27/01/2025
KA YI WASA DA MATAR KA!!!
🌹Kayi wasa da matar ka sunnah ne
🌹Ka kirata da suna mai dadi sunnah ne
🌹Yawan fada mata kana sonta sunna ne
💧Wani namijin fa rabon matar sa da ganin dariyar sa har ta manta
💧Saboda yana ganin in ya sake ma matarsa yayi wasa da dariyar da ita kamar kimarsa zata ragu ko kuma raini zai shiga tsakanin su
💧Wata macen ma da taji alamun mijinta ya dawo sai gaban ta ya fadi saboda tsoron ydd zai shigo gidan fuska a hade ba fara'a ba nishadi
💧Haba yayana rayuwar aure fa rayuwa ce ta sakewa, kwanciyar hankali da fahimtar juna, bawai rayuwar kunci ba ace a gdn ka ba ka wasa da matar ka baka kiranta da sunaye na soyayya baka yawan fada mata kana son ta, Ai kam baka san dadin aure da kwanciyar hankali ba
💧Ai in kana son ganin tsantsar tsagwaron kwanciyar hankali da soyayyah a gdn ka, to time to time ka dinga biyewa matar kuna wasa da nishadi ka kira ta da suna me dadi na soyayya sannan ka dinga yawan fada mata kamar INA SON KI a kowane lokaci, Mu mata muna son hakan, sannan za ku kara samun Shakuwa da kaunar juna
💧Kayi mata uzuri idan tayi ba dai dai ba sannan ka gyara mata idan tayi kuskure
💧Kayi koyi da sunnar Annabi muhammad (ﷺ)
Wajen tafiyar da rayuwar gidanka Akhy, Dan Allah a daure a gyara ko dan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kaunar juna
Allah yasa Mudace