๐€๐๐ซ๐ข๐จ๐ ๐’๐ก๐ข ๐Š๐ž ๐๐š๐ง ๐˜๐š ๐™๐š๐ฆ๐š ฦŠ๐š๐ง ๐Œ๐ž๐๐ข๐š (ฦŠ๐š๐ง ๐‰๐š๐ซ๐ข๐๐š) ๐๐š ๐‡๐š๐ซ๐ค๐š๐ซ ๐Œ๐ฎ๐ฌ๐ฎ๐ฅ๐ฎ๐ง๐œ๐ข ....โ“๐€๐ฆ๐ฌ๐š ๐€'A โŒ.  T...
05/11/2025

๐’๐ก๐ข๐ง ๐ƒ๐ฎ๐ค ๐–๐š๐ง๐๐š ๐˜๐š ๐Œ๐š๐ฅ๐ฅ๐š๐ค๐ข ๐–๐š๐ฒ๐š๐ซ ๐€๐๐ซ๐ข๐จ๐ ๐’๐ก๐ข ๐Š๐ž ๐๐š๐ง ๐˜๐š ๐™๐š๐ฆ๐š ฦŠ๐š๐ง ๐Œ๐ž๐๐ข๐š (ฦŠ๐š๐ง ๐‰๐š๐ซ๐ข๐๐š) ๐๐š ๐‡๐š๐ซ๐ค๐š๐ซ ๐Œ๐ฎ๐ฌ๐ฎ๐ฅ๐ฎ๐ง๐œ๐ข ....โ“

๐€๐ฆ๐ฌ๐š ๐€'A โŒ. Tabbas a'a ba ษ—an Media bane, ba mallakar babban waya ke mayarda Mutum ษ—an Media ba. Ita Media Forum wata ษ“angare ce na Harkar Musulunci, wato wata Forum ce a cikin Forums ษ—in dake cikin Harkar Musulunci.

Su kuma mutanen da ke cikin wannan forum ษ—in, mutane ne da suka ษ—aukarwa kansu, isar da sakon Harka ta kafafen sadarwa, tsakanin Hoto mai motsi da mare motsi, tsakanin Rubutu da kuma sakon Sauti (Audio). Bisa wannan mutanen dake cikin wannan Forum ษ—in , sukan koyar da kansu yanda ake wannan aikin, a ilmance a kuma zamanance, sukan samar da tsarukan karatu ga membobinsu, domin koyar da su sanin ฦ™a'idojin yanda ake aikin, sukan shiryawa kawukansu taron karawa juna sani, inda ake horar da ma'aikata yanda za suyi aikin a zahirance (Pratical). Bayan duk wannan sannan sai ace to yanzu kuna iya fara aikin isar da sakon.

Bisa wannan yakan zama ฦดan media Forum sukan san kawukansu , kowa kuma yakan san cewa a media aikin shi ka za ne, wato wani aikin shi ษ—aukar Hoto ne, wani Rubutu, wani ษ—aukar Audio, wani ษ—aukar Bidiyo, don haka sanda suka baiyana a wuri kowa sai kaga ya kama aikin da ke gabanshi.

๐Œ๐ž๐ง๐ž๐ง๐ž ๐๐š๐ง๐›๐š๐ง๐œ๐ข๐ง ฦŠ๐š๐ง ๐Œ๐ž๐๐ข๐š ๐…๐จ๐ซ๐ฎ๐ฆ ๐ƒ๐š ๐Š๐ฎ๐ฆ๐š ๐Œ๐š๐ฌ๐ฎ ๐’๐ข๐ฒ๐š ๐–๐š๐ฒ๐š ๐’๐ฎ ๐Š๐ข๐ซ๐š ๐Š๐š๐ง๐ฌ๐ฎ ๐˜๐š๐ง ๐Œ๐ž๐๐ข๐š

1. Duk waษ—ancen abubuwan da muka zaiyano, da yan Media Forum kema wakilansu, shifa wanda yasai Adriod ya mayar da kanshi ษ—an Media, baida wanda yamai su, baima sansu ba sam.

2. Wanda yasai Adriod ya mayar da kanshi ษ—an Media, baisan wani Hoto ya kamata a yaษ—a ba wanne ne ba a yaษ—awa. Shi kuma ษ—an Media Forum ya sansu

3. Wanda yasai Adriod ya mayar da kanshi ษ—an Media, shi ne wanda a rubutu ya ke nuna ษ“angaranci ฦ™arara, shi ko ษ—an Media Forum yasan cewa a ฦ™a'idar aikin Jarida babu ษ“angaranci

4. Wanda yasai Adriod ya mayar da kanshi ษ—an Media, shi ne wanda ya ke tunanin cewa yana da gwani, don haka zaiyi ta posting yana zagin wanda ba gwanin shi ba, a lokaci guda kuma yana kare gwaninshi . Shi ko ษ—an Media Forum yasan cewa a aikin Jarida babu zagin wani don kun saษ“a ra'ayi, inma kana da gwani baka bari masu karatunka su iya gane hakan.

Banbancin suna da yawa kwarai, amman nasan ko iya nan na tsaya, mai karatu ya fahimta inda na dosa.

๐’๐ก๐ข๐ง ๐™๐š๐ข ๐˜๐ฎ๐ฒ๐ฎ ๐Œ๐š๐ฌ๐ฎ ๐’๐ก๐š'๐š๐ฐ๐š๐ซ ๐€๐ข๐ค๐ข๐ง ๐Œ๐ž๐๐ข๐š ๐’๐ฎ ๐’๐š๐ฆ๐ฎ ๐†๐ฎ๐ซ๐›๐ข ๐€ ๐Œ๐ž๐๐ข๐š ๐…๐จ๐ซ๐ฎ๐ฆ...โ“

Amsa kwarai kuwa zai yuyu โœ… , abinda kake buฦ™atar yi kawai shi ne, a duk inda kake ka samu yan Media Forum na yankinku , ka gwada musu shi'awar ka da tafiyar, su kuma zasu faษ—a maka tsarukan tafiyar da ฦ™a'idojinta .

Bissalam

Rubutawa:- Ali Ibrahim Yareema .. โœ๏ธ
05112025

"Kar ku yarda a  hada Ku rigima da juna koda da wani Irin abu za'a kira rigimar,Ko da Sunan Addini Ko da Sunan Qabila ku...
04/11/2025

"Kar ku yarda a hada Ku rigima da juna koda da wani Irin abu za'a kira rigimar,
Ko da Sunan Addini Ko da Sunan Qabila ku haษ—e Kai ku zauna Lafiya.

Kiristoci ba Sunan Su Arna ba, Sunan da Allah ya ambace su a Qur'ani Ma'abotan littafi."-Jagora (H) yayin da yake masu bayanin muhimmancin zaman lafiya.





13/Jimada ula/1447
04/11/2025

GAYYATA ZUWA TARON  MAKON IMAM ALI (AS) Dandalin Matasan Harkar Musulunci ฦ™arฦ™ashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaqub Zak...
04/11/2025

GAYYATA ZUWA TARON MAKON IMAM ALI (AS)

Dandalin Matasan Harkar Musulunci ฦ™arฦ™ashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaqub Zakzaky (H) na farin cikin gayyatar ษ—aukacin Matasan Harka Islamiyya zuwa taron "Makon Imam Ali (AS)" karo na biyu, tare da Muโ€™utamar โ€œAmmโ€ wanda suka saba shiryawa karo na 37.

Wannan karon, taron zai gudana ne tsawon mako guda, inda aka zo da sabbin tsare-tsare waษ—anda suka haษ—a da: karatuttuka, tattaunawa, wasanni, kyautata muโ€™amala tsakanin โ€˜yan uwa, da sauransu.

Akwai manyan malamai gami da masana da zasu gabatar da jawabai da tattaunawa akan mauduโ€™ai daban-daban da suka shafi ci gaban matashi a mahangar Harka Islamiyya.

Taken Taron:
โ€œGina Shaksiyyar Matashi ฦŠan Gwagwarmaya Tare da Kusanto da ฦณaฦดan โ€˜Yan Uwa Zuwa ga Harka Islamiyya.โ€

Tsarin Taron:
๐Ÿ—“ Rana: Lahadi 7 ga watan Rajab zuwa Jumaโ€™a 13 ga watan Rajab
๐Ÿ“… Daidai da: 27 ga December zuwa 02 ga January, 2026.

Gari: Abuja

Kuษ—in Rajista:
๐Ÿ‘ฌ Brothers & Sisters: โ‚ฆ5,000 (Naira Dubu Biyar)

Za a rufe rajista a ranar 18 ga watan December (27 ga Jimada Thani), kwanaki goma kafin fara taron.
Ana roฦ™on duk wanda zai halarta da ya kammala rajistar sa kafin wannan lokaci.

Mun fitar da Google Form domin fara "Online Registration."
๐Ÿ“ฑ๐Ÿ“Ž
https://forms.gle/4a5SU1B63pjiJ3Ny6

Domin tuntuษ“a: 08140748841, 08179589825, 09061411874, 07035266571, 08035333179, 08083940490.

Sanarwa:
Youth Forum Media Team
0 2 โ€” 1 1 โ€” 2 0 2 5.

ุฃุนุธู… ุงู„ู„ู‡ ุฃุฌูˆุฑู†ุง ูˆุฃุฌูˆุฑูƒู… ุจู…ุตุงุจู†ุง ุจุดู‡ุงุฏุฉ ุณูŠุฏุฉ ู†ุณุงุก ุงู„ุนุงู„ู…ูŠู† ุณู„ุงู… ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ุง
04/11/2025

ุฃุนุธู… ุงู„ู„ู‡ ุฃุฌูˆุฑู†ุง ูˆุฃุฌูˆุฑูƒู… ุจู…ุตุงุจู†ุง ุจุดู‡ุงุฏุฉ ุณูŠุฏุฉ ู†ุณุงุก ุงู„ุนุงู„ู…ูŠู† ุณู„ุงู… ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ุง

Wani Mutumi Ya ce Baya Tsoron Amerika Ta Kawo Hari Najeriya, Domin Akwai El-Zakzaky A Cikin ta, Kuma Yasan Kasar IRAN Ba...
02/11/2025

Wani Mutumi Ya ce Baya Tsoron Amerika Ta Kawo Hari Najeriya, Domin Akwai El-Zakzaky A Cikin ta, Kuma Yasan Kasar IRAN Ba Za Ta Bari A Kashe Mata Zakzaky Ba.

SAVE THE DATE 15/RAJAB/1447 MUNA DA GAGARUMIN BIKI!!!Muna farin cikin gayyarku zuwa wajen daurin auren ฦŠan uwa Abdurrahm...
29/10/2025

SAVE THE DATE 15/RAJAB/1447 MUNA DA GAGARUMIN BIKI!!!

Muna farin cikin gayyarku zuwa wajen daurin auren ฦŠan uwa Abdurrahman zakariyya Kidandan tare da amaryarsa Amina Ml.Shafiu Gumau Bauchi.

Wanda zai gudana a ranar 15/Rajab a garin Gumau Bauchi State.

Allah yabada Ikon halarta Ameen.

Sako daga Abdurrahman zakariyya Kidandan

malam Mudi press
29/10/25

26/10/2025
Gwarzo:Sallamawa Jagora irin na su Shahid Muhammad Turi, abu ne da tarihi ba zai taba mantawa da shi ba, kuma zai tabbat...
22/10/2025

Gwarzo:

Sallamawa Jagora irin na su Shahid Muhammad Turi, abu ne da tarihi ba zai taba mantawa da shi ba, kuma zai tabbata a matsayin ramzi na sadaukarwa ga dukkan 'yan gwagwarmaya har ฦ™arshen duniya.

Mun ji abubuwa da yawa a wajen su Jagora (H) dangane da Shaikh Turi (RH), da irin shauฦ™insa ga Shahada, wanda duk sadda Jagora suka yi bayani akan falalar Shahidi, suka ce, Shaikh kan yi iyakan kokarin sai ya nemo Hadisin don ya kiyaye shi. Kila a kokarinsa na samun ฦ™warin guiwan dakewa a yayin jarabawa.

Shahid ya taba rokon ai masa addu'ar ya samu Shahada a wajen wani bawan Allah, a gaban su Jagora (H), wanda har sai da su Jagora suka ji ina ma bai roki wannan addu'ar a irin wannan wajen ba.

Lokaci na ฦ™arshe shi ne Waki'ar Buhari ta 2015, wanda tare da Shaikh sun yi waya da Jagora (H) ya tuntubi me ya kamata a yi, an ba da Irshadin ko da Muzaharori aka yi a garuruwa ya wadatar. A babin biyayya ga su Jagora (H), Shaikh (RH) ya fita Muzaharar a garin Kano, har an hasko shi a hoto a sahun Muzaharar tare da ba'adin 'yan uwa, karfe 12:00 da wani abu na dare ana kan yi, ya zabi lallai ya kama hanyar Zaria don ya je ya sauke wazifarsa.

Su Jagora (H) kansu sun yi mamaki a sadda Malam Qasim ya kira su yace musu, ga Malam Turi nan ya zo Gyallesu, kuma ya nufi inda sojoji ke harbi a wajejen karfe 2:30 na dare. Su Jagora suka ce, ace masa ya dawo.

Ina daga wadanda suka tare Shaikh, akan lallai ya yi hakuri ya koma, tun kafin zuwan Shahid Qasim don isar da wannan sakon. Amma Shaikh yace, ku kyale ni, zan je ne in gaisa da 'yan uwa da ke can gaba suna ta kokarin a madadinmu, gashi suna ta yin Shahada, za mu je mu nemi albarkarsu. Wani dan uwa (ana kiransa da Tall Man) yana ce masa, Akramakallah yanzu dare ne, da ace da rana ne da za mu bari ka yi hakan, sai ga Shaikh Qasim ya zo, ya ce masa, su Malam sun ce a dawo....

Da Asubah, Jagora (H) ya fito an yi Sallah tare da ba'adin 'yan uwa a cikin gida. Bayan an idar, a yayin da sojoji na kan harbe-harbe a unguwar a kokarinsu na kutsowa gidan Jagora, kafin shigan Jagora cikin gida daga wajen da suka bayar da sallah, sai da ya ce wa Shaikh; Malam Turi, na ji an ce ka nufi inda sojoji suke harbi dazu, na san kana son Shahada ne, in lokacinta ya zo, za a yi. Amsar da Shahid (RH) ya baiwa Jagora ta sa Jagora ya dauki darduma ya shiga gida ba tare da ya kara cewa komai ba. Yace masa: "Nafsi bi nafsikumul fidha" Wato: โ€œRayuwata ta zama fansa ga rayuwarku.โ€

Lahaula wala quwwata illa billah. ๐Ÿ˜ข

Daga sallar nan ne Shaikh ya fito daga gidan Jagora (H) ya kasance mai ฦ™arfafawa ga 'yan uwan da suke kokarin bayar da kariya, har ma in ya ga wani zai sare, sai ya masa nasiha akan cewa, dan uwa, yau ba ranar kuka ba ne, ranar cikawa Allah alkawari ne. "Ba mun ce da jini da ruhi za mu fanshi ran su Malam (H) ba? To yau ranar wannan ne. In kuma jarabawa ta yi nauyin da ba za a jure ba, har yanzu akwai hanyar fita ta bayan makabartan nan, don kar a raunata wadanda suke kokari" Haka Shaikh ya fada wa wani dan uwa da yaga ya fashe da kuka saboda yadda ya ga ana fasa kwakwalen 'yan uwa da jikkunansu da harsasan soji. Sai kuwa wannan dan uwan ya share hawaye, take ya hakura, ya koma yana farfasa duwatsu. Allah masani, ba mamaki shi ma ya yi Shahada.

Har soji ya zo bakin gidan Jagora ta wajen kofar gida, Shaikh Turi na tsaye kyam a gaban gidan, zuwa lokacin da suka seta shi suka harbe shi ya fadi a ฦ™asa.... Aka dauke shi aka shigar da shi cikin gidan Jagora cikin jini, yana abin zalunta, mai sadaukarwa, Shahidi, ma'abocin cika alkawari ga Allah Ta'ala.

Ba za ka san wane ne Shaikh Turi ba, sai ka tambayi matarsa Malama Maimuna akan karamcinsa ga iyalansa a babin zamantakewa. Ko ka tambayi 'ya'yansa mata shida masu albarka, da Allah Ta'ala Ya azurta shi da su, wanda ya ba su tarbiyar addini, da ilimi, ya tafi ya bar su a cikin albarkar. Ko ka tambayi makwaftansa, ba kawai wadanda suka hada katanga guda ba, har mutanen garin Kano bakidaya, wane ne Shaikh Turi? Ciki kuwa har da mahukunta, da suka masa shaidar cewa ba su taba masa tayin abin hannu ko da wane irin salo ya amsa ba. Baka batun gidajen Malaman Kano, ko ma'abota Allah, Shurafa, karamcinsa gare su baya ฦ™afewa har yau.

Shaikh karimi ne da dukkan ma'anar karamci, ma'abocin haiba da kwarjini ne kwarai, jarumi ne, sadauki, muklisi. Wajen koyi, yana kokarin sanya kafarsa a inda Jagora (H) suka daga ne. Shi yasa Sisters din Kano suka zama 'yan gatan Shaikh, saboda koyi da yadda Jagora (H) ke kokarin sauke hakkoki da bayyana 'yancin mata a aikace.

Yana wahala in yi hira da wani mutum, musamman 'yan uwa na Kano akan Shaikh Turi a yanzu, har mu kammala hirar ba tare da mai maganar ya fara hawaye ko ya fashe da kuka ba. Abin mamaki, ina rubutun nan kwalla na fitowa daga idanuna, zuciya na bugawa da sauri fiye da sadda na fara yi.

Allah Ta'ala Ya girmama ladan Shaikh (RH), Ya girmama matsayinsu. Ya tsinewa makasansu albarka. Ya kuma bamu itasu, albarkacin Annabi da Ahlulbaiti (AS).

โ€” Saifullahi M. Kabir



27 ga Rabi'ul Thani 1447 (20/10/2025)

Daga Garin Kidandan An Gudanar Da  Muzaharar Mauludin Manzon Allah (S).Jiya  Talata, 23/Sep/2025 Daidai, 30-Rabi'ul Awwa...
24/09/2025

Daga Garin Kidandan An Gudanar Da Muzaharar Mauludin Manzon Allah (S).

Jiya Talata, 23/Sep/2025 Daidai, 30-Rabi'ul Awwal 1447H. Daruruwan Yan'uwa Musulmai Almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) Na Garin Kidandan Da Kewaye Suka Fito Nuna Farin Cikin Su Da Zagayowar Watan Da Aka Haifi Fiyayyen Halitta Manzon Allah (S.A.W) Labari Cikin Hotuna.

Garin Malam Mudi Media

Maulud1447H
Ya Rasulullah 2025

02392025

Address

Kaduna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hanyar Garin malam mudi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category