Kano State News

Kano State News Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kano State News, Grocers, hotoro, Kano.

Labari Da Ɗumi Ɗumi:Na janye ƙudirin kai hari Najeriya —Trump
03/11/2025

Labari Da Ɗumi Ɗumi:

Na janye ƙudirin kai hari Najeriya —Trump

Mun shirya za mu dira Najeriya, ta sama da Ƙasa domin mu murkushe masu kashe mana Kiristoci cewar Trump
03/11/2025

Mun shirya za mu dira Najeriya, ta sama da Ƙasa domin mu murkushe masu kashe mana Kiristoci cewar Trump

DA ƊUMI-ƊUMI :  An ɗauke Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara daga gidan gyaran hali na Kurmawa zuwa Kuje da ke Abuja.Wani Ɗa...
14/10/2025

DA ƊUMI-ƊUMI : An ɗauke Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara daga gidan gyaran hali na Kurmawa zuwa Kuje da ke Abuja.

Wani Ɗan uwansa mai suna Askiya Nasiru Kabara ne ya bayyana haka a shafinsa na Manhajar Facebook a ranar Talata, 14 ga watan Oktoba na shekara 2025.

Ministan Yaɗa Labarai Ya Taya Ɗanlami Nmodu Murnar Zama Shugaban Ƙungiyar Mawallafan Jaridun Yanar GizoMinistan Yaɗa Lab...
13/10/2025

Ministan Yaɗa Labarai Ya Taya Ɗanlami Nmodu Murnar Zama Shugaban Ƙungiyar Mawallafan Jaridun Yanar Gizo

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya Alhaji Ɗanlami Nmodu murna kan zaɓen sa a matsayin Shugaban Ƙungiyar Mawallafan Jaridun Yanar Gizo (GOCOP) a zaɓen da aka gudanar a Legas.

Idris ya ce: “Malam Nmodu, mawallafin Newsdiary Online, wanda nake da alaƙa ta abota da ta aiki da shi tsawon shekaru da dama, ɗan jarida ne nagari wanda ya tabbatar da cancantar sa a aikin jarida, kuma ya dace da wannan matsayi mai daraja.”

Ministan ya kuma yaba wa tsohuwar Shugabar GOCOP, Hajiya Maureen Chigbo, mawallafiyar RealNews Online, kan jagorancin ta na mawallafan onlayin su sama da ɗari da kuma barin “gado mai cike da daraja, ƙima, gaskiya, da cigaba mai ban-sha'awa ga ƙungiyar.”

Idris ya yi kira ga sabon Shugaban na GOCOP da abokan aikin sa na gudanarwa da su bai wa haɗin kan ƙungiyar muhimmanci, inda ya jaddada muhimmancin ƙulla kyakkyawar dangantaka a ƙungiya wadda za ta dauwama tsawon lokaci.

Ya ce: “Yayin da nake taya Nmodu murna, yana da kyau in yi kira a gare shi da ya jagoranci ƙungiyar ta hanyar haɗa kai, wanda ke tabbatar da cewa dukkan membobin GOCOP sun haɗa hannu da hannu wajen ci gaba da cimma burin ƙungiyar."

Haka kuma, ya jaddada muhimmancin lura da “mummunan tasirin labaran ƙarya, bayanan da ba daidai ba da kuma labaran ɓarna da ke barazana ga sahihancin aikin jarida.”

Saboda haka, Idris ya yi kira ga sabon shugabannin GOCOP da su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, wadda ke jagorantar wayar da kan jama’a kan ilimin kafofin yaɗa labarai a faɗin ƙasar nan.

“Na yarda da Malam Nmodu, wanda ya gina sana’ar aikin jarida bisa gaskiya, jajircewa, ƙarfin hali, da juriyar aiki, ya kuma kawo wannan irin ƙwarewa wajen haɗin gwiwa da gwamnati domin tabbatar da aminci da ilimin kafofin watsa labarai, musamman a cikin harkar kafofin watsa labarai na gidan gizo,” inji shi.

DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu Ta Aika Da ‘Yar Guda (Wadar Nan) Zuwa Gidan YariKotun majistare mai lanba 7 karkashin jagorancin mai ...
13/10/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu Ta Aika Da ‘Yar Guda (Wadar Nan) Zuwa Gidan Yari

Kotun majistare mai lanba 7 karkashin jagorancin mai shari'a Halima Wali ta aike da 'yar wadar nan da aka fi sani da 'yar guda gidan gyaran hali, bisa samunta tare da Mai wushirya da wallafa bidiyon batsa, kamar yadda Freedom Radio Nigeria ta ruwaito.

DA ƊUMI ƊUMI: Sojoji sun ceto wasu da aka sace a Jihar KwaraSojojin Runduna ta 2/Sashen 3 na Operation Fansan Yamma sun ...
13/10/2025

DA ƊUMI ƊUMI: Sojoji sun ceto wasu da aka sace a Jihar Kwara

Sojojin Runduna ta 2/Sashen 3 na Operation Fansan Yamma sun ceto mutane uku da aka sace a wani samame da s**a kai a dajin Babanla, Jihar Kwara.

Mataimakin Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Kyaftin Stephen Nwankwo, ya bayyana cewa sojojin sun kubutar da Mrs. Oluwabusayo Taiwo da ɗanta mai shekara uku, waɗanda aka sace a garin Oke-Ode tun ranar 28 ga Satumba, 2025.

A wani aiki dabam, sojojin sun kuma ceto wani mai sayar da shayi, Malam Mohammadu Sani, wanda aka same shi cikin jini bayan ‘yan bindiga sun gudu s**a bar shi.

An kwato bindiga da adda daga wurin da aka kai samamen.

Kwamandan rundunar, Birgediya Janar Ezra Barkins, ya yaba da jarumtar sojojin, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da sintiri da hare-haren kai tsaye don kawar da duk masu tada hankalin jama’a a jihar da kewaye.

Yadda kwamitin Shura na jihar Kano ta zauna da Sheikh Lawal Abubakar Triumph a Ofishin DSS, kan zargin da ake yi masa na...
13/10/2025

Yadda kwamitin Shura na jihar Kano ta zauna da Sheikh Lawal Abubakar Triumph a Ofishin DSS, kan zargin da ake yi masa na kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW.

Shugaba Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban ƙasa Namadi Sambo murna bisa nadin sa a matsayin Sardaunan ZazzauShuga...
10/10/2025

Shugaba Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban ƙasa Namadi Sambo murna bisa nadin sa a matsayin Sardaunan Zazzau

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Namadi Sambo, murna bisa nadin sa da aka yi a matsayin Sardaunan Zazzau daga Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli.

Nadin ya gudana ne a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, a Zariya, Jihar Kaduna.

A cikin wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa, Tinubu ya bayyana wannan mukami da cewa yana da matuƙar daraja a al’adu da tarihi na Arewacin Najeriya, kuma ya nuna yadda masarautar Zazzau ta amince da basira, gaskiya da jajircewar Namadi Sambo wajen ci gaban al’umma.

Shugaban ya ce wannan girmamawa alama ce ta jagoranci nagari da gudummawar Sambo ga cigaban ƙasa tun daga lokacin da ya rike manyan mukamai a gwamnati.

Ya kuma yabawa Sarkin Zazzau bisa ci gaba da riƙe al’adar girmama mutanen da s**a yi fice wajen jagoranci, kishin ƙasa da kuma ɗorewar zaman lafiya.

Shugaba Tinubu ya yi fatan Allah ya ba tsohon mataimakin shugaban ƙasa nasara a sabuwar rawar da zai taka, tare da kira gare shi da ya ci gaba da zama abin koyi ga matasa da kuma yin aiki kafada da kafada da shugabannin gargajiya domin ci gaban al’umma da ƙasar baki ɗaya.

Sabbin Jami’an ‘Yan Sanda 10,000 Sun Kammala Horo a Fadin ƘasaRundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yaye sabbin jami’ai 10,00...
08/10/2025

Sabbin Jami’an ‘Yan Sanda 10,000 Sun Kammala Horo a Fadin Ƙasa

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yaye sabbin jami’ai 10,000 bayan kammala horo a manyan cibiyoyin horas da ‘yan sanda na ƙasa. Bikin yaye jami’an ya gudana a lokaci guda a ranar 7 ga Oktoba, 2025, a faɗin Najeriya.

A jawabin da aka gabatar wa sabbin jami’an, an bukace su da su kasance masu ɗa’a, tsoron Allah, da ƙaunar ƙasa, tare da bin ƙa’idojin aikin su da sadaukarwa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

An horar da su ne bisa ƙa’idodin aikin ‘yan sanda na zamani, ciki har da dabarun hulɗa da al’umma, kiyaye hakkin bil’adama, da yadda za su fuskanci kalubalen tsaro na wannan zamani.

Wannan yaye jami’ai ya ɗaya daga cikin matakan da ake ɗauka domin ƙara ƙarfin rundunar da inganta tsaro a ƙasa. Rundunar ta tabbatar da ci gaba da horarwa da sauye-sauyen da za su inganta aikinta da kuma tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya.

Rundunar Ƴansanda ta ƙasa ta dakatar da tilasta nuna da shaidar izinin amfani da gilashi mai duhu ga direbobin motoci.Da...
08/10/2025

Rundunar Ƴansanda ta ƙasa ta dakatar da tilasta nuna da shaidar izinin amfani da gilashi mai duhu ga direbobin motoci.

Daily Trust ta rawaito cewa Kakakin rundunar ƴansanda ta Abuja, SP Josephine Adeh ce ta baiyana hakan a zantawar ta da gidan talabijin na AIT a yau Laraba.

SP Adeh ta ce sanarwar ta fito ne bayan rundunar ta samu umarnin kotu da ya dakatar da ita daga daukar matakin.

Ta ce dakatarwar za ta ci gaba har sai abinda kotu ta yanke nan gaba.

Ya ce rundunar ƴansanda ta ƙasa ta ɓullo da tilasta nuna shaidar izinin amfani da gilashi mai duhu ne a jikin motoci saboda tsaro, inda wasu ke amfani da hakan su aikata munanan laifuka.

Sanata Abdul Ahmed Ningi ya ɗaga yatsu biyu inda ya yi ƙira da a 'yanta Al'ummar Falasɗin a cikin Majalisar Dattawa ta N...
08/10/2025

Sanata Abdul Ahmed Ningi ya ɗaga yatsu biyu inda ya yi ƙira da a 'yanta Al'ummar Falasɗin a cikin Majalisar Dattawa ta Najeriya

TIRƘASHI: Cristiano Ronaldo ya zama ɗan wasan ƙwallon ƙafan da ya fi kowane ɗan wasa kuɗi a duniya, inda ya zama na fark...
08/10/2025

TIRƘASHI: Cristiano Ronaldo ya zama ɗan wasan ƙwallon ƙafan da ya fi kowane ɗan wasa kuɗi a duniya, inda ya zama na farko da ya mallaki Dala Biliyan Ɗaya na dukiya.

Cristiano Ronaldo ya zama ɗan wasan ƙwallon ƙafa na farko da ya zama bilyane, a cewar kamfanin bayanan kuɗi da kafofin watsa labarai na Bloomberg.

Bloomberg Billionaires Index, wanda ke bibiyar attajirai a duniya bisa ga darajar kadarorinsu, ya bayyana cewa dukiyar ɗan shekaru 40 ɗin nan dan asalin Portugal kuma ɗan wasan Al-Nassr an auna ta a karon farko.

Rahoton ya haɗa da abin da ya samu a duk tsawon aikinsa, jarin da ya saka da kuma tallace-tallace da yake yi, inda aka kiyasta cewa dukiyar Ronaldo ta kai dala biliyan 1.4 (£1.04bn).

Bloomberg ta ce ya samu fiye da dala miliyan 550 (£410m) a matsayin albashi tsakanin shekarar 2002 da 2023, sannan ta bayyana yadda yake samun kuɗi ta hanyar yarjejeniyoyi da tallace-tallace, ciki har da yarjejeniya da kamfanin Nike mai ɗaukar tsawon shekaru goma da kimanin dala miliyan 18 (£13.4m) a kowace shekara.

Address

Hotoro
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kano State News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category