07/10/2025
📸⚽ Senne Lammens ya fara buga wasan sa na farko a Manchester United, kuma abin mamaki, ya tashi da Clean Sheet a wasan da s**a doke Sunderland!
Amma abin da ya fi daukar hankali shi ne yadda kwatsam mashahurcinsa ya tashi – daga masu bibiyarsa 10,000 a Instagram zuwa fiye da 400,000 cikin 'yan awanni kacal!
Yaron mai shekaru 21 da haihuwa ya nuna bajinta a ragar United, kuma duniya na karɓarsa da hannu bibbiyu a dandalin sada zumunta. Wannan kuwa hujja ce mai ƙarfi cewa — idan ka samu dama, ka yi amfani da ita sosai, duniya za ta gan ka.
🔥 Daga debiyu a filin wasa, zuwa shahara a Instagram — Lammens ya fara tafiya da karfi!