19/08/2026
Part 2
ZUWA LAGOS BA KA JIN TURANCI WATA LUKUTAR MASIFA CE😂
Na kashe wayar na fara had'a kaya na a ba'kar leda.
Murna kuwa a wuri na ba'a cewa komai, ko banza dai zani babban birni, kuma dole inci abinci irin wanda yake ci.
Har dare ya sake kira na, yana kara shaida min
"Kada ki zo, don baki san yadda ake rayuwa a kudu ba ne, wahala kawai zaki sha, kin saba da zama a cikin gida cikin rufin asiri, yanzun in kinzo lagos kin san halin da zaki fad'a?"
Na ce "E na sani mana, ba ina tare da kai ba, in da wahala ake sha ai kaima da baka zauna ba, ai kasan can d'in yafi dad'i shiyasa kake tafiya kayi zamanka, in gaskiya kake fad'a ka dawo gida ka zauna mana."
Abin ma ya bashi haushi, ya ce "Binta kada ki kuskura ki zo! Ni ma duk inda na samu kwana nake."
Na ce "To aini na riga nayi niyya, kayi ha'kuri idan nazo za'asan ya za'ayi."
Ban jira ya 'kara cewa komai ba na kashe wayar.
Ranar da zan tafi kuwa saida na amshi rancen dubu biyu saboda kashewa a hanya, nace ina zuwa zai bani kud'in in turo.
Haka naje wurin hawa mota, duka mutanen da zamuyi tafiyar dasu maza ne, ni kad'ai ce mace a ciki.
Ana "Baiwar Allah ko a d'an samu ayi maki wuri daga ciki, tunda ke mace ce."
Na ce "A'a abarni a sama, ai zan mafi shan iska."
Haka muka d'auki hanya ana tafiya ana surutu, tafiya ta'ki 'karewa.
Tafiya ake-Tafiya ake har kud'i na s**a 'kare bamu kai ba, sai dai in wani ya sayi abinci ya sammin.
Har s**a fara tambaya ta "Wai ke ba zaki kira mujin ki bane, ki sanar da shi gaki nan, ya 'kara turo maki kud'in guzuri."
Na ce "Ai bana so ya san na tafo, so nake sai dai kawai yaganni, inyi mai safarayis, saboda bai san cewa yau ne tafiyar tawa ba, ai saidai kawai ya ganni."
Wani ya ce "Dama kin san inda yake ne? Hala kin ta'ba zuwa dama.?"
Na ce "A'a ban ta'ba zuwa ba, amma dai na san a lagos yake."
Ya ce "To idan kinje ki kira shi a waya ki shaida mai kin iso, sai yazo ya tafi da ke."
Na ce "To shikenan.
Kwana d'aya kwana biyu, munata tafiya, wahala dai ta gidan duniya na sha ta, tunda nake ban ta'ba tafiya mai nisa ba, na gaji.
Ga yunwa, abinci baya isa ta, sammin dama ake.
Ba anan tashin hankalin yake ba, muna fara shiga yankin lagos kowa na cikin motar ya koma turanci, ba wanda ya 'kara magana da Hausa.
Haka aka sauke mu gaba d'aya sauran wad'anda muka rage a cikin motar, domin wasu sun sauka tun a hanya.
Sai a lokacin na d'auki waya na kira shi.
Na ce "Gani nan fa na iso."
Cikin razana ya ce "Wai da gaske? To yanzun kina daidai ina?"
Na ce "Nima ban sani ba, ga shinan dai mun shigo inda kowa turanci yake, akwai mutane da yawa a wurin, amma ban san sunan wurin ba..... "
Ya zata kasance? Comment ✔️liking ✔️ sharing ✔️
Idan kuna son ci gaban labarin.
Share nace ayi mani ba copy and paste ba, kada ayi min copy ban amince ba
Fatima Dahiru Funtuwa Binta ✍️