27/07/2025
Ka daure ka kyautata ma'amalarka kaida mutanan da kuke rayuwa karka cuci wani kar kabari acuceka idan ancuceka kabi haqqinka idan anfi qarfinka ka barshi da ALLAH amma mafi aala ka yafe masa kazamo me haquri da juriya da riqon amana
Kazauna da kowa lafiya
Don wannan mutanan sune zasu rakaka in ka mutu zuwa makwancinka kuma sune masu yabanka insun yabeka akan halin kirki haka kake inma sun yabeka a halin banza haka kake
Ya ALLAH ka kyautata karshenmu albarkar annabi muhammad (s a w)