NOMAN AREWA

NOMAN AREWA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from NOMAN AREWA, Farmers market, www. nomanarewa. com, Katsina.

๐ŸŒฟ Important Facts About W**d Control ๐ŸŒฟAs a farmer, understanding w**ds is crucial for successful crop management. Here a...
07/07/2024

๐ŸŒฟ Important Facts About W**d Control ๐ŸŒฟ

As a farmer, understanding w**ds is crucial for successful crop management. Here are some key insights every farmer should know:

๐ŸŒฑ W**ds come in three main types: broadleaves, sedges, and grasses.

๐Ÿšœ W**ds are fierce competitors, vying with crops for vital resources like nutrients, water, and light.

๐ŸŒพ W**d control methods include manual, mechanical, cultural practices, and chemical solutions tailored to different growth stages.

๐ŸŒฑ Chemical w**d management occurs at three stages: pre-plant (burn-down), pre-emergence, and post-emergence.

๐ŸŒฟ Pre-plant burn-down herbicides are vital in zero-till systems to eliminate existing w**ds before crop sowing.

๐ŸŒพ Pre-emergence herbicides target w**ds post-seeding but before their emergence, ensuring optimal moisture levels.

๐ŸŒฑ Post-emergent herbicides are applied after both crops and w**ds have sprouted, typically at the 3-4 leaf stage.

๐Ÿšœ Choosing the right herbicide is critical, considering the w**d type (broadleaf, sedge, or grass) and the stage of w**d control required.

Stay informed, stay proactive, and keep those w**ds at bay for a successful harvest season! ๐ŸŒพ๐ŸŒฟ **dControl

In farming as a business you need to learn how to crawl before you can walk , it is key that you master one type of crop...
07/07/2024

In farming as a business you need to learn how to crawl before you can walk , it is key that you master one type of crop before you can heavily invest In diversification.
Before you decide to introduce Many crops
To the mix, be known for one thing !And try by all means to be the person known for it..
Iโ€™m sure when we name a few farmers we know crops associated to their business and what they Grow mostly and thatโ€™s their core Strength , despite them growing other things .

When you start its important to establish what type of produce you would like to specialize in and that you are known for. This way you are the go to person because you are good at it.
You must learn to focus on your core strength to ensure long term growth
Keep in mind that a farm can only produce according to what is invested in it .
As a farmer remember to base your decision on the future and not Just your desire to farm or what is being hyped !!
PC Mwape Your AgroPreneur The Potato Farmer

Manoma za su samu tallafin N2.5bn domin bunkasa aikin noma a jihar Jigawa - Karin bayani a sashen sharhi.JigawA state
06/07/2024

Manoma za su samu tallafin N2.5bn domin bunkasa aikin noma a jihar Jigawa - Karin bayani a sashen sharhi.

JigawA state

06/07/2024
06/07/2024
YACCA AKE NOMAN DANKALIN TURAWAJANHANKALI: KA KULA SOSAI DA ABINDA ZAKA KARANTA KUMA KA LURA DA KA,IDOJIN DANA ZAI YANO ...
06/07/2024

YACCA AKE NOMAN DANKALIN TURAWA

JANHANKALI: KA KULA SOSAI DA ABINDA ZAKA KARANTA KUMA KA LURA DA KA,IDOJIN DANA ZAI YANO KA KUMA KARA NEMAN ILIMIN HAKAN SOSAI KA KUMA FARA KWAREWA KAFIN KA ZUBA KUDINKA MASU YAWA ACIKI. DUK WANNAN MATAKAN NOMA ZA AYI AMFANI DA SUNE WAJEN YIN NOMANSA A BUHU, BOKITI KO KUMA TAYA KO KUMA CONTAINER.

MATAKIN FARKO

Kafin ka fara noman dankali turawa ya kamata ka fara lura da yadda girmansa yake. Domin yana yin tsuru akanshi. Wanda idan wannan tsuron ya samu yanayi mai kyau sai yayi yado ya zama ece. Wanda shi kuma wannan icen shine daga baya yake komawa bishiyar da ta ke fitowa saman kasar daka shuka sa akai. Sannan kuma duk wani sinadren da yake so suna samuwa ne daga jikin wannan bishiyar ne. Yana kuma tafiya kasa ne domin wannan dankalin. Hakan kuma zai saka ya samu jijiyoyi masu karfi wainda zasu samar da wannan dankalin.

MATAKI NA BIYU

ka zabi irin dankali mai kyau dan yin nomansa. Ka zabi yayan dankali masu kyau domin yin iri dasu abu ne wanda ya zama dole Don samun ribar noman nasa. Wanda awajen zabar dankalin da zaka yi shuka dashi dole ne ka lura da abubuwa guda biyu. Akwai iri mai saurin fitowa Wanda baya daukar dogon lokaci Ana kuma Kiran wannan irin da short cultivation season seed da kuma mai daukar dogon lokaci kafin yafito Ana kuma Kiran wannan da long cultivation season seed.

Banbanci awajen wanne ya dace dakai amfani dashi yana dogaro ne da inda zakayi shukar. idan agurin da zakayi shukar akwai hasken rana sosai kuma akwai yanayin zabi kana bukatar iri mai karamin zango ne wanda baya huce kwana sittin 60days zuwa sabain 70days. Ka fin yafito. Ana kuma samun irin wannan yanayin ne a tropical areas da kuma inda yake da Sahara sosai. Kamar muma nan arewa mun fi amfani da irin wannan seed din.

Sannan kuma idan aguraran da kake akwai karancin hasken rana wanda hakan ke haifar da long cultivation season to kanada bukatar iri mai daukar dogon zango kafin ya fito. Wanda galibin wannan irin yakan dauki tsawon gwanaki kafin ya fito kamar kwana 110 zuwa 135 kafin ya nuna yadda ya kamata. Wanda alfanun irin wannan seed din mai karamin zango yakan cigaba da fitowa har bayan ka cire wanda s**a fara yi. Idan kaga ya daina yi sai dai in tushiyar ta sa ka cire ko kuma kwari da kuma ruwa ne s**a rubar dashi koma dai rashin taki.

JANHANKALI: IDAN KANASON GANIN ALFANUN SHUKAR TAKA TO KA SIYI IRINKA DAGA MANOMA DA AKA TATBATAR DA CEWA NASU BAYA DAUKE DA CUTA KUMA NA GURINSU YANA DA AMINCI SOSAI.

MATAKI NA UKU

GA YADDA ZAKA IYA SAMAR DA TSURON DANKALIN

Abu na farko da za kayi bayan ka siyo dankalin turawa ka samu taya ko kuma waje mai kyau sai ka zuba ciyawa Sannan kuma sai ka dauko irinka ka zuba. Daga nan sai ka zuba wata ciyawar akai kabar shi ya dauki kamar sati biyu kullum kana zuba masa ruwa. Bayan ka dauke shi ka kai shi inda rana take yadda a kullum zai ringa samun hasken rana na tsawon awa shida. Kuma yanayin inda ka kai shi temperature din takai 60f to 70f degrees. Kullum kana yayyafa masa ruwa da zarar ya fara tsuro akan sa wato ya fara fitar da idanuwa. A dai dai lokacin da ya kai girman kwai sai ka dauke shi. Ka fara yayyankashi zuwa kanana wato gutsire daban-daban wanda duk guda daya zai dauki tsuro daya ko kuma biyu wato idanuwan da s**a fito.

JANHANKALI:IDAN KA TAMBAYI MASU SAI DA DANKALIN KANA NEMAN IRI MAI KYAU ZASU IYA BAKA. WANDA WASU HAR WANDA YAYI TSURON ZASU BAKA. AKWAI IRI MASU SUNA DABAN-DABAN IRINSU HAKURIN HAJIYA, RC, DA KUMA DUKOLO.

MATAKI NA HUDU

LOKACIN FARA SHUKAR DANKALIN TURAWAN

A kowane lokaci yana fitowa Amman abun lura anan shine kai a gurin da kake rayuwa wana yanayi ne yafi. Kamar mu nan arewa da muke cikin tropical regions kuma muna hasken rana kaga kenan irin da zamuyi amfani da shi bai huce mai gajeren zango ba kuma a kowane lokaci daga September zuwa January zamu iya fara shukar dankalin. Ka tattabata ka kula da yanayin damuna domin baya son lema sosai Sannan kuma baya yi acikin fadama sosai idan noman fili zaka yi. Bayan ka shuka sa da zarar ruwa ya fara masa illa to ka cireshi kayi amfani da shi domin abinda zai faru na gaba shine rubewa zai fara bayan sati biyu.

MATAKI NA BIYAR

KANEMI MAZUBI MAI KYAU

kanemi mazubi mai kyau mai kuma zurfi wanda zai iya daukar ruwa kamar gallon arbain. Domin samun mazubi mai kyau mai kuma zurfi na bashi damar girma yadda ya kamata cikin sauki da kuma ban sha,awa. Ka nemi buhun taki, ko kuma jarka, ko kuma ka nemi bokitin fenti ko taya. Koma mai ka zaba da za kayi amfani dashi dole ne kabi wannan ka,idar da zan zai yano maka. Ka fin ka fara shuka dankalinka ka duba sosai shin zai iya fitowa acikin mazubin. Domin duk guda daya yana bukatar kamar inda ruwa gallon uku zai shiga ciki. Domin da zarar sun cunkushe a waje daya hakan zai hanasu damar fitowa yadda yakamata domin jijiyoyinsu bazasu samu damar baza ya,ya masu matukar girma ba sai dai ka girbi kananan ya,ya.

Sannan kuma idan ka zo shuka ka fara zuba kasar nomanka mai hade da takin gida kafin ka fara saka dankalin ka. Domin dank

WANNAN IYA DAMAR MANOMA CEAssalamu alaikum to manoma ga dama ta samu Mun bude online Extension programme wadda zamu rika...
06/07/2024

WANNAN IYA DAMAR MANOMA CE
Assalamu alaikum to manoma ga dama ta samu Mun bude online Extension programme wadda zamu rika gabatar da bayanai akan noma zalla da kuma bada shawarwari game da duk wata matsala da kuka shiga cikin harkokin noma kowane iri domin tabbatar da kunyi nasara. A wannan shiri zamu rika kawo darussa akan dabarun noma abubuwa kala dabam-dabam tare da yadda ake nomawa a duk inda kuke. Wasu daga cikin Ire-iren abubuwan da zamu rika bayanin yadda ake nomansu sun hadar da Gero, dawa, masara, shinkafa, waken soya, farin wake da jan wake, noman gyada, ridi, zobo, kankana, sweet melon, dankalin hausa da na turawa da sauran duk abinda Allah yasa wani yayi tambaya akai. Wadannan bayanai sun hada tun daga zaben iri,filin gona,gyaran gona, shuka/dashe, noman ciyawa,irin takin da ake sakawa, magungunan ciyawa da na cututtuka dadai sauransu. Duk wadda yake da ra'ayi zaiyi rijista sai ya tuntubemu ta hanyar kira ko whatsapp a wannan lamba 08060869672. Shirin zai rika gudana ne ta hanyar whatsapp, amma idan an samu masu yin telegram dayawa suma zamu bude musu group domin duk bayanan da aka dora tanan basa gogewa.
TO MANOMA SAI GAREKU DAMA TA SAMU.
KU TURAWA YAN UWA (SHARE) DOMIN SU SAMI DAMAR SHIGA WANNAN GIDA NA NOMA ZALLA.

YADDA AKE NOMAN GERO KASHI NA 1GABATARWAGero daya ne daga cikin abincin da miliyoyin manoma da masu matsakaicin karfi ke...
06/07/2024

YADDA AKE NOMAN GERO KASHI NA 1
GABATARWA
Gero daya ne daga cikin abincin da miliyoyin manoma da masu matsakaicin karfi ke amfani dashi yau da kullum wanda yawanci akafi nomawa a yankin kasashen Africa da Asia. Gero ana noma shi a kasar Najeriya musamman a Arewacin kasar a cikin jihohin yankin arewa maso yamma (Kano, Kaduna, Katsina, Jigawa, Kebbi, Sokoto, Zamfara) da kuma a jihohin dake arewa maso gabas (Borno, Adamawa, Bauchi, Taraba, Gombe,Yobe). Haka kuma ana noman gero a dukkan kasashen yammacin africa musamman masu makotaka da Najeriya Nijar da Kamaru.
Gero daya ne cikin jinsin tsirrai dangin ciyayi (cereals) wanda a jikin guda ba'a samun yaya kadan (Misalinsu sune Dawa, Maiwa, Shinkafa, Masara, Alkama dadai sauransu, duka wadannan gida guda suke da gero). Idan akayi duba da darajar Gero kuma, a yanzu haka yana daga cikin abubuwan da takala ke nomawa masu matukar tsada a kasuwannin arewacin Nageriya da kuma a kasar Nijar domin a lokuta da dama yana wuce masara kudi a doron kasuwa musamman idan yayi karanci kasantuwar masu cinsa a matsayin abinci sunfi yawa.
A yanzu haka gero ya shiga cikin jerin rukunin amfanin gona masu daraja (value chain crop) a cikin dukkannin kasuwannin da ake siyarwa a Najeriya, hakan ya samo asali ne saboda kasantuwarsa daya tilo cikin abinci mai mahimmanci ga talakawa marasa karfi, haka kuma ya zama daya cikin abubuwan da ake nomawa sau daya kacal a cikin shekara (Lokacin damina). Gero yana iya jurar yanayin karancin ruwa (fari) kasancewar dama shi a tudu bisa kasa mai yashi ake iya nomashi kawai.

AMFANIN NOMAN GERO
Noman gero nada matukar amfani domin hakan ne ya bashi damar shiga cikin abubuwa masu daraja. Hanyoyi biyu da gero yake amfanarwa kamar haka:
1) Abinci: Gero ana amfani dashi a matsayin abinci ta hanyoyi da dama, kuma wannan shine dalili mafi girma da yasa ake nomansa a Najeriya da sauran kasashen Africa. Gero ya zama abinci mai matsayi a wajen mutanen arewacin Nageriya da Nijar saboda yana daya daga abincin alโ€™ada mai

NOMAN ALBASA NA ZAMANIWannan shine kalan noman zamani da ake kira da hydroponic farming, noma ne da yake da wannan fasah...
05/07/2024

NOMAN ALBASA NA ZAMANI

Wannan shine kalan noman zamani da ake kira da hydroponic farming, noma ne da yake da wannan fasahar , karancin fadin filin gona, karancin ruwa, karancin lokaci,da rashin noma,(w**ding)aturance ,uwa uba gujewa harin bandit,, wannan idan tafiya na tafiya hakan to dolene mu koma wannan digital farming,bashi ba tsammani, kuma shina bada ammafini gona fiye da conventional agriculture,ga karancin lokaci da ammfanin gona zai ษ—auka.yAllah shi sa mucika da imani, lalle saresarin hauka tsintar tsumman jiji.

((Yadda ake dashen albasa.))Mun fara mantawa da noman masara da dawa da shinkafa mun rungumi noman albasa.Noman albasa n...
05/07/2024

((Yadda ake dashen albasa.))

Mun fara mantawa da noman masara da dawa da shinkafa mun rungumi noman albasa.

Noman albasa noma ne mai kyau da zai shigo maka da manyan kudin da bakayi tsammani ba a lokaci guda. Idan baka tayi ba shine ba zaka san haka ba

Address

Www. Nomanarewa. Com
Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when NOMAN AREWA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category