18/12/2023
MACE A MUSULUNCI (12)
HAKKIN MIJI A KAN MATARSA (5)
Biyayyar Mata Magabata Ga Mazajensu
◾ A farkon lokaci da aka saukar da wahayi ga Annabi صلى الله عليه وسلم a kogon Hira bai tafi ko Ina ba sai gida wajen Nana Khadija رضي الله عنها وأرضاها, ya dawo gida a firgice zuciyarsa cike da tsoro ya ce: "Ku lullube ni. Ku lullube ni." Nana Khadija ta lullube shi har tsoron da yake ji ya tafi. Sai ya bata labarin abin da ya faru, ya ce: "Ina ji wa kaina tsoro!" Sai ta kwantar masa da hankali, ta ce: "Ina! Wallahi Allah ba zai taba kunyata ka ba har abada. Kana sadar da zumunci, kana kula da marasa karfi da marayu, kana taimakon mabukata, kana karrama bako, kana taimako akan dukkan wani abu da ya shafi gaskiya. Daga karshe ta dauke shi zuwa wajen dan baffanta Waraqa bn Naufal inda ya dada kwantar masa da hankali ya ce mala'ika ne ya zo masa. Duba Bukhari:4953
Annabi صلى الله عليه وسلم ya fita tare da Nana Aisha رضي الله عنها وأرضاها a daya daga cikin tafiye-tafiyensa da s**a isa wani wuri da ake kira Zatul Jaishi sai abin wuyanta ya tsinke ya fadi sai Annabi صلى الله عليه وسلم ya tsaya neman sa, kuma ba ruwa tare da su. Sai sahabbai s**a je wajen Sayyidna Abubakr رضي الله عنه s**a ce, baka ga abin da Aisha ta yi ba, ta dakatar da Annabi صلى الله عليه وسلم da sauran mutane, ga shi kuma ba ruwa tare da su?" Sai Sayyidna Abubakr ya je ya same ta, Annabi صلى الله عليه وسلم ya dora kansa a kan cinyarta yana bacci. Sai ya yi mata fada ya fadi abin da Allah ya nufe shi da fada ya dinga zungurinta a kuibinta da hannunsa. Ta ce: "Ni kuma na kasa motsi saboda Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yana kwance a cinyata." Duba Bukhari:334, Muslim:367
Abin lura a nan, shi ne irin yadda Nana Aisha ta mallaka wa mijinta cinyarta domin ya yi bacci a kai. Har ma bata yarda ta motsa jikinta ba ko yaya, domin kada ya tashi. Tare da cewa mahaifinta ya taso mata a fusace, har ma yana zungurinta.
◾A yayin da Annabi صلى الله عليه وسلم yake cikin rashin lafiyarsa ta karshe, matansa gaba daya suna k