01/02/2026
Da ɗumi-ɗumi: Shirin juyin mulki — An shirya harbe ni idan na ƙi miƙa wuya, inji Ministan Tsaro
Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya bayyana cewa yana daga cikin manyan mutanen da aka sa a gaba a wani shirin juyin mulki da jami’an tsaro s**a gano kuma s**a dakile.
Janar Musa ya ce, bisa bayanan leƙen asiri da aka tattara, an shirya harbe shi ne idan ya ƙi miƙa wuya ko ya nuna adawa da waɗanda s**a ƙulla shirin. Ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi na tsaro, inda ya jaddada cewa shirin ya kai matakin tsara k**awa da amfani da ƙarfi kan wasu manyan jami’an gwamnati.
Ministan ya yaba da hanzari da ƙwarewar jami’an tsaro, yana mai cewa haɗin gwiwar sojoji da sauran hukumomi ne ya taimaka wajen dakile barazanar kafin ta kai ga aiwatarwa.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙarfafa tsaro da bincike domin kare dimokuraɗiyya da zaman lafiya a ƙasar.
A cewarsa, duk wani yunkuri da zai kawo ruɗani ko juyin mulki ba zai samu gurbi ba, domin jami’an tsaro na nan a faɗake, kuma za a ɗauki tsauraran matakai kan duk wanda aka k**a da hannu a lamarin.