17/04/2024
ุฅููููุง ูููููู ููุฅูููููุง ุฅููููููู ุฑูุงุฌูุนููู
Rikici tsakanin Jami'an Kastam da Mutanen gari ya yi sanadiyar Asarar Rayukan Mutum biyu
Da safiyar ranar Laraba 17 ga wata Afrilu Wani rikici ya barke tsakanin Direbobi da Jami'an hana fasa Kwabri (Custom) dake kan hanyar Kaita daga Shatale-talen Shinkafi, wanda Direbobin na manyan Motoci da kananan motoci s**a kashe T**i don bayyana fushin su bisa abinda s**a yi zargi cewa Jami'an hana fasa Kwabrin na yi masu.
Sun bayyana cewa Jami'an na Kwastan sun takura masu da amsar na goro babu gaira babu dalili kuma ba busa Doka ba, s**a ce idan zasu shiga da kaya a garin kaita ko Dank**a ana maishe su k**ar ba 'Yan Najeriya ba, sai an kwalkwalesu tas kana a barsu su wuce.
Bayan wannan gangami da kashe hanya da Direbobin s**ai, daga bisani al'amura sun lafa, wanda kuma bayan Direbobin kowa ya k**a gabansa akan hanyar zuwa Dank**a ta karamar hukumar Kaita, sai wani Cakin Point na Jami'an Kwastan ya tare wata babbar mota da fasinja, inda shi kuma Diraban yaki tsayawa wanda haka ya sabbaba jami'in yayi harbi da bindiga har ya samu wani fasinja, wanda aka ce ya Mutu.
Harbin ya sanya Diraban ya tsaya inda fasinjan Motar s**a fito a cikin fushi da ya haddasa daukar fansa ga jami'in Kwastan din da yayi harbin mai suna Auwal Haruna.
Mun nemi jin ta bakin Jami'in Hurda da jama'a na hukumar hana fasa Kwabri a jihar Katsina yace zasu fitar da sanarwa a hukumance, wakilan Katsina Times ya ga Motar Daukar gawa da Jama'an Kwastan din a lokacin da s**a isa inda s**a dauko mamacin har zuwa dawowarsu.
Matsala tsakanin jami'an Kwastan da mutanen gari ko Direbobi ba sabon abu bane, a kan iyakokin Nijeriya da Niger musamman iyakar Jibiya zuwa Niger da iyakar Dank**a zuwa Niger, ko a watannin bya ansha irin wannan Tankiyar a tsakanin Mutanen Jibiya da Jami'an wanda abin har ya kai su ga zama Kotu, bayan tsauwalawa da kuma Asarar rayuwa can da in da yake faruwa.