Abubakar idris kadiri

Abubakar idris kadiri ALL PRAISE IS TO ALLAH
MAY ALLAH HELP US

24/06/2025

A Saukake

DARASI NA 2

REBE-REBEN ARTIFICIAL INTELLIGENCE AI (NAU’UKAN AI)

Gabatarwa

K**ar yadda mutum ke da matakan fahimta

K**a daga yaro → saurayi → dattijo),

Haka ma AI ma yana da nau’o’i guda uku dangane da yadda yake fahimta da aiki. Wannan darasi zai bayyana yanda AI ya Kasu zuwa Nau'i Guda Uku kamar Haka,

na Farko.

1. ANI – Artificial Narrow Intelligence

(AI Mai Ƙwarewa a Aiki ɗaya)

Wannan shi ne nau’in AI da muke amfani da shi a yau.

Yana iya aiki ne akan wani abunda aka Tsarashi kawai, Ba zai iya yin abin da bai koya ba. Yana yin aiki guda ɗaya misali kamar gane murya, fassara kalma, ko tantance fuska.

Misalan ANI:

Google Translate – AI ne da zai maka fassara daga Hausa zuwa Turanci wato Translation.

Siri/Google Assistant – AI ne Da yake amsa tambayarka da Aiwatar Da Umarni.

Chatbot – AI Ne da yake Taimakawa Mutane Wajen Amsa Tambayoyi kamar Chatgpt, Deepseek, Perplexity, Claude Da Sauransu.

Motocin da suke tuƙa kansu– AI ne da Aka Tsarasu Don iya gudanar da mota amma ba su da fahimtar duniya.

Da Sauransu.

Na Biyu

2. AGI – Artificial General Intelligence

(AI Mai Aiki K**ar Dan Adam)

Wannan nau’in AI ne da zai iya yin duk wata fahimta da aiki kamar mutum, kamar tunani, fahimta, iya magana, yin shawarwari, har ma da jin tausayi. AGI AI ne da yake aiki kamar yadda mutum zai iya.

Misali: Idan aka samar da AGI, zai iya zama malami, likita, lauyan AI

duka a lokaci guda, kuma da fahimta kamar mutum.

Sai na Uku Kuma

3. ASI – Artificial Super Intelligence

(AI Mai Aiki da Tunani Fiye da Mutum)

Wannan AI ne da zai yi aiki da Tunani fiye da mutane hankali, AI ne da zai iya warware matsalolin da dan Adam bai zai iya ba warwarewa ba. Yana iya karatu da koyon abu cikin sauki sosai fiye da Mutum.

Misali: Idan ASI ya kasance, zai iya gano maganin cuta mai wahala fiye da duk wani likita, Har yanzu ASI yana cikin mafarki da bincike, amma masana na fargabar illa ko barazana daga irin wannan AI idan bai samu kulawa ba.

Abun da

24/06/2025
18/06/2025
With Moniepoint – I just made it onto their weekly engagement list by being one of their top engagers!
18/06/2025

With Moniepoint – I just made it onto their weekly engagement list by being one of their top engagers!

12/06/2025

It's easier than you think

12/06/2025

Jirgin Sama Mai Dauke da Mutane 240 Ya Fado Jim Kad’an Bayan Tashi A kasar
INDIA
_______

Wani jirgin sama da ke kan hanyarsa ta zuwa Birtaniya ya fado jim kad’an bayan tashinsa, yana dauke da fasinjoji da ma’aikata 240 a cikinsa.

Lamarin ya faru ne mintuna kaɗan bayan jirgin ya tashi daga filin jirgin sama, inda ake zargin ya gamu da wata matsala ta fasaha ko lalacewar injin kafin ya samu damar yin nisa. Wannan mummunan hadari ya jefa al’ummar da ke kusa da filin jirgin cikin firgici da tashin hankali.

Ma’aikatan agajin gaggawa sun bazama zuwa wurin da hadarin ya faru domin gudanar da aikin ceto. Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da kokarin ceton rayuka da kuma kashe gobarar da ta tashi daga jirgin.

Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewa:
"Na ji karar fashewa, sannan na hango hayaki mai yawa yana tashi. Nan take jami’an ceto s**a fara karasowa da motoci da kayan aiki."

Hukumomi sun tabbatar da cewa jirgin na dauke da mutane 240, ciki har da fasinjoji da ma’aikatan jirgin. Har yanzu ba a fitar da cikakken bayani kan adadin wadanda s**a rasa rayukansu ko s**a jikkata ba.

Wata majiya daga hukumar sufurin jiragen sama ta ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin hadarin, kuma za a fitar da cikakken bayani da zarar an kammala rahoto.

Me zaku ce kan hakan...?

12/06/2025

Wacce santoriya ce tafi dacewa da wakili a zauren Majalisar dattijai daga Jihar Kano, wanda yake sauke nauyi ba tare da yaudara ba?

12/06/2025

Ta fuskar sauke nauyin wakilcin al'umma, maki nawa zaku bawa dan Majalisar tarayya na yankin ku cikin shekaru biyu da s**a shafe a zauren Majalisa?

10/06/2025
10/06/2025

Address

Kadiri Ajingi Kano
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abubakar idris kadiri posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category