13/09/2023
*WAJABCIN YIWA LIMAMI BIYAYYA ACIKIN SALLAH;*
-
"Zaka samu acikin masallatan mu da dama wasu mutanen suna saɓawa limaninsu acikin sallah, sai kaga mamu ya riga limami ɗagowa, ko kuma ya rigashi tafiya sujjadah, kodai wani abu mak**ancin hakan, sun manta da cewa lallai shi limami ana yi masa biyayya ne idan ba ya wuce ƙa'idah bane acikin sallah"
-
"An sami ruwaya daga anas bin malik (r.a) yace: Manzon Allah ﷺ, yace: lallai abin sani shine; an sanya limami ne domin ayi koyi dashi, idan yayi kabbara, to kuma kuyi kabbara, idan yayi ruku'i, kuma kuyi ruku'u, idan ya ɗago, kuma sai ku ɗago, kuma idan yace sami-Allahu-liman hamidahu, ku kuma kuce; Rabbana walakal-Hamdu"
Sahih Al-Bukhari (1114)
-
"Mamu kala uku ne:
💧Akwai yayan limami.
💧Akwai abokin limami.
💧Akwai ƙanin limami.
-
"Yayan limami shine wanda yake riga limami aiwatar da aiki a cikin sallah, bayan kuma limamin shine jagoransa, wannan kuskure ne"
-
"Abokin limami shine wanda yake aiki bai-ɗaya da limami, yana riƙe masa bamba, wato suna aikata komai a tare acikin sallah, wannan kuskure ne"
-
"Ƙanin limami shine wanda yake jiran limami saiya aiwatar da wani abu a cikin sallah sannan sai shima ya bishi, wannan shine daidai"
-
-
Biyo Instagram ɗinmu 👇
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5
-
-
Telegram chennel 👇
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes