12/06/2026
Al'umma KU GUJI HASSADA, KU RINKA GASAR A AIKATA AIYUKAN ALKHAIRI GA MUTANE MALAM AHMAD IBRAHIM ILYAS (SAYYADI).
Na'ibin Limamin Masallacin Juma’a na Maulana Sheikh Ilyas bin Abdurrahman da ke Danhassan, Malam Ahmad Ibrahim Ilyas (Sayyadi), ya yi kira ga al’umma da su guji hassada tare da mayar da hankali wajen aikata ayyukan alkhairi da za su amfani addini da al’umma.
A cikin huɗubar Juma’a da ya gabatar, Malam Ahmad Ibrahim Ilyas ya yi bayani kan illolin hassada, yana mai cewa hassada na daga cikin manyan munanan ɗabi’u da ke haddasa gaba, ƙiyayya da rabuwar kai a tsakanin mutane.
Ya bayyana cewa hassada ita ce laifin farko da aka fara sabawa umarnin Allah Maɗaukakin Sarki da shi, lokacin da Allah Ya umarci mala’iku su yi sujada ga Annabi Adam (A.S). Ya ce duk mala’iku sun yi biyayya ga umarnin Allah, amma Shaidan ya ƙi saboda hassada da girman kai, lamarin da ya sa Allah Ya kore shi daga rahamarsa.
Malam Ahmad Ibrahim Ilyas ya jaddada cewa Musulunci addini ne da ke koyar da soyayya, haɗin kai da yi wa juna fatan alkhairi, don haka ya kamata Musulmi su nisanci hassada tare da tsarkake zukatansu daga duk wani abu da zai haifar da ƙiyayya.
A ƙarshe, ya yi kira ga al’umma da su guji hassada, su rungumi kyawawan ɗabi’u, tare da yin rigingimu ne kawai wajen aikata ayyukan alkhairi da neman yardar Allah Maɗaukakin Sarki.
Rahoto Malam Yusuf Adamu Ɗanhassan kofar yamma DH Hausa TV.