03/09/2025
Salam. Aunty barka da safiya.a taimaka kimin posting aban shawara plz. Mijinmu ne ni da kishiyata duk ranar girkina gidanta yake cin abinci yayi hira sai kusan 12 na dare sai ya shigo gidana ya kwanta Kuma 8 ko 9 na safe yabar gidana ba zai sake dawowa ba sai girkina ya zagayo. ko su fita yawo sai dare amma ni baya son fita dani Koda hanyarmu daya sai dai ya bani kudi na hau motar haya.hatta kudin cefane ita yake ba ta siyo abinda take so sai dai ta dau yanda take so ta kawo min saura Koda ranar girkina ce cefanena yana saurin karewa, idan nayi magana har dukana yakeyi har hawan jini ya kamani gani da Yara 2 twins Yanzu yana so ya hademu gida 1 nace bazan iya ba saboda da bama zaune gida daya dai nasha wahala ina ga muna zaune waje 1 shine ya sakeni saki 1. Wai idan zan hakura ya hademu sai ya maida auren idan ba zanyi ba Kuma shikenan. Menene naku raayin? Kuma fa nice uwar gida