29/07/2025
HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (070).
BIN ALLAH DA RIKON ZUMUNCI
*********************************
Hadisi daga Sayyiduna Abu Ayyub Al Ansariy (ra) yace :
"Wani Mutum yazo wajen Manzon Allah ﷺ sai yace "Ka nuna min wani aiki wanda idan nayishi zai kusantar dani zuwa ga Aljannah kuma ya nisantani daga wuta".
Sai yace masa : "KA BAUTA MA ALLAH KADA KA HADASHI DA KOMAI. KA TSAI DA SALLAH, KA BAYAR DA ZAKKAH, KUMA KA SADAR DA MA'ABOCIN ZUMUNCINKA".
Yayin da mutumin ya juya baya, Sai Annabi ﷺ yace : "Idan yayi riko da abinda aka Umurceshi, lallai zai shiga Aljannah".
Aduba Sahihu Muslim juzu'i na 1, shafi na 43.
BAYANI
********
_Wadannan ayyukan da aka lissafa acikin hadisin nan, ayyuka ne masu sauki ga duk wanda Allah ya saukaka masa. Amma suna da mutukar wahala ga mafiya yawan Mutane.
Ga misali :
1. TSARKAKE BAUTA GA ALLAH : Da yawan mutane (Har ma wasu Maluman) yanzu riya da son duniya da neman girma ya mamaye zukatansu. Tun daga Wa'azi ko Muhadharah zaka ga mutum Qarara yana son nuna cewa shi wane ne ta hanyar zagi ko cin mutuncin wadanda yake da sabanin ra'ayi dasu, koda sun girmeshi a ilimi da shekaru, koda bai yi zamani dasu ba.
2. SALLAH : Itama riya tayi katutu azukatan mutane game da ita. Kaga mutum yana sallah k**ar wanda cinnaka ke cizonsa (Idan shi ka'dai ne).
Amma idan agaban Jama'a ne sai kaga yafi yinta cikin nutsuwa!.
Kaga mutum yana sallah yana karairaya duk wai don ache "Ya iya". Mutane sun mance cewar ikhlasi Allah yake dubawa daga bayinsa ba wai yawan aiki ko kyawunsa a idon mutane ba.
3. ZAKKAH : Ita ma k**ar dai sallar ne. Masu kudin basu cika son fitarwa ba. Idan ma sun fitar da zakkar tasu, atsakanin junansu da iyalansu suke rarrabewa.
Kai ka fitar ka kawo ma iyalaina, nima idan na fitar na kaiwa iyalanka.. Ita ce siffar zakkar wasu masu kudin zamani.
Wani kuma idan ya tashi fitarwa haka zai rarraba Naira dari biyu ko dari biyar biyar.. Maimakon ya dunkule ya bayar.
4. ZUMUNCI : Shima yanzu mutane sunyi watsi dashi.