14/01/2025
Duk da cewa majalisar dattawa ta yi wa ƙudirin dokar karatu na biyu kafin tafiyarta hutun ƙarshen shekara, an dakatar da dukkannin wasu ayyuka kan ƙudirin sakamakon janyo hatsaniya da ya yi daga faɗin ƙasar.
An nemi shugaba ƙasa da ya janye ƙudurin ko kuma majalisa ta yi watsi da ƙudurin baki ɗayansa, amma daga bisa sai majalisar ta dattawa ta sanar da jingine aiki kan ƙudirin.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin - wanda ya jagoranci zaman - shi ne ya sanar da hakan yayin da suke muhawara zauren majalisar.
Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan Shugaba Tinubu ya umarci ma'aikatar shari'a ta ƙasar ta yi aiki tare da majalisar dokokin domin samun masalaha kan wasu ɓangarori na dokar da ake taƙaddama a kai.
Barau ya kuma sanar da kafa wani kwamati da zai yi aikin dubawa da kuma gyara saɗarorin dokar da ke jawo taƙaddama, musamman daga yankin arewacin ƙasar.
Majalisar ta kafa kwamiti ƙarƙashin sanata Abba Moro daga jihar Benue domin tattaunawa da ministan shari'a kan yadda za a yi wa ƙudirin garanbawul kafin sake mayar da shi ga majalisa.
Kuma bayanai na nuna cewa kwamitin ya kammala tattaunawa da tuntuɓar juna dangane da gyran siɗirorin da ke janyo cece-kuce a ƙudirin, inda bayanai ke nuna cewa akwai yiwuwar gudanar da jin ra'ayoyin ƴanƙasa kafin majalisar dattawa ta yi wa dokar karatu