18/01/2024
Muna cikin tashin hankali bayan ƙarewar wa‘adin karɓo ƴan'uwan Nabeeha'.
Sa'o'i 2 da s**a wuce
Iyalan budurwar nan, Nabeeha Al-Kadriyar da a baya-bayan nan ta rasa ranta a hannun yan bindiga sun ce suna cikin tashin hankali saboda karewar wa'adin biyan kudin fansar da masu garkuwar s**a bukaci a biya.
Asiya Adamu, wadda ta yi magana da BBC a madadin iyalan yan matan, ta ce a yanzu haka suna sauraron kiran waya ne daga ƴan bindigan domin sanin mataki na gaba.
Ta ce a halin yanzu iyalan sun yi bakin abin da za su iya, to amma suna jiran umarni daga masu garkuwa da yaran.
Ta ce: "Hankalin kowa a tashe yake, muna jira, muna kewar su. Kawai muna son mu ga sun dawo," in ji Asiya.
Ta ce a duk lokacin da yan bindigar s**a tuntubi iyalan yan matan suna hada su da iyayensu a waya su yi magana don su fada musu halin da suke ciki tare da neman su gaggauta biyan kudin fansar da masu garkuwa da su s**a nema.
A ranar 2 ga watan Janairu ne yan bindigar s**a sace Nabeeha da mahaifinta tare da yan uwanta biyar - Nazeera (20), Najeeba (23) sai tagwaye Ajeeba da Aneesa (13) da Mardiyya daga yankin Bwari da ke Abuja, babban birnin Najeriya inda kuma s**a nemi a biya su maƙudan miliyoyi, waɗanda iyalan s**a ce sun fi ƙarfinsu.
Sai dai sun saki mahaifin yan matan domin ya je a hada kudin fansar yayansa amma kafin a kai ga hada kudin ne kuma Nabeeha ta rasa ranta a hannun yan bindigar daga bisani s**a kara adadin kudin fansar.
Asiya ta ce suna kewar yan matan kuma iyalan na ci gaba da addu'a domin neman mafita.
Labarin sace yan matan dai ya karade shafukan sada zumunta inda kungiyoyi da fitattun yan siyasa kamar Atiku Abubakar da Sheikh Isa Ali Pantami da wasu masu amfani da shafukan sada zumuntar s**a yi ta nuna rashin jin dadi kan yadda matsalar sace-sacen jama'a ke kara kazancewa a Najeriya.
Ita ma mai dakin shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu ta bayyana yadda labarin mutuwarNabeeha ya girgizata inda ta yi kira ga jami'an tsaro su kara kaimi domin ganin an kubutarda ragowar yaran