Arewa celebrity

Arewa celebrity Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Arewa celebrity, Grocers, Kana, Kano.

02/11/2022

'YAN UWA❗ Dan ALLAH Muringa Kulada kannanmu Mata Wallahi Suna Shiga Wani Hali😭😭😭

Shawara ga 'yan uwa masu kanne mata, Wlh wasu yan matan suna lalacewa ne cos of rashin ɗaukar ƙananan nauyin su kamar irin takalma, waya, kati, kayan kwalliya, kayan sawa wasu wlh idan suna period basu da kuɗin da zasu sayi sanitary pads ma.

Akwai wata wnd na sani mamanta ta rasu, tana gaban matar babanta, babanta karamin ma'aikacin gov't ne kuma suna dayawa a gida take cemun sometimes omon wanki da sabulun wanka yana fin ƙarfinta, kuma tana da yaya wnd suke uwa daya uba daya dashi, yana aiki kuma yana samu amma sam baya taimaka mata da ko naira daya, kuma ba mata yake dashi ba. Idan babanta ya siyo dan abinda zai iya din ita ba’a bata a gidan.

kullum tunanin da take yi ta yaya zata samu kuɗi, ta ɗan fara business na zoɓo shima jari ya karye, ga rashin aure ga rashin aiki ga kuma bata samun financial support. Sbd haka dan Allah duk wanda take da ƙanwa ko ƙannai mata a taimaka musu ba sai sun buɗi baki sun tambaya ba. Idan kuma ba haka ba sai mace ta fara bin samari domin zasu bata kuma dole ita ma tayi payback.

Dan Allah maza da matan, muji tausayin yayye da ƙannan mu mata especially wnd basu da aure, Rashin kananun abubuwa irinsu pad din, kayan gyaran jiki dan turare haka su un**es na mata, da sauransu barazana ce a gareta.. a dinga taimaka musu dan Allah..

CC Hauwa Farouk Ibrahim

01/11/2022

Ana gobe zaa daura auran tsohuwar matarsa ya ga ba zai iya jurewa a rasa rai ba, don haka ya samu Wanda zai aureta ya ce masa.
"Ta gaya maka tana da cuta me karya garkuwar jiki kuwa?
Cikin tashin hankali Balarabe ya ce "Cuta me karya garkuwar jiki kuma?
Mahmud ya ce "Eh, a gurin haihuwar yaronmu na biyu aka gano ni da ita muna da wannan cutar, to ina son na gaya maka don na ga alamar ba ka da ita, don na ceci rayuwa, bana son a rasa rai, idan baka yadda ba za ka iya zuwa a muku gwaji, sai anjima."
Balarabe ya shiga matukar tashin hankali, don haka washegari bayan an cika gurin daurin aure wakilinsa ya tashi tsaye ya ce yana baiwa dangin amarya hakuri domin ango ya fasa wannan aure saboda wasu dalilai, hankalin kowa ya tashi a gurin musamman mahaifinta, guri ya rude da hayaniya da surutai, sai tsohon mijinta Mahmud ya Mike tsaye ya kalli mahaifinta ya ce.
"Baba ni na shirya mayar da auranmu da matata daman sabani ya rabamu har kuka fusata da ni, ina son a kara bani dama "
A take anan mahaifinta ya cika da farin ciki ya ce shi zai biya sadakin ma aka daura aure, bayan an daura aure mahaifin Maryam ya tari wakilan Balarabe ya ce yana son ya gaya masa dalilin fasa auran domin ya san laifin da yarsa ta aikata, wakilin ya gaya masa cewar baya son ya fada cikin mutane ne amma an gayawa Dansu cewar Maryam tana dauke da cuta me Karya Garkuwar jiki, hankalin mahaifin Maryam ya tashi ya shiga gida a fusace.

Maryam da iyayanta mata suna ta jimamin abunda ya faru, Maryam ta ji bakin cikin abun da Balarabe ya yi mata sai dai ta ji dadin yadda tsohon mijinta uban yayanta biyu ya fitar da ita kunya, don haka ta ji ta yafe masa duk wasu kurakurai da ya mata a baya.
Daidai lokacin mahaifinta ya shigo yana mata fada akan boye musu tana dauke da cuta me karya garkuwar jiki har ta so shafawa Wanda bai ji ba bai gani ba, hankalin Maryam ya kara tashi matuka, ta rantsewa mahaifinta bata da wannan ciwo idan kuma bai yadda ba aje a gwada, sai lokacin hankalin mahaifinta ya kwanta.

Shugaba Buhari na Najeriya ya ce shugaban CBN Godwin Emefiele ya samu sahalewarsa wajen canja takardar kudin NairaShugab...
01/11/2022

Shugaba Buhari na Najeriya ya ce shugaban CBN Godwin Emefiele ya samu sahalewarsa wajen canja takardar kudin Naira

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce matakin da babban bankin Najeriya CBN ya dauka na maye gurbin wasu kudade na Naira ya samu goyon bayansa kuma yana da yakinin cewa al’ummar kasar za su ci riba mai yawa ta yin hakan.

Da yake magana a hirar da tashar ralabijin ta Tambari TV, Shugaba Buhari ya ce dalilan da CBN s**a ba shi sun tabbatar masa da cewa tattalin arzikin kasar zai ci gajiyar raguwar hauhawar farashin kaya da jabun kudi. Kuma ya ce bai dauki tsawon watanni uku na canjin sabbin takardun kudi a matsayin gajeru ba.

Barkanmu da yau abokai
01/11/2022

Barkanmu da yau abokai

Address

Kana
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa celebrity posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category