27/05/2026
ALHAMDULILLAH, EIDUL-ADHA MUBARAK
Labari cikin hotuna...
An gudanar da Sallar Idi lafiya a Bakassi Eid Ground da ke kan titin Biu, a nan garin Maiduguri, Jihar Borno.
Daga:
Hassan Bulama (Abu Khadeejah)
Ali Muhammad Musine (Salaf)
A yau Laraba, wanda ya yi daidai da 10 Dhul-Hijjah 1447AH, an gudanar da Sallar Idi raka’a biyu ta Babbar Sallah a filin Idi na Bakassi da ke kan titin Biu, a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Sheikh Muhammad Badaru ne ya jagoranci sallar, inda dubban mutane s**a halarta domin gabatar da ibadar Eid.
Sheikh Malam Ibrahim Hassan ne ya gabatar da nasiha kafin zuwan liman.
Malam Ibrahim ya yi nasiha a kan Suratul-Asr, sannan daga ƙarshe ya yi addu’ar zaman lafiya ga Jihar Borno da ƙasa baki ɗaya. Haka kuma, ya yi addu’a ga tsohon shugaban kwamitin Bakassi wanda ya rigamu gidan gaskiya a makonnin da s**a gabata, tare da yi wa shugabanni da malamanmu da s**a rigamu gidan gaskiya addu’a.
Daga ƙarshe, Mallam Muhammad Badaru ya gabatar da Khutbah tare da addu’o’i kamar yadda aka saba.
Allah Ya maimaita mana cikin ƙoshin lafiya da zaman lafiya. Ameen.
JIBWIS Social Media
ABU KHADEEJAH ✍️
10 Dhul-Hijjah 1447AH
27 June 2026