21/06/2023
YANZU-YANZU: Gwamnan Kano Ya Mayar Da Rimin Gado Muƙamin Shugaban Yaƙi Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Jihar
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya mayar da Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado muƙamin shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC).
A wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce mayar da shi kujerar ya samo asali ne don yin biyayya da hukuncin kotu.
Gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje ce ta dakatar da Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado daga muƙaminsa bayan bisa ɓoyayyun lamura.