15/04/2025
GWAMNA NAMADI YA AZA HARSASHIN GININ KATAFARIYAR CIBIYAR KULA DA LAFIYA A DUTSE.
Mai girma Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi FCA, ya jagoranci bikin aza harsashin ginin wata babbar cibiyar kula da lafiya da babu irinta a duk faɗin Najeriya. Wannan cibiyar za ta ƙunshi manyan rukunai guda uku, wato:
-Cryo-Oxygen Plant – Wurin sarrafa iskar oxygen ta hanyar cryogenic distillation.
-Cibiyar Kula da Cututtukan Zuciya (Cardiac ')
-Cibiyar Gwaje-gwaje ta zamani (Diagnostic Centre)
A ƙoƙarin da Gwamna Namadi ya ke na ciyar da fannin kiwon lafiya gaba a jihar Jigawa. Tun daga lokacin da ya hau mulki, gwamnan ya kaddamar da manyan ayyuka masu muhimmanci a fannoni da, musamman ɓangaren kiwon lafiya.
Kafin wannan aiki na yau da aka ƙaddamar, gwamnati ta inganta ƙanana asibitoci guda 181 ta hanyar samar musu da kayan aiki na zamani, na’urorin hasken rana, ruwa, da gidajen zama ga ungozoma, wanda duk ya lakume kusan naira biliyan 12.
Haka kuma, an ware biliyan 5 don gina sabon matsugunni na dindindin ga makarantar koyon aikin jinya da ungozoma da ke Hadejia, tare da kashe biliyan 1.9 a kan kwalejin koyar da fasahar jinya ta jihar da ke Jahun. Sauran kudaden da aka kashe sun haɗa da naira miliyan 386 don gyara wasu makarantun jinya da ke Birnin Kudu, Ɓabura da tsohuwar makarantar Hadejia, wanda hakan ya bai wa makarantun damar karɓar karin ɗalibai daga hukumar kula da makarantun jinya ta ƙasa da kuma fara karatun aikin ungozoma a Hadejia.
Gwamnatin jihar, a karkashin jagorancin Gwamna Namadi, ta raba gidajen sauro da magungunan zazzaɓi har guda miliyan 3.2 a faɗin jihar. Haka zalika, mutane sama da 143,500 sun amfana da shirin inshorar lafiya na J-Basic Health Care, wanda ya bai wa masu ƙaramin karfi damar samun magani kyauta. An saka naira biliyan 1 cikin wannan shirin, inda kuma gwamnati ke bayar da magani kyauta ga masu fama da cututtuka kamar hawan jini, ciwon suga, cutar hanta da kuma yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar.
Har ila yau, an bayar da kwangilar gina