21/04/2024
HAPPY BIRTHDAY KARAMAR SHEIKHU IBRAHIM NIASSE RTA
Lokacin da Maulana Sheikh Ibrahim Niasss RTA ya Auri Sayyida Bilqees (Mahaifiyar Sayyida Ummuhani Niasse) tayi shekaru tara 9 Allah bai bata Haihuwa ba, Sheikhu Ibrahim Niasse ya kaita kasashe daban-daban ta hadu da Manyan likitoci Amma Allah bai bada haihuwa ba, Manyan Sheikhunnan Nigeria sunyi kokari wajen Addu'a saboda Suna ganin Sayyida Bilqees ita kadaice Matar Sheikhu RTA ta Nigeria suma suna so ace Tasu ta Nigeria ta samu ɗa ko 'ya tare da Sheikhu Ibrahim Niasse RTA. Ana cikin haka ne wata Rana Sayyida Bilqees ta shiga dakin Sheikhu Ibrahim RTA domin tayi Masa Ina kwana bayan ta gaishe shi ta juyo ta nufo ƙofa domin ta fito kawai sai Sheikhu RTA yayi Kaki ya tofa mata a bayanta sai Tace Sheikhu kayimin Tofi a baya, Sai Sheikhu RTA yace mata shin bakyaso ki goya ɗa na a bayanki ne? tace inaso Toh a wannan Shekarar aka Haifi Maulatuna Sayyida Ummuhani Ibrahim Niasse RTA
Bayan an Haifi Sayyida Ummuhani ta zauna A hannun Kakarta ta wajen Uwa Hajia Amina har zuwa lokacin fara karatu wato shekara bakwai, da wata Waqi'a ta faru Sai Sheikhu Ibrahim Niasse RTA yacewa Sayyida Bilqees ki gayawa Mahaifiyarki ta kwantar da hankalinta akan Ummuhani Mahaifina Alhaji Abdullahi Yana Tare da ita a koda yaushe.
Sayyidah Ummuhani itace "Yar Sheikhu RTA ta karshe wanda s**a yi Magana da Sheikhu ana gobe Sheikhu RTA zaiyi tafiya zuwa london domin jinya da daddare sai ya tura khadiminsa Musa Ghana ya kirawota daga Makaranta, Yace Mata tunda mahaifiyarki ta tafi ganin gida ina ɗiban Abincina na zuba a kwano na bayar a kawomiki Makaranta dafatan ana kawowa? Tace Eh ana Kawomin, sai yace Mata Ya karatu Dafatan kinayi Tace Eh inayi, Sai yace yanzu ina k**e, Sai Tace Nayi Hadda ta farko na juyo ina Surati Hudin daidai
وما من دابة في الأرض إلا على الله رزقها ويعلم مستقرها ومستودعها كل في كتاب مبين
Sheikhu RTA yace karantamin tayi masa karatu, yace Mata Lallai ki karasa karatunki domin nayiwa Kakanki Abdulmalik Alƙawari kece wac