19/01/2025
Katsina Ta Cika Ta Batse Yayin Da Lado Ya Aura ’Ya’yansa Mata Hudu
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Juma’a, 17 ga Janairu, garin Katsina ya cika da ya batse yayin da manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasar s**a hallara a Masallacin Juma’a na Bani Coomassie domin halartar daurin aure na ’ya’yan ɗan siyasa, attajiri kuma ɗan taimakon jama’a, Sanata Yakubu Lado Danmarke.
Amare su ne Rukayya, Maryam, Fatima da Dr. Zainab Yakubu Lado, waɗanda aka aurar da su ta hannun attajiri Alhaji Dahiru Bara’u Mangal a madadin Sanata Lado.
An ɗaura auren Rukayya Yakubu Lado da Abubakar Zaharaddeen wanda tsohon Babban Hafsan Sojojin Sama, Air Vice Marshall Sadiq Abubakar ya wakilta. Fatima Yakubu Lado kuma ta auri Khalid Kabir Barkiya wanda mahaifinsa, Sanata Kabir Barkiya, ya wakilta.
Haka nan, Dr. Zainab Yakubu Lado ta auri Farfesa Wasiju Madina Almustafa, inda Gwamnan Jihar Adamawa, Umaru Fintiri, ya wakilci ango yayin daurin auren. Sabira Yakubu Lado kuwa ta auri Aminu Abubakar Musa wanda Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya wakilta.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya karɓi baƙi da s**a halarci bikin daurin aure, tare da rakiyarsu zuwa wurin taron. A cikin baƙi akwai ’yan majalisu na tarayya da na jihohi, hakimai, masu rike da sarautun gargajiya, attajirai, shugabannin masana’antu da ’yan siyasa daga sassa daban-daban na ƙasa.
Har ila yau, mambobin jam’iyyar PDP daga ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina sun halarci bikin, tare da wasu fitattun mambobin jam’iyyar, ciki har da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Mustafa Inuwa.
Shugaban Jama’atu Izalatul Bid’a Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) na Jihar Katsina, Sheikh Yakubu Musa Hassan, ya jagoranci addu’o’in zaman lafiya da ci gaban ƙasa tare da roƙon Allah ya albarkaci rayuwar aure ga amare da angwayen.
Sanata Yakubu Lado Danmarke, wanda tsohon Sanata ne, tsohon dan Majalisar Wakilai, tsohon memba a hukumar NDDC, tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Kankara, da