27/09/2025
Tunatarwa
“Kun ga lokacin Annabi aka samu irin wadannan mutanen, kuma aka tafi tare da su; masu raunin imani, da masu zuciya da ƙaƙo, da kuma tsantsan munafukai, amma duk an yi tafiya da su. Har da Tabuka ma an je da su, don a Tabuka sun yi maganganu amma an tafi da su. To, tafiya ya gaji wannan kenan. Amma muhimmin abu shi ne ya zama akwai wasu masu Iklasi waɗanda yake da ba don su ba, ba abin da zai tabbata. To mu samun masu Iklasin ne ya dame mu. Don kwasan duuu din mutane wannan kar ya dameka, ko ba komai in abin ya yi ƙarfi ba wani duuu din da ba zai zo ba. Kuna tsammanin akwai wanda ba zai zo ba in abin ya zama ɗaukaka? Kowa zai zo.
“Amma lokacin da yake wahala ne, in ka ga wani ya zo yana ɗan abubuwa, yana irin na tatsuniyar kura ce, ‘daga baya da baya na ka tsaya, in na ji kaya-kaya in noƙe.’ Sai ya yi irin wannan, ranar Waqi’a a noƙe, in ba Waki’a a dawo. In aka ga alamar Waki’a a bace, in ta baje a dawo, ai ta cika baki.
“An samu irin wannan a lokacin Annabi (S) ai. ‘Fa’iza zahabal kaufu salaqukum bi alsinatin hidadin ashihhatan alal khair.’ (Ahzab: 19) Wato, idan tsoro ya tafi, sai su zo su yi felen-felen su dameku da feƙaƙƙen baki don kwadayin abin duniya. Idan kuwa tsoro ya yi tsanani za su yi burin (ina ma) suna ƙauye suna tambayar labarinku.
“Wannan ba ana faɗin abin da mai yiwuwa su yi bane, akwai wadanda s**a je ƙauye ne s**a maƙe, suna tambayar an kashe Annabi? An kashe shi? Su sun fella a guje sun yi ƙauye, amma kuma da aka tabbatar cewa komai lafiya lau sai s**a dawo fele-felen da baki suna cewa, haba! Ai rannan irin yadda s**a dafki Mushrikai Malam! Nan kuwa suna kauye a ɓoye. Amma suna cewa; ai in ka ga irin yaƙin da na yi rannan, habawa Malam. Ai dama mu ba gudu ba ja da baya! Domin neman abin duniya wanda ya haɗa da dukiya (ganima) da muƙami. Wasu suna ce ganima kawai, nace baya ga ganima har da matsayi. Suna son ace su ne manya.
“To, ba za a rasa wannan ba, amma mu abinda muke so ya zama kai ka zaɓa wa kanka wanne kake so. Kun san a karatunmu na Nahjul Balagha da ya wuce, kun san wani abu da Abdurrahman Bin Auf ya yi, kun ji yadda Miqdad bin Aus ya masa ko? Miqdad zai je gidan Imam Ali (AS) sai ya haɗu da Abdurrahman Bin Auf a hanya, sai ya k**a hannunsa ya riƙe, yace Abdurrahman, wannan abin da ka yi in saboda Allah ka yi, Allah ya ba ka ladan duniya da lahira. In kuma saboda duniya ka yi, Allah ya ba ka arziƙi mai yawa. Sai Abdurrahman yace, tsaya ka ji. Miqdad yace masa, ba ni buƙatar in ji komai. Sai ya yi gaba abinsa. Yace me za ka fada min? Wato bani buƙatar in saurare ka.
“Nace ai kuwa ya yi masa nasiha, tunda yace in don duniya ne Allah ya sa ya samu duniyar sosai, in kuma don Allah ne Allah Ya ba shi ladan duniya da lahira, in kuma don duniya ne ya bashi duniyar da yawa. To, ya masa mummunan addu’a ne? A’a. Da ace ya ce ne, in don duniya ne Allah ya raba ka da duniyar, sai ace ai ya masa mummunan addu’a. To sai yace, in don duniyar ne Allah ya ba shi ita sosai.
“Abin nufi, kai yanzu za ka zaɓawa kanka ne, kai ‘yan wanne ne? Kar ka damu da wane me ya zaɓawa kansa, kai ne za ka yi tunanin kai me za ka zaɓawa kanka? To, in ka zaɓawa kanka Lahira, irinka ne ake ganin dabi’a ta canza a wajenka. Domin wanda ke da 'ghaya' na Lahira, yake hanƙoron can, shi nan (duniya) bai cika damunsa ba, kuma ba za ka ga yana ƙorafi kan abubuwa ba.
“Amma lallai kam mun san akwai abubuwa da daman gaske, wadanda suke ana ta nasiha don a gyaggyaru, amma mun san ba za a gyaru duka ba. Kuma lallai ba muna neman kowane mutum lallai ya zama gyararre ba ne, amma dai in aka samu gyararru masu yawan gaske, ba sai kowa da kowa ba, amma masu yawan gaske, wani adadi da za mu iya cewa yanzu mun shirya, to za mu iya cewa Ok. Amma yanzu adadin da za mu ji cewa ‘it's ok’ ɗin ne ba mu da su.”
— Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) yayin rufe Tadrib din 'yan uwa Mata (Sisters), a ranar 20/9/2015 a Fudiyya Islamic Center, Zaria.
26/09/2025